← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 124

Sashe 46

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

```Bayan Sati biyu```
Alhmdllh Mubina taji sauƙi yanzu tana tafiya kwananta takwas a hospital aka sallame su, sbd kulawar da take samu gun iyayanta sosai suke bata kulawa, duk da haka kullum cikin kuka take bataci bata sha sai daket suke samu taci. Kamal da Sageer kullum se sunzo hospital amman Kamal laɓewa yake yana kallon ta ta window yaji dadin sauƙin da take samu, kukanta kawai ke damunsa, tin rana ta uku da ta ganshi ya shigo ta sake suma, Dr tace kar ya kuma shigowa dole sai laɓewa yake, Sageer kuwa da farko bata son ganinsa shima se da umpah ya mata faɗa cewar shi me ya mata? To shine har idan ya mata ya jiki take amsawa. Kabeer kusan kullum nan yake yini ko aikin baya iyawa yana kusa da ita sai da aka sallame su ne ya koma aiki gadan-gadan. Sageer na aikin sa Kamal ne fur yaki zuwa aiki duk da yadda ake matse dashi a makarantar, amman yaƙi fur har umpah ya masa faɗa amman bayada nutsuwar aiki yaƙi zuwa, yaba Sageer wayar Mubina ya kaima ta tin suna hospital shiko yaba Umpah dan a sannu yake binta a yanzu. Su Abbu kuwa da Ummah faɗan da umpah ya masu da nuna fushin sa yace shine a kama laifi kuma ya yafe amman su meyasa bazasu ja yaronsu ajiki ba, ko suna so ya faɗa wata rayuwane daban? To shi yasa basu sake ma Kamal zance yabar gidan ba yana gidan baya fita ko ina in ba hospital ba ganin Mubina, matsalar sa a yanzu kukan Mubina da Sageer yace masa kullum idan yaje gidan dubata se tayi kuka, se kuma fushin su Abbu tinda basa amsa gaisuwara sa se daket, daga Zakiyya sa Samha suke kula shi har ɓangaransa suke iske shi suna masa hira da jansa ajiki, kamar yadda Sageer ke masa, amman Kamal sam yanzu ya zama shiru baya magana har ya fara tara wata ƴar ƙasumba. Basma kuwa kullum se tazo taji labrin ƙawarta ace basu zoba, a haka har aka sako su, sun ma Mubina kwakwaran kashe karta kuskura ta faɗawa Basma gaskiya, kai ta ɗaga dan yanzu bata magana se kuka suyi ta lallashinta, amman idan Basma nanan bata yi, to jiya da yau an sami sauƙin kukan, kullum cikin lallaɓata suke ta koma makaranta tinda ta warware amman tace se dai a canza mata bazata Maryam Abacha ba... Jama'ah da dama na mamakin fasa auran Kamal da Amrah, wasu kuma na tunanin ko an gusa ne? Basma ma tayi tambayar duniya Mubina bataata mgnr ba dole ta zubama sarautar Allah idanu.

Alhaji Munkaila da Tukur sun baza kunnuwa sun saki baki suji labari a gidan Radeo da TV abinda ya faru da Kamal amman shiru sama da kwana goma shiru, kake ji ga Company sa kome na tafiya dai-dai babu abinda ya sauya, duk da baya fitowa, hankalinsu ya tashi gashi basu da damar faɗar wannan maganr tinda basu ɗau video ba.!! Suna nan dai suna saƙa yanda zasu billowa abin...

Kwance Mubina take a parlour tayi matashi da cinyar Amrah, daga ita se mini siket ruwan hoda, se vest fara sunyi mata kyau kamar Æ´ar tsana, yau garin rana ake sosai ga hadari Mubina ko da rashin son zafi a hakama ji take kamar tayi tsirara duk da akwai Ac na aiki sosai.

Idanunta a lumshe Amrah tana taje mata gashinta se fitar da kamshi yake ga santsi, ta ɗan kara ramewa se baiwar kyawunta na nan, da manyan breast ɗinta da hips ba inda suka rage. Lallausan farin hannunta ta dora saman hannun Amrah tana ciza pink lips ɗinta, A hankali kamar me koyan magana tace"Aunty da kin bari inajin zafi bari Mamu tamin kinji." Ummi Sabeela tace"Auta rigima kawai dan baki gama warwarewa bane ba." Mubina batayi magana ba dai idanunta numshe, dan yanzu ko zaka shekara mata mgn idan ba tayi niya ba to kallon ka ma baza tayi ba, Mamu ce kawai bata ma wannan sabuwar halaiyar tata. Umpah ne ya shigo da sallama. Mubina ta buɗe idanunta ta ɗago a hankali tace"Umpah nah sannu" karasowa yayi yace "Yauwa Auta" ya faɗa yana zama ya kama hannunta yace"Baby gyaran kai ake ko muje salon ne?" shiru ta masa ta sadda kanta. Murmushi yayi yace" Auta ki daure gobe ki fara zuwa makaranta tinda kinji sauki dan Allah kinji?" Kuka ta fashe masa dashi ta rungume umpah tana cewa"Natsane shi bazan je ba wlh tsoro nake kar ya sake sawa a kai masa ni hotel ni duka ma garin maradi tsoransa nake bana jin zan sake fita daga gidanan , wlh umpah" ta faɗa tana kuka mai tsuma zuciya. Abalah ta miƙe zatayi magana taga Abbu da ya shogo da sallama kafin a amsa yayi baya da sauri yana haɗa hanya.....

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣6️⃣

Ablah ganin Abbu ya juya ya fice bata kawo kome a kanta ba, ta iso gunsu Umpah wanda ke rungume da Mubina yana rarrashinta. Ablah tace"Wlh yaron nan ya naka samin rayuwar jika, gashi tana ikiraran bazata ko sake fita waje ba, haba ina dalili." ta faɗa tana zama, ta janyo Mubina jikinta tana lallashinta. Umpah yace"Baby kiyi hkr insha Allahu babu abinda zai sake miki, dan Allah ki saki ranki auta kinji."Mubina tayi shiru tayi lamo jikin Ablah tana sauke ajiyar zuciya, amman bata iya sake mgn ba, dan yanzu bata fiye mgn ba sam. Amrah ta matso tana kame mata gashinta da ribbon, tace"Umpah ko abari zuwa gaba ta kara warwarewa?"Umpah ya sauke numfashi da karfi yace"Ai baby bazata kunyata Umpah ba zata koma gobe insha Allahu, yanzu ku tashi muje Shoping baby ta zaɓi abinda take so..."Sabeelah tace "Yaya Abdul niko se nake ga me zai hana idan takiya anan ɗin, idan mun tashi komawa mu tafi da ita can London taci gaba a can ai zai fi sauƙi ko?" Umpah ya jinjina kai yace"Ba naƙi bane babyn ce bana son tayi nisa dani..."Mubina ta maƙale kafaɗa ta kamo hannun Umpah tace"Bana zuwa umpah zanci gaba anan, amman a canza min makaranta pls."Umpah yace"Yanzu dai tashi kuje ku shirya muje Shoping akwai hadari kar a fara ruwa."Mubina ta dafa Amrah ta miƙe tsaye batayi mgn ba, ta nufi kitchen tana tafiya a nutse. Mamu na tsaye tana tafasa shayi Laure na wanke kwanikan da akayi abuncin rana yanzu. Mubina ta rungume Mamu ta shige jikinta sosai tana turo baki gaba. Mamu ta ɗago kanta tana murmushi tace"ina jin ku fa baby ki daure ki koma babu abinda zai faru kiinji Mubina ƴar fara yarinya kyakyawa ba ruwanta da fitina ko?" Mubina ta maƙalkale Mamu tana murmushi. Mamu ta janyeta tace"Muje na tsara miki kwalliya ki haɗe kiyi kyau abinki kuje Shoping ɗin." ta faɗa tana riƙe da hannun Mubina suna tafiya, tace"Laure kina dubamin shayin idan ya gama dafuwa ki juye a butar shayin ki jera cup a tire ki kawo ma su Ablah zani na shirya babyna." Laure ta masa da "To Mamu."

Wucewa suka yi ta parlon Sabeela tace"Uhum yau ƙawance ake ko?" Mamu tayi dariya suka wuce saman bene. Umpah ya bisu da kallo yana mai jin dadin kulawar da Mamu take ba Mubina a yanzu sosai. Ablah tace"Nusaiba Allah dai ya maki albarka, Abdul idan kun tafi kar ka manta ka siyo min fa dabino ɗin kaga saura kadan ya kare wanda nazo dashi." Umpah yace"Ablah bazan manta ba bari na amsa waya kafin su fito"ya faɗa yana miƙewa ya nufi bedroom ɗinsa ta ƙasa. Azeema tace"Ummi ina Aleem da yaya Majeed basa zuwa ne?" Sabeela tace"uhm ke uwar yawo se kije ai Majeed da Aleem suna tare da Kabeer yau." Ablah tayi mgn da harshen larabci tace"Kema dai Sabeela da gangan kike Abdul zai baki Mubina kuje London, tabdijam..." Sabeelah tayi dariya tace"Ablah ai nima uwace ko...?" Ablah ta taɓe baki tana jinjina kai.

Suna shiga Amrah na fitowa daga wanka, Mamu ta haɗa Mubina ruwan wanka taje tayi ta fito, ta tsatsara mata kwalliya da kanta ta kece raini, ta buɗe katoton wardrobe ɗinsu wanda yake shaƙe da kaya, ta zabo mata Abaya red wacce aka cakudata da black, haka mayafin ma yake ta ciro mata ta bata ta saka ta yane mata kanta da gyalen, wow iya kyau yarinyar tayi kyau ba ƙarya, ta dauko mata taklma ƙasa-ƙasa basu da tsayi sbd yanayin jikin nata, ta saka sai headband baƙa itama ta fesa mata turare.

Mamu tace "Masha Allah ɗiyata Allah ya tsare min ke, Allah yaba Sageer ikon riƙe min Amana bayan auranku..."Mubina ta faɗa jikin Mamu ta saki kukan sangarta ba hawaye tace"Ni Mamu na ma fasa tafiya to..."Mamu tace"To na bari shiru muje Umpah na jiranku." Amrah da ta haɗe cikin wani arne less maroon yayi mata kyau sosai kome das tana fesa turare tace"Wlh Mamu kin iya shirya kwaliya baby tayi ba ƙarya."ta faɗa tana ɗaukar jakarta tabiyo bayansu...

Umpah tinga nesa yace"Mamu kinci tukuici zan siyo maki cingam..."Mubina se da ta saki murmushi tace"Umpah cingam kuma?" Yace "Yes baby, oya muje to sai mun biya ta gidan baffa." Mamu tace "a gaishe min su to." Ablah tace"A dawo lfy"Umpah ya masa da "Ameen"Amrah ta kama hannun Azeema suka fice, Sabeelah na cewa"Baby ki kawo tsaraba." Mubina ta gyada kai, suka fice. Mamu ta zauna tana zuba shayi tana kurba suna hira.
Chapter 46 · 0% Book details