← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 124

Sashe 92

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamal yana gama alwalla ya fito yaga wayam bata ɗakin, murmushi yayi yaji daɗin tana sanye da hijabi, yace" tayi fushi fa." ya faɗa yana nufar kofar fita. Zai buɗe kofar ya fito su ummi suka shigo tana riƙe da hannun Mubina, itako koda wasa bata yarda ta kalleshi ba. Ummi tace"shirman tama ta gudu ko?" Kamal cikin ladabi yace.
Ni nama shiga alwalla ta fice." ummi tace ƙirawo Dr ya sallame mu tinda taji sauƙi, daman yace da zaran ta farka zamu iya tafiya." Kamal ya amsa da"Tom" ya fice. Mubina ta bishi da harara. Ummi tace"Yau naji ikon Allah wai me ya miki?" Mubina ta ɓata rai tana diddira ƙafaɗunta, ta nufi toilet. Ummi tana cikin haɗa kayansu Kamal da Dr da Makel suka shigo da sallama. Ummi ta amsa, Mubina tana fitowa Dr zai dubata Kamal yace"No Dr na dubata bamu sallama kawai." Ya faɗi yana haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba. Ɗan baturan dariya yayi ya maidama Kamal da yaran turancin yace"Ok biyoni ka mashi takardar." Kamal ya bishi Mubina tace"To ina ruwanka ma kawai shishigi kai me zuwa gun karuwa fa to sai an dubani ɗin Dr zo ka dubani ba jikina bane." Juyowa Kamal yayi ransa a mugun ɓace, ya watsa mata wani irin kasheɗi ta idanunsa. Da sauri ta kawar da kanta tana lumshe idanunta, tsikar jinkinta na mimmiƙewa. Ummi tace"Tab wannan kuwa zai barta tayi karatu? wai wai." Mubina jikin ummin ta shige tana gunguni.
Kamal bai jimaba ya dawo da takardar sallama ɗin yace"Ummi harda magani za'a siya kuma babu anan pharmacy ɗin sai mun shiga gari gashi lokacin sallah yayi." Ummi tace ai kuje kawai tinda kasan gidan sai kukai idan ka sayo bari na ƙira Majeed kafin yazo munyi sallah." Kamal ya ɗaga kansa yana kallon Mubina wacce taki yarda ta ɗago ma. Kamal yace "Muje ummi sai mu ajiyeku." Ummi tace A'a kuje dai kayi salla sai ka amso maganin yanzu Majeed yazo sai ya kaimu." Cikin girmamawa suka mata sallama shida Makel yana ma Mubina magana ta shareshi, haka suka fice. Ummi ta ƙira Majeed yazo ya kaisu gida, yace "suna hanya da papansu ma"

Su Mubina na gama sallah su Majeed da papa Saleem suka iso, Mubina ta gaishesa yace"Sannu Amarya ya jikinki?" fushi tayi tana neman kuka, papan ɗin ya lallaɓata ya kama hannunta suka fito suka nufi compound ɗin hospital ɗin, ummi da Majeed suka ɗauki kayansu suka bi bayansu, Majeed sai kumbure² yake. Suna zuwa mota ya buɗe mata seat ɗin baya ta shiga ta zauna, ummi na zuwa ta zauna kusa da ita, papa na zaune kujerar me zaman banza, Majeed ya zauna mazauni direba yaja motar da karfin gaske yabar hospital ɗin. Mubina a hankali ta rungume ummi ta shige jikinta tana baza hancinta, har yanzu daddaɗan ƙamashin turaren Kamal da ta shaƙa, yana manne a hancinta da wanda ya manne a jikinta. A hankali ta ƙira sunnan"Ummina."ummi tace"Na'am Mubina ya akayi?" Baki ta turo gaba tan alumshe idanunta bata iya magana ba tayi luf abinta. Murmushi ummin tayi, bata sake magana, sosai Majeed ke zuɓa uban gudu, saida Papa ɗin ya masa faɗa ya rage...

Umaimah kuwa ana zuwa hospital da ita, aka masheta aka shiga bata temakon gaggawa, domin ceto rayuwarta. Saida aka kwahe kusan awa ɗaya cur akanta kafin ta farfaɗo. Tana farkawa sunan Kamal ta ambata tana sambatu. Saida aka mata alluran bacci. Yumnah na zaune kusanta tana riƙe da hannunta wanda aka ɗaurana drip. Jafar da Anwar suka shigo da sallama. Yumnah ta amsa, tare da cewa. " Wai kana nufin haka zamu bar ƴarmu cikin ƙunci har ta rasa ranta alhalin abin baifi ƙarfinmu ba?" Jafar ya karaso ya zauna bakin gadon ya zuba ɗiƴar tasa idanu yana jinjina kai....

*~Real Ladingo ce Oummu Fareesa~*😘

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣1️⃣&2️⃣2️⃣

Yace"To Suwaiba ya kike so ayi ne? Yaron nan an É—aura masa aure yau É—inan, to kuma sai na sake matsama mahaifinsa akuma É—aura masa wani auran...? Idan mijintane zakika ya aureta da yarda Allah, muyi mata Addu'a, ko nace muyi masu Addu'a idan da Alkhairi Allah ya tabbatar." ya faÉ—i yana kama hannun Umaimah, wacce take bacci. Yumnah tace"Hummm Amin to, amma ni gaskiya bana son wani abu ya sami Æ´ata." Anwar yace.
Yumnah insha Allahu kome ziyi daidai Allah ya bata lafiya." suka amsa da "Amin." zuciyoyinsu babu daÉ—i.

Majeed na isa gida bayan ya gama parking, Mubina ta buÉ—e mota ta fito, ummi ma ta fito suka nufi ciki. Parlon suka shigo da sallama. Natalee na zaune dasu Azeema da Aleem suka tarbi su, Mubina Azeema ta rungume Mubina, Aleem ummi suna masu oyoyo.
Mubina ta zauna tana maida numfashi, tace"Natalee kawomin ruwa me sanyi a fridge." ta amsa da "Tom" ta miƙe. Papa da Majeed suka shigo suka zauna. Natalee na kawoma Mubina ruwa ta amsa tasha, ta miƙe ta nufi bedroom. Ummi tace"Baby kiyi wanka kifito kafin mijinki yazo, ya kawo maganin kisha kar zazzaɓi ya dawo ko?" Mubina ta yamutsa fuska, kamar zatayi kuka tace.
"Ummi ni bana son magani..."Sallamar Kausar ta katse mata mgn, ta tafi da gudu ta rungumeta, tana mata oyoyo.
Kausar tace"I miss u haba sahiba ina kika shiga ne? Nayi ƙira phone ɗinki switch off, dakyar na yini makaranta yau nayi missing ɗinki sosai " Mubina tace.
"Me too muje ciki yanzu fa nazo daga hospital banida lafiya."ta faÉ—a tana wani yamutsa fuska. Kausar ta zaro idanu tace"Subahanallahi! Sannu." ta faÉ—i tana sakin Mubina ta isa wajansu ummi ta gaishesu. Ummi tace.
"Sai da kika gama da ƙawarki ko?" Kausar tayi murmushi, ta kalli Majeed tace"Yayanmu ba mgn ma ko?" Murmushi yace"Ai naga bakya tamu shiyasa."Mubina tace"Nima yaya Majeed yau baya wani kulawa dani sai shareni yake." Ta faɗi tana kama hannun Kausar, suka nufi bedroom, Azeema na biye dasu. Majeed ya miƙe yana cincin magani ya fice. Ummi tace.
"Ikon Allah wai kai dawa?" Papa Saleem ya miƙe yana murmushi yace"Keko yasha kanwa mana."Dariya ummi tayi tace da Natalee.
"Muje kitchen mu girka mai dan sauƙi." Mubina suna zuwa bedroom ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel ta shiga bathroom ta haɗa ruwan gumi tayi wanka sosai, ta dauro alwalla tana fitowa ta goge jikinta suna hira da Kausar tana bata labarin an ɗaura mata aure, ta shafe jikinta da lotion mai azabar laushi da ƙamshi ta gyara gashin kanta, ta shafa man kai me shegen ƙamshi ta ɗaureshi da ribbon. Ta buɗe akwatinta ta ciro riga ƴar kanti wata pink me bin jiki, gata da laushi ta saka ko breziya bata saka ba, ta feshe jikinta da turare mai ƙamshi. Ta shiga neman wayarta, bata ganiba ta saka abaya da hijab kan kayanta, ta tayar da sallar isha. Kausar ma sallar tayi. Mubina tana gama sallar ta cire abayar, ta nufi saman bed ta kwanta tana lumshe idanunta, tana ma Kausar bayanin auranta da Kamal ba Sageer, ba cewar bata ma sonsa sam.
Kausar duk inda Mubina tayi kallonta take har ta kwanta tana mata hira bata son Kamal dan Mubina ɗin tayi kyau sosai. Mubina kuwa sai zuba² take idanunta a lumshe. Kausar ma zauwa tayi ta kwanta, tana kallon Mubina tace.
"Sahiba kinyi kyau sosai kibani rigarnan, wai waye Kamal ɗinan da ya kasa Sageer?" Mubina tayi kyalkyale da dariya ta miƙe ta sauko ƙasa tace.
"Bari na amso wayar ummi na ƙira su Umpah da Mamu da Ablah nah Aunty Amrah nah duk mu gaisa, ni bansan inda wayana take, daga can na dafo mana indomie muci." ta faɗi tana ficewa cikin takunta mai dauke da nutsuwa...

Ɓangaransu Kamal kuwa bayan subar hospital can masaukinsa, suka nufa suna zuwa bayan yayi sallah, ya shimfida sabon zanin gado ya feshe ɗakin da turare, ya ciro wasu haɗadɗun kayan bacci ya ajiye saman bed ɗin haka cikin kayan da ya siyoma Mubina ya zabo wata shegiyar rigar bacci iya cinye pink ce me santsin batada maraba da tsirara igiyoyin gaban rigar masu masifar kyau, ya haɗa da nashi ya feshesu da turare, haka blanket ɗinma wanka turare ya masa..... Bayan ya gama shirya kayan baccinsu da gun kwanciyarsu, ya ɗauki waya ya ƙira, Umpah bayan sun gaisa yay ta masa godiya, ya roƙi Umpah kan yanaso zai wuce da Mubina saudiya gobe da dare can zasuyi azumi, da zaran anyi sallah zasu dawo nan maradi zai mayar da ita nan Maryam Abacha ta ƙarasa karatunta. Umpah bai nuna damuwa ba, nan ya amince sanin Kamal yafishi iko da ita ayanzu, nan ya masa godiya yace abashi su Mamu da Ablah.... Haka ko Umpah ya bashi Mamu da Ablah saka gaisa ya masu sallama. Nan ya ƙira Hafsat ya faɗa mata koma, dariya tayi tayi tana mamakin yaushe Kamal ya fitsare haka? Har ya iya ƙiran suruki zai ɗauke matar sa...?
Kamal kuwa bayan ya gama duk abinda zaiyi bayan yay sallar isha, suka sukaje pharmacy suka, sayi maganin Mubina, daga can kuma ya tafi nema Mubina biza ta gaggawa, uban kuɗi ya kashe saboda Makel ya masa hanya zai samu, amman sai jibi hakan ma yaji daɗi bayan sunyi duk abinda zasu an kuma tabbatar masu jibi jirgin dare zai tashi dasu, hankalinsa ya kwanta, dan Umpah yace ya jira zai ƙirayi Papa Saleem zaije makarantarsu Mubina gobe ya amso takardunta na makaranta ya bashi. shiga gari Kamal da Makel sukayi dan bayaso yaje kai maganin da wuri.
Chapter 92 · 0% Book details