← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 124

Sashe 70

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamu suna zaune a farlo bayan sallah magarib. Wayarta wacce take hannun Amrah ta É—auki ringing. Mamu tace" Bani mana naji ya jikin nata ne?" Ablah tana jan carbi tace.
" Wlh kuwa munji shiru tin ɗazu wannan sakaran yaron daga ya siyomin kati nakira naji Mubina shiru tin yamma , ko wane munahircin ne ake ƙullawa ne?" Mamu tace"Ablah na me kuma? Kinaji fa suna asibiti batajin daɗi haka Umpah ya turomin message tin ɗazu, Mubina nashan wuyar cikin nan wlh." ta faɗi tana amsar wayar a hannun Amrah tana dab da katsewa Mamu tai picking ɗin call ɗin ta akara wayar a kunnenta, tare da sallama. Daga can kuwa Umpah ne manne da wayar a kunnensa ya ma kasa mgn, yana zaune kusa da Mubina har yanzu bata farka ba! Abbu na gefen Mubina yayi tagumi, da hannunsa ɗaya ɗayan hannun yana riƙe da hannun Mubinar wanda baya sanye da drip ɗin, yana mata Addu'a tausayinta fal cikin zuciyarsa Ummi da Papa Saleem ma na gefe Majeed ya tsura mata idanunsa yana mai cike da tausayinta tare da sonta mai tsanani. Mamu jin shiru yasa ta sake sallama tare da cewa.
"Wai ko dai ba Umpahn yara bane ba?" Umpah ya sauke numfashi daga can yace.
"Nusaiba nine mana kuyi hakuri Allah yayi ikon sa cikin Mubina ya zube..." Mamu tace" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! To ita Mubinar fa ya take? bani ita naji muryata?" Umpah yace" Wallahi tinda aka mata wankin ciki bata farka ba har yanzu bacci take ƙarin ruwa kawai ake mata..." Mamu ta fashe masada kuka tace"Don Allah Abdulrahim ka faɗa min gaskiya wai Mubina nada ma rai kuwa?" Ablah ta kece da kuka tacema Mamu "Ke!! Nusaiba bakinki ya sari ɗanyan kashi irin na Asubah ɗinnan , wace Mubinar ce ta mutu, wallahi bazamu yardaba da irin wannan mugun bakine , ki saurari abinda yake faɗi maki." ta faɗi tana miƙewa tana kuka. Amrah kanta ya kwance jikinta sai ɓari yake. Hakan yayi daidai da shigowar Kabeer da Sageer parlon bakinsu ɗauke da Sallama, wanda jin abinda Mamu take faɗi da Ablah yasaka Sageer jin wata irin faɗuwar gaba zuciyarsa tayi wani irin bugawa, da karfin gaske, ya buɗe baki zaiyi mgn ya kasa wanda kafin ya tantance ya yaken jikinsa ya faɗi ƙasa sumamme...

```Real Ladingo😍```

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

1️⃣&2️⃣

Aguje ummi da Majeed da papa Saleem suka nufo ɗakin da Mubina take. A bakin kofa sukayi karo, tana kururuwa, Ummi ta riƙota tana cewa.
" Subahanallahi, Mubina lafiya tsaya ki nutsu ki mana bayani.? Mubina ta rungume ummi gam ta kece da kuka mai tsuma zuciya, jikinta na kyarrrma, ta kasa magana. Papa Saleem cikin sigar lallashi yace"Baby nutsu mana kiyi magana me ya faru ne?" Majeed kuwa hankalinsa duk ya tashi, ya riƙo gefen kafaɗarta, yace.
"Kimana magana Mubina! me kika gani a cikin ɗakin ne?" Mubina ta maƙale ummi ƙam cikin shasheƙar kuka tace.
"Papa Kamal ne ya kirani yace na zubar masa da cikinsa wai sai yazo a yau ya ƙaramin wani cikin.... Wayyo ummi ni a maidani gida wallahi bazan zaunaba ya kuma min wani cikin." ta faɗi tana ƙara sautin kukanta. Da mamaki ummi da Majeed atare sukace.
"Ikon Allah ina ya sami numberki wacce ko 2 hours bata cika da siyaba...?" papa yace ai shine, so yanzu dai yi hakuri zo mu isa parlo kimana bayanin inda ya sami number ki." ya faɗi ya janyeta daga jikin ummi ya kama hannunta har yanzu kuka take, tana cewa" Nidai a maidani gida wallahi tsoro nakeji." Majeed ya dunƙule hannunsa ya bugi bango, ya ƙarasa shiga cikin ɗakin ya hango wayarta a saman bed, ya ɗauka missed calls 9 ya gani ya ciza lips ɗinsa ya fito da wayar a hannunsa.

Can parlo ummi da papa suka saka Mubina gaba da tambaya, ta ina Kamal yasan sabuwar numberta? Majeed yace "kiransa tayi ko?" Mubina ta zumburo baki gaba tace" Yo ni nasan shi yo, Ummi papa bari fa kuji yanda akayi." nan ta kwashe kome ta faɗa masu tin lokacin da Kamal ya fara kiran Sageer da kuma ita, da kuma nuna mata shi kurma ne da irin yanda ta shaƙu dashi. Mubina taja dogon numfashi haɗe da Tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba, tana kwalla tace.
"Kunji abinda mugun nan yay min billah ban yafe ba sai yaga ƙarshensa."
Ummi tace"Kai amman yaron nan baida kunya ko kaÉ—an me hakan yake nufi da yayi?" papa Saleem yace"Hummm sonta fa yake ba wani abuba wallahi..." Mubina ta zabura ta hawaye tace"Wlh ni bana sonsa me zanyi dashi ni Sageer nake so..."Majeed dake zaune ya cika da takaici yace.
"Bari ma rantsuwa kwantar da hankalin ki ba dai dai wannan layin bane ya sani?" Mubina ta juyo ta kalli Majeed fuskarta sharkaf da hawaye, ta ɗaga kai. Majeed ya cirosa a cikin wayar ya saka cikin bakinsa ya taune sa kwatsan kwatsan ya goge duk irin message da suke da number sa baki ɗaya, ya goge komai a wayarta na Kamal, ya ciro ɗayan layinsa A wayarsa sabo ya saka mata, ya beƙa mata wayar yace.
"Duk na goge numbersa yanzu babu hanyar da zai kiraki ki saki jikinki nan london ce bai isa ya shigo ba to tama ina zai fara neman ki?" Cikin farin ciki, Mubina ta amshi wayar ta matso kusan Majeed tace.
"Nagode my brother na yada ɗan mangwaro na huta da guɗa." ta faɗi tana goge ƙwalla. Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhmdllh wuta ta mutu Baby ki ajiye hankalinki kiyi karatu karki faɗama Umpah idan ya kiraki sbd kar hankalinsa ya tashi." papa yace.
"Ai yanzu kome ya wuce Baby ki saki ranki." Kai Mubina ta ɗaga. Aleema yace"Kai Aunty Mubeen nan akwai kuka."Azeema tace "To ba taɓota akayi ba..."Majeed yace" dallah uwayan iyayi kuma mutane shiru."
Mubina ta miƙe tace "Papa Ummi zan kwanta Azeema ku tashi muje mu kwanta, brother good night."Majeed yace.
"Night." Mubina ta kama hannun Aleema da Azeema suka nufi bedroom. Papa yace"Wlh karyar banza yake dan ya tunzurata ne."Majeed yace"Zai iya ɗin yayi da farko kuwa, wlh da yanzu na kashe banza wollah." Ummi tace"Allah ya fishi ba dai anyi maganinsa ba basss." Majeed miƙewa yay ya fice papa ya shiga don ya watsa ruwa. Ummi ta miƙe ta nufi ɗaki. Mubina kuwa suna zuwa shirin bacci tayi ta kira Sageer wayar na ringing bai ɗaga ba! Ta kira Mamu suka sha hira dasu Ablah da Amrah ta kira Kabeer da Basma, kamar su cinye juna sai hira suke suna kyalkyala dariya, haka ummi ta isko Mubina, abin ya mata daɗi sosai. Gani ta saki ranta tana hirata yasa ta barta itama tai shirin kwanciya. Su Aleema har sunyi bacci. Mubina ta jima sosai kafin suke sallama da Basma ta ajiye wayar ta shige jikin ummi tana turo baki. Ummi ta rungumeta ƙam tace.

"To mage uwar son jiki kalli kanninki suna kwancinsu can kowa da katifarsa amman ke ko."Mubina ta lumshe manyan idanunta ta shagwaɓe tace"Ummi bacci nakeji."ummi ta shiga buga bayanta haɗe da shafawa. Ai kuwa cikin 5 minutes har tayi bacci. Ummi ma ba jimawa baccin ya ɗauketa. Can Niger ɓangaran Sageer kuwa lokacin da ya kado parlo a guje, Nini tana zaune ita da Najwa da Abban Sageer ya fito yana zazzaro idanu. Nini tace"Sageeru lafiya?" Sageer yace"Wlh Kamal ne ya kirani yana min wasu maguguna..." sai kuma yay shiru tunawa bai sanar da iyayansa kome ba game da ƙaddara Kamal da kuma ita kanta Mubinar yaji tsoron su sani suce bazai aureta ba.! Abban sa yace.
"Me ya sami Kamal ɗin ne?" Sageer ya tattaro ƴar guntuwar nutsuwarshi, ya zauna kusa da mahaifin nashi yace"Daman cewa yay zai dawo cikin wannan satin , to kuma yanzu ya kirani wai gashi a kofar gida har na fito ɗinan da gudu cikin murna kuma ya bushe da dariya wai wasa yake min..." Nini tace"Kai Sageer ai mu ka tsorata mu wlh nazata ba lfy." Najwa tayi dariya tace"Yauwa na kusa ganin yaya Kamal."Sageer miƙewa yay jiki asanyaye ya koma ciki ya ajiye wayar tasa ya shirya ya fice ba tare da wayar ya nufi gidansu Kamal ɗin. Ɓangaran Kamal kuwa bayan ya gama masu tijara ɗin ya shiga sintiri yana jan tsaki karo na babu adadi, yana dunƙule hannanusa ya bugi ɗayan hannun, yace.
No! Impossible wlh kunyi kaɗan ku dukan biyu ɗin sai na baku mamaki wollah." ya faɗi da karfi yana zirganiya tsakiyar parlon, tsumammun idanunsa sunyi jajur, ya kai a ƙalla awa ɗaya cur kafin yake nufar bedroom, ya shige toilet ya kunna fanfon ya sakar ma kansa shower ruwan na sauka tsakiyar kansa, a hankali ya furta" *Mubeena* sai nayi maganinki ƙaramar marar kunya." ya jima sosai kafin yake ɗaura alwalla ya fito ɗaure da towel kasancewar nan dare yayi sosai, jallabiya ya saka yaje fridge ya dauki bottle ɗin water ya buɗe ya kafa bakinsa sai da yasha rabi ya rufe ya mayar fridge ya nufi gun darduma, ya tayar da sallah.
Chapter 70 · 0% Book details