← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 124

Sashe 31

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mubina wacce take tsaye gaban dreesing mirror ɗaure da towel, handryer a hannunta tana busr da jiƙeƙen gashinta. Ta bushe da dariya tace"Kai Aunty yasin ina kwasar dariya wannan sakaran mijin naki ya kasa gane nice nake masa basaja fa ,hhhh wlh anji kunya jaki ya kada me shi." ta faɗa tana dariya, ta ajiye handryer ɗin ta shafama gashin ta mai ta kame shi da ribbon kamun gefe, ta zauna saman stool ɗin mirror ɗin ta shiga kwalliya tana wake-wakenta. Amrah kuwa da haushin abinda Mubina ta mata ya isheta ta sauko daga saman gadon sai lkcn na kare mata kallo tayi kara mulmulewa jikinta yayi kyau se sheƙi take se yar ramar fuska da tayi se fitinannan kamshi ke tashi a jikinta, kallo ɗaya zaka mata kasan ita ɗin Amarya ce. Rigar jikinta ta tattare tana murmushin mugunta ta riƙe wayarta gam ta iso dab da Mubina, ta ɗaga hannunta dirka ma Mubina duka abaya seda ta saki nishi ta zabura tace"Kan uba yau se naci gidan ku wlh tallahi." ta faɗa tana miƙewa. Amrah a guje ta nufi kofa da gudu tana cewa"uban wa yace kina zagar min mijina? ke idan na zagi wanan figagen Sageer ɗin me kamar ki zaki ji daɗi?" ta faɗa tana buɗe kofar ta wuce a guje. Mubina ta ko biyo ta daga ita se towel. Amrah bibiyu take tsallaka steps ɗin tana ihun kiran "Mamu zata dake ni wayyo Ablah..."Mamu da suke tare da Hajja lubah wacce shigo ba jimawa, ta miƙe tana tafa hannunwa tace"Amrah a siri zaki tona mana kike tsallaka steps bibiyu?" Bayanta Amrah ta laɓe tana shasheƙar gudu. Se ga Mubina da towel. Mamu tace" Baby hauka zaki fara ko me wai?" Mubina tace"Mamu Allah se na rama dukana tayi ban mata kome ba fa." Ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa bayan Mamu ɗin. Hajiya lubah tace" yi hakuri baby wai ba makaranta zaku ba Basma yanzu direba ya kaita maza je shirya idan kin dawo kin rama." ta faɗa tana kama Mubina ta jata suka bar gurin tana gunguni. Se ga Ablah ta fito tace"Me yake faruwa anci zalinta ko?" Mamu tace" Amrah ce Mummy." Amrah tace" Yo ai mijina ta zaga ke da bakida aiki sai ɗaure mata gindi se kace mu ba jikokin ki bane." Mamu ta buge mata maki tace" zan barki da babyn raguwar banza , kanwarki kike gudu wannan figigiyar yarinyar me zata miki?" Ablah tace" an zaki mijin naki yaci gidan su kaji mara kunya kuma wlh se ta rama bugunta , Nusaibah keko meye abin guri haka Allah yayi ta me ake da ƙiba Allah na tuba." ta faɗa tana tokara sanda ta zauna ta ɗauki remote ta kamo tashar Aljazeera. Mamu bata yi mgn ba ta koma ta zauna. Lubah sai da ta raka Mubina sama ta dawo ta zauna tana gaishe da Ablah, Ablah tace" da kin barta ta rama ai haka kawai me aka gani na bugo a jikinta? haka ranar Nusaiba ta bugeta idan bakwa sonta wlh zan tarkata kayana mu koma Algerie wajan dangi..." Mamu tace"Mummy ayi hakuri bama sake ba..." Amrah ta bushe da dariya tace" ikon Allah humm..." Mamu ta bugeta ba shiri tabar gun ta nemi gun ɓuya har Mubina take barin gidan.

Mubina shiryawa tayi cikin wando jeas fari irin me bin jiki, ya yabi lafiyar kyakyawar fatarta, yabi ƴan kananun cinyoyinta ya fito mata ƴan matasan mazau nanta hips dinta ya fito sosai wandon ya mata kyau matuƙa kamar ƴar tsana, se rigar irin me dan tsayi ce kaɗan bata karasa guiwa ba tana da yankeken hannuwa pink ce gaban rigar igiyoyi ne farare masu adon duwatsu a jikinsu baƙake, sune tabi ta ɗaɗɗaure su yanda ta gani a pic ɗin ledar rigar dan yau ne zata fara sawa, yanda Mubina ta ɗaure din yayi masifa ma rigar kyau ya fito da asalin kyawun Mubina tayi ɗass tamkar ka sace ta ka gudu. Hadadɗan takalminta Basket fari ta saka, ta saka siririyar sarƙa na gold da ɗan kunne farare ne masu kyau sai abin hannunsu ta manna zoben su a zara-zaran yatsotsinta, ta fesa wani shu'umin turare mai shegen daɗin tsiya, ta sako jelar gashinta gaba ta ɗauki ƴar ƙaramar jaka fara ta ɗauki phone ɗinta, zata saka jaka kiran Basma ya shigo ta ɗaga da sauri tace"kiyi hkr ganinan zuwa Haladu zai kawo ni ki fito ma kofa ina zuwa se mu waske tin ɗazu laweesa take kirana taro yayi taro zamu cashe yau fa idan na aami shisha yasin se bata hayaƙi." tana faɗin haka ta tsinke kiran tana dariya, ta saka wayar ajaka ta fice cikin takunta me cike da nutsuwa ko ina jikinta motsawa yake kamar tarwaɗa abin gwanin burgewa gata dai ba wani jikiba amman akwai kyan diri.

Tin daga nesa Mamu ta ke kallonta tace"Me zan gani wai baby a haka zaki fita bazaki saka kayana na hausa wa ba? makarantar zaki a haka?" Ablah tace "Ai naga ita ba ɓahaus bace kuma ai makaranta zata ba wani ƙiba ce da itaba bare kice surata ta fito" ta faɗa tana kallon Mubina wace ta zumburo baki gaba tana bubbuga ƙafa. Ablah tace" Ki kula da kanki maza jeki Haladu na jiranki kin makara ma." Mubina tayi murmushi tace "yauwa Ablah nah wai yaya Kabeer bai zo ba ne?" Mamu ta kauda kanta tana mana lubah magana. Lubah tace"ai fa ƙawar tata ma wando tasa Allah dai ya tsare mana yaranmu , ai bakinsu cikin makaranta ne." Mamu tace" Wlh hakan dai baiba ni bana son saka wandon nan." Mubina ta karaso ta fado jikin Mamu ta shagwaɓe tace" Mamu ai bakin makarantane fa kawai kimun Addu'a kinji." ta faɗa tana mannawa Mamu kiss" a kummatu ta saketa ta rungume lubah ta manna mata kiss, ta miƙe ta rungume Ablah ta mata kiss ta fice da ɗan gudunta tana dariya tace" se na dawo." Ablah da Lubah suka ce"a dawo lfy." Mamu tace"Ameen"

Tana fitowa haladu ya bude mata mota ta shiga suka kama hanyar makaranta.

Kamal yana zuwa ya shiga Office ɗinsa ya jima yana nema takardun kafin ya samu, ashe wai ƙasan table ɗin suka fada. Tsaki yaja ya shiga toilet ya wanke fuskar shi ya fito. Ya dauki takardun sa ya nufi kofar tafiya yana kallon tsadaddan agogon hannunsa yaga 3:40 pm, tsaki yaja ya buɗe kofa ya fito ya murza key ya zare ya fara taka matattakalar benen a nutsu, karaf idanunsa ya sauka kan Mubina da take fitowa daga mota waya manne kunnenta tana sakin kayataccen murmushi dimple ɗinta na lobawa, siririyar wushiryata ta baiyyana. Idanu ya zaro ganinta da wannan shigar barin yadda halittar ta ta baiyyana, boobs ɗinta kamar su fasa rigar su fito, ga hips ɗinta sun fito. Idanu ya zuba mata ganin haladu ya juya yaga ta nufi Basma da gudu jikinta na dan motsawa barin boobs ɗinta, juna suka rungume suna dariya se yaga iyamu ta nufo gunsu tana murmushi. Kamal wayar sa ya ciro a aljihun wandan sa yay dailing ɗin number Amrah, bugo ɗaya ta ɗaga cikin ɗaga murya ya fara mgn" sweethear wai me yasa umpah ya sama yarinyar nan idanu take son lalacewa ne kin ko ga da kayan da ta fito yanzu?" ya faɗa da ɗan karfi. Amrah se da ta zabura tace" Wlh ba ganta ba ina bangaran Laure mai aiki dukanta nayi na gudu , amman naga su Mamu ai suna parlour ko basu ga fitar ta ba, dan Allah my hubbi ka korota ta canza kaya kuma nifa ina zargin gun party ne zasu dan na kamata tana waya cewar yau da yamma basu da lecture da tajini ta canza mgn." Kamal ya fesar da zazzafar isa waje yace"Ina zuwa sweetheart zan kiraki." ya faɗa yana tsinke kiran. Ya karasa saukowa ƙasa ya nufi gunsu Mubina. Mubina Tace Basma "kinsan wani abu yau so nake mu ƙure kausar anya ba da motar aro ba ake kawota makaranta ko ta makwafcin su ko saurayi? shegiya me zubin samudawa ai yau sai mun ƙureta muce zamu gidan su dan kara zumunci , kinga daga nan mun san gaskiya an ishemu d akaryar banza shegiya me zubin inyamurai..." Basma ta bushe da dariya tace" Wlh ba ruwana wannan idan ta kama mu ko har zawo mayi..." Iyamu ce ta isu wajan su tace"Wow baby Mubina wlh kin hadu fa Basma ma kinyi kyau sosai." Basma tace "tnx anty iyamu." Mubina ta haɗe face tace "Su Aunty iyamu gulmar me aka kwaso ne naga ba wani harkar juna muke ba?" Iyamu tace" Kai baby ke fa matsalata dake masifa kuma kuna zuwa partyn laweesa ne?" Mubina tace"yauwa ni nasan da walakin goro a miya , to eh muna zuwa se akayi me?" ta faɗa tana kama hannun Basma suka kama hanyar fita. Iyamu tace"Muje nima can zani shiyas naki shiga lecture , Leeza har ta tafi ga." Mubina ta murguda baki ta buɗe bakin zata yi magana kenan suna dab da fita daga get ɗin makarantar taji an fizgota da karfin gaske tayi tagal-tagal zata faɗi yay saurin tarota ta fado jikinsa ya ɗauketa da gigitaccen mari biyu wanda duhu ya baibaye mata ido ta rasa jinta da ganinta nan take. Wani gigitaccen ihuuuuu Mubina ta saki bata ganin kome sai baƙi cikin idanunta. Basma da iyamu suka ja baya da sauri suna neman hanyar guduwa....

Hkr da rashin Editing me kyau ina busy ne😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻**💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Free Page*

🅿️1️⃣9️⃣
Chapter 31 · 0% Book details