Sashe 22
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kaiki har gidan ku idan kika ki nunamin kuma zan kaiki gidana ne , na turmusheki na baki abar da kike so oya muje ki nuna min gidan ku." yana faɗin haka ya janyeni daga jikinsa ya kama hannuna ya damƙe cikin nashi wani irin gumi na ratsa tafukan hannuwanmu. Kukana na haɗiye nace"Allah ya isana ban yafe ba insha Allah se ka gani a kwaryar cin tuwonka , mugun azalumi..." yanda ya juyo ne yasa na haɗiye maganar na kauda kaina nayi saurin ɓoyewa bayansa. Kai ya girgiza ya janyoni na dawo gaban sa, ya buɗe kofar yana riƙe da hannuna muka fito. Muna fita na cika da mamaki ganin hospital ɗinmu ne amman nayi shiru. Office ɗin Dr Munnir muka shiga, yana ta rubuce-rubuce cikin takardu. Yana ganina yace"Ah Baby auta wai daman kece aka kawo? wlh ban lura dake ba sam" ya faɗa yana miƙewa yace da gurgu"yallaɓai kaine ka bugeta to a ɗiyar me hospital ɗince , ɗiyar Abdulrahim Kabeer algèrie ce , amman ƴan gidan su basu da labari ko?"."Kamal cike da mamaki yace "No wanda kake faɗa Abokin Abbu ne kuma nasan yaransa masu hankali ne da tarbiyya da nutsuwa , basa yawon ta zubar, kai ba wannan ba ni zan wuce kayi lissafin duk abinda ya kama ka kirana bata buƙatar magani bata jimu ba, se anjima." ya faɗa yana jaye da hannuna, cikin tsiwa nace" se ka hana ya zama ubana kuji shi kai to shiɗin ubana ne , nayi yawon ta zubar ɗin yawon dandi nake karewar ta zubar karshen rashin tarbiyya kuwa tsirara nake yawo kaji malam , da banyi niyar nuna ma gidan muba amman yanzu se na nunama... " Na faɗa ina mintsinin hannunsa da yake cikin nawa, bai koyi gezoba ya kaɗa kafaɗarsa yace" Banda lokacin ki." ya faɗa yana jana muka fito. Dr Munnir ya koma ya zaun yana dariya yaci gaba da rubuce rubucen sa. Muna zuwa gun motarsa na gane da itace ya tunzurani ɗazu kuma itace na bugi adedeta da ita. Buɗewa yay ya tunkuɗani gaban motar se da na dan bugu nace "Allah ya isa mugu kawai." bai ko kalleni ba ya zagaya ya shiga motar gun zaman direba yay mata key ya fizgeta da karfi ya nufi bakin get, aka wangale masa get, ya fice a guje. Tinda muka fito bai kalleni ba driving ɗinsa yake a cikin nutsuwa, nima nai banza dashi na kame kaina. Can naji sautin muryasa ƙasa-ƙasa yace"Gantalala ina ne wajanku?" Ban kula shiba na kauda kaina ina kallon titi. Ya sake cewa" Ok bazaki faɗa ba to bari na kaiki gidana muyi kwanan dadiro se kimin tausa da wannan busassan hannun naki..." cikin ɓacin rai na juyo na fara dukansa na wawuri kunnensa da cizo. Da karfi ya taka burki yana cewa"Sakeni ko kiga yadda zan miki duran yawu nasan shine kike so kin kasa dangana jarababbiya..." sakinsa nayi ina matsar kwalla na haɗa kaina da guiwa ina sauke numfashi da karfin gaske. Da sauri na ɗago nace masa"Ali ɗan tsoho zaka kaini gidan ɗan Algerie." na faɗa ina goge kwalla idanuna na kalli titi. Kamal kuwa se yanzu yake kallon tsantsar kamarta da Umpah da wannan yayar tata to amma ya akayi bai taɓa ganinta ba? Shi se yanzu ma hanklin sa ya bada da sunan da take aiki dashi a makaranta, tabbas ɗiyarsa ce... Kallonta yayi ya taɓe baki yace" Ashe kece zakkar gidan ku an baki tarbiyya kece kika watsata a titi.? Ban de kula shiba, sbd gudun kar yamin duran yawu nayi shiru ban sake kallon inda yake ba har muka iso kofar gidan mu daidai lokacin kuma su umpah suka yi parking ɗin motar su a kofar gidan. Yana tsayawa na soma ƙoƙarin bude mota ina kiran umpah amman bazai ganni ba sbd glass ɗin me suhu ne. Hucin numfashin sa naji kusan kunnena, hannunsa yana gugar jikina, nai saurin ɗagowa idanunmu suka sarƙe guri guda, fuskokin mu suka haɗe, har lips ɗinmu na gugar juna, nayi saurin janyewa ina murguda masa baki, yana ƙoƙarin buɗe min motar, yana budewa na zuro ƙafafuna waje na ƙaƙalo yawun bakina na tofa masa a fuskar shi haɗe da kai masa duka tin karfi a kirjinsa na kece da kuka nace "na barka da Allah"na fice a guje na nufi motar umpah ina ihuuuuu.... Inde *Kamal ne...* Ba'ama fara ba!!! Hakuri da rashin Editing me kyau😌