Sashe 117
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Mubina tana fita bedroom ɗin Mamu ta shiga, ta iskota saman gado tana sharara bacci gadon ta hauro ta shige jikin Mamu tace"Mamu ni ki tashi jikina ciwo yake yi wlh."Mamun ta buɗe idanunta Mubina ta ruƙumƙumeta. Tace"Baby nagaji ina hutawa kin tasheni, me ya hanaki bacci har yanzu?" Mubina tace"Mamu kimun tausa zazzaɓi ne ya shamin kai." Mamu ta ƙara rungume Mubinar ta shiga danna mata jikinta, kuka Mubina ta saki na shagwaɓa tace"Allah Mamu kamar bakyayi ni ki danna mun da karfi. kuma gaɓa gaɓa ko ina tauna yake, Aunty tanacan wallahi har yanzu hira take da mijinta, taki min tausar." Mamu tace"Wlh Baby kin fiye rigima haka kawai kizo ki hanani bacci, ina ruwanki da firasu ke waye ya hanaki hirar danaki mijin?"." ta faɗi tana tashi zaune ta ɗora Mubina kan cinyarta ta shiga manmatsa mata jikinta. Lamo tayi jikin Mamu tana jin daɗin tausar, ta turo baki. Dan sosai takejin daɗin tausar, a haka
har bacci ya É—auketa. Mamu tajima bayan baccinta ma tana mata tausar. Kafin ta gyara mata kwanciyarta ta rungumeta taja masu blanket. Umpah ne ya shigo, da sallama ya murzawa kofar key, ya nufo saman bed É—in wajan Mamu yana cewa"My nusy ya najiki shiru?" Mamu tace"Kama koma É—iyarka tazo ta hanani bacci gata a jikina ta manne ni Na...!" ~*Sweet LadeeTimnit Welday ceðŸ˜*~
*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*
*Book 2*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
3ï¸âƒ£9ï¸âƒ£&4ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
"Nafi awa ɗaya ina mata tausa, gata ta manne min tayi bacci ni ina raba idanu, Babynka sai fitina daman ya bare ta haɗu da ciki mai kasala da ciwon jiki, dan haka koma yau lokacin ƴarka ne." Ta faɗi tana murmushi ta ƙara manne Mubina jikinta, wacce take ƙara riƙe Mamu ɗin kamar zata gudu.
Umpah ya ƙaraso ya zauna bakin gadon janye blanket ɗin ya taɓa jikin Mubina yaji ba zafi, kiss ya manna mata a goshi ya shafi fuskarta yace" Allah sarki Auta Allah ya raba lafiya, ina so naga jikana ɗan Auta ba. Nusy Mun gode bari na koma good night nima tausar nazo na miki amman ba kome a kularmin da rabin raina sosai."ya faɗi yana murmushi ya luluɓesu da blanket ya shafi fuskar Mamu ɗin, ya fice ya kashe masu wutar ɗakin. Mamu murmushi ta saki ta rungume ƴarta tsam har barawo bacci ya ɗauketa...
Washegari gidaje guda hudune suka kasance cikin farin ciki, na aurar da ƴaƴansu. Masha Allah duk yanda zan faɗa maku bikin wannan ya wuce hakan, dan tsayawa faɗin irin shagulgulan da ake zai ɓatamin lokaci ne, masu karatu ku kisama da kanku😜. Kowane gida cike yake ƴan uwa da abokan arziki, tin safe karfe 9:00 am na safe aka ɗaura auran Kabeer da Basam auran da ya sami halartar manyan mutane. Idan kaga yanda Mubina da Amrah sukayi kyau abin ba'a cewa kome, masha Allah gidansu damƙam da mutane haka gidansu Kamal Basma Sageer. Kamal da Sageer waje ɗaya suke zaman bikinsu. Gidansu Kamal ma walima akayi yayin da suka saka ankon atamfa. Haka gidansu Mubina haka gidansu Sageer Basma kuwa ta haɗa liyafa itama da ƙawayanta kafin zuwa dinner. Su Kamal da Sageer sunce basa dinner ɗin kome nan suka hada walimarsu ta maza wanda suka samu halarta jama'ar da basuyi tunaniba. Kabeer kuwa karfe hudu suka tafi dinner, dan da farko sun ɗauka ɗaurin auran yamma za'ayi sai akayi na safe.
Mubina taso zuwa Kamal ya hanata dole ta haƙura, haka suka kasance ita ƴar uwarta da ƙawayensu, se Samha wacce tayi kwaliya tamkar sarauniyar kyawawa, tana tare dasu Mubina. Mubina sai yabonta take. Dinner yayi daɗi kam anci ansha an raƙashe anyi watsin kuɗi, dangin sunsan ƴarsu gidan akwai zata shiga, Basma har kukan rashin Mubina tayi a wajan dole sai ƙawarta Zulaihat ce ta tsaya kan kome... Haka akayi wunin biki aka gama lafiya, su Mamu har angaji da sakawa da fitarwa ƴaƴa uku zasu kwana gidajansu abin ba ƙaramin dadi yake mataba. Haka Ummah da danginta suma sun nuna bajinta wajan auran dan bazaka taɓa cewa ba sabon aure bane ba, ma'ana kamar yau ska ɗaurashi, ba taron biki bane ake ba, amarya harda ciki, haka dangin Abbu Goggo saida taje taga Mubina ta tsokaneta. Gidansu Sageer haka abun yake, Nini cikin danginta suma gidansu ya tara jama'a, bila adadin.
Misalin karfe tara motoci suka cika kofar gate É—in gidan Umpah na É—aukar Amrah da Mubina, Kabeer shima antafi É—auko masa tasa matar, wacce gidansa mai masifar kyau ke nan baya ba nisa itama kuwa Lubah da ismi'il sun zuba mata dukiya.
Mubina na jikin Mamu tana kuka. Amrah jikin Umpah an saka masu wani haɗadɗan sahari, farine an masa adon plowers blue, haka rigar ta ciki Farace tas mai samtsin gaske, sunyi kyau sosai Nasyya sosai Umpah da Mamu suka masu da Ablah. Umpah yace"Haba auta kiyi haƙuri Mana, Zuwaira kama Auta kuje hajiya kama Amrah Allah ya baku zaman lafiya ya kuma maku albarka." Mubina ta saki Mamu ta rungume Umpah tana kuka. Dakyar ya samu ya lallaɓata aka fice dasu Mamu hawaye take sosai na Murna auransu da kuma rabuwa da ƴaƴanta, Amrah saboda kuka har wani shiɗewa take neman yi, Ablah ma matsar kwalla take tana cewa"Allah sarki ƴan jikokina aure mai rabawa ya rabamu, Allah baku zaman lafiya."Umpah yace "Ameen." Mota aka sasu kowace aka nufi gidanta da ita. Basma ma kukan tasha gaban iyayanta suna mata nasiha, tayi kyau iya kyau wani rantsatsan les ne ajikinta ɗinkin doguwar riga an rufeta ƙaton mayafi mai shegen kyau, itama da kyat aka fito da ita daga gidansu aka yi ɗakin mijinta da ita. Amrah haɗadɗan gidanta aka kawota mai shegen kyau masha Allah. Kai tsaye bedroom ɗinta aka gice da ita, wanda yaji kyau iya kyau bed ɗin nata kaɗai abin kallo ne. Mubina ma nata gidan aka kaita mai kama da aljanar duniya, yaji kome na rayuwa haka Basma ma gidanta ya haɗu ba ƙarya...