Sashe 48
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mubina kuwa numfashi kawai take fitarwa sama-sama bata san inda kanta yake ba. Kamal na laɓe Yana kallin su umpah suka iso wajan, a farko basu ganta ba sai da Amrah ta fasa ihu ganin Nunus ɗin kare harshe waje. Umpah ya ga Mubina a yashe tana fitar da numfashi sama-sama, Aguje yay kanta yana cewa"Baby tashi kare ne ya tsorata ki ashe , sam Baby bakya son kare."ya faɗa ya sunkuyawa ya kamata. Security ɗin suka ɗauke Nunus ɗin, suna cewa"Ai shiyasa wannan suke ta nan, to me ma ya kawota ta nan ne?" ɗayan yaje da gudu ya ɗauko gora ruwa me sanyi, ya kama Umpah na rungume da ita yana kiranta ta buɗe idanunta, Amrah kuwa na murza mata tafin hannunta tana cewa, "Baby buɗe idanunki ba karan gaske bane..."
Security É—in ya bada ruwan, Umpah ya yayyafa mata kan fuskarta, wawar ajiyar zuciya ta sauke da karfi, ta fashe da kuka tana cewa"Kamal ka fita a rayuwata, don Allah karka kuma cutar dani, wlh na tsaneka tsana mafi muni a rayuwata, Allah ya isa..."Umpah ya rufe mata baki yace"Baby ba Kamal bane buÉ—e idanunki, kinga Nunus É—in kare ne ya firgitaki..."
A hankali na buɗe idanuna wanda suka min nauyi na kalli Umpah da gurin da muke ina hawaye, nama rasa ta ina zan fara, na kalli Amrah ina shasheƙar kuka nace"Aunty wallahi Kamal ne amman baza ku yarda ba." na faɗa ina tofar da katuwar chocolet ɗin bakina. Kamal kuwa rumtse tsumammun idanunsa yayi ya dafe kansa, a hankali ya furta"Am sorry Mubina..."
Umpah ya miƙar dani tsaye yana cewa"Baby wlh kin firgita da ganin Nunus ɗin kare ne ba Kamal bane."shiru nayi ina share hawaye na sanin duk yanda akayi bayan na suma Kamal ya ƙulla min wata kutunguilar ne, bai bari su Umpah sun ganshi ba tare dani, amman Allah ya kubutar dani bai sami dama a kaina ba! Yasa na goge hawayena, a hankali na furta"Allah ya isa mugu..."
Kamal ɗan karamin bakinta yake kallo yadda yake motsi ya gane Allah ya isa take masa, sbd su Umpah sunki yarda cewar shine. Umpah yace"To yi hakuri dai muje."ya faɗa yana riƙe da hannunta, Amrah na riƙe da Azeema suka fice daga wajan, security na biye dasu. Umpah yace"Auta kayan naki suna ta ina ne"Bakina na zumbura na nuna masu da yatsa.
Securityn suka nufi wajan suka suka turo kayan. Suna zuwa gun biyan kudi aka masu lissafa kome Umpah ya biya, har Manager ɗin gurin na tsokanar Mubina yanda ta lafe jikin Umpah, cewar taji tsoron kare ta kausa suma nan ya faɗa masu shiyasa aka ware masu can ciki sai masu buƙata ake kaiwa wajan dan yara da mata ɗayawa na tsoro. Suna fita Umpah ya sata gaban mota su Amrah a baya suka rankaya gida sai lallaɓata yake tayi lamo jikinsa idanunta a rufe wani irin daddaɗan kamshi take ji na adabar hancinta sai bubbuɗe hanci take tana sauke ajiyar zuciya...
Kamal kuwa sai da ya tabbar zuwa lkcn sun fice daga wajan ya fito jikinsa duk wani iri kamshin jikin Mubina yana adabar hancinsa sosai yake jin daɗin ƙamshin. Zagayawa ya fara yi waje-waje yana jidar duk abinda ya bashi sha'awa, siya yake, bai jima ba yaje aka buga masa lissafi ya biya kudin, ya ɗauki ledojin har biyu ya fice.
Yana fitowa ya buÉ—e set É—in baya ya zuba kayan ya rufe ya shiga yaja motar, yabar wajan.
Kwana É—ayace ya sha se gashi a kofar get É—in makeken gidan sa wanda yaji kome na rayuwar duniya. Horn yayi har sau biyu kafin megadi yazo ya wangame masa katon get É—in, ya shige da motar.
Bayan Kamal ya fito sun gaisa ne ya nufi ciki. Wasu irin makullai ya zaro daga aljihunsa ya zura jikin kofar glass ɗin ya murza ya buɗe kofar, ya sanya kansa cikin haɗaddaɗan parlon mai wasu irin dirka dirkan kujeru manya-manya, wata tafkekiyar TV manne jikin bango wanda bango ɗakin kansa wasu irin adone masu walkiya ko wacce kusurwa manya pic ɗin Kamal ne manne wani yana dariya wani yana murmushi wani ya dan sha ƙamshi, wasu da kananun kaya wasu da manyan kaya. Gabaki ɗayan parlon malale yake da wasu carpet lumtsuma lumtsuma masu taushin gaske. A nutsu yake taka steps ya haye saman bene. Wata hamshaƙiyar bedroom ya shiga tsayawa faɗin kyan ɗakin ɓata lokacine. Katuwar wardrobe ya buɗe ya jidi kaya kan kananu kan manya sama da kalla goma ya zuba cikin wata akwai mai shegen kyau ya ɗauki takalmai ya zuba, ya kwashi wasu takardu ya zuba da leptop guda ya rufe babbar akwatin ya janyo ya fito ya murzama ɗakin key ya zare ya sauke ƙasa yana janye da akwatin. Yana sauka bai tsaya kome ba ya fito ya faɗa mota yaja ya nufo get. Nan yace ma megedi da mai ba plowers ruwa zaiyi ƴar tafiya se yazo suna kula da gida Umpah zaizo yana kawo masu kaya na buƙata kafin yazo, suka masa Addu'ar sauka lfy ya tafi.
Kamal yana fita kai tsaye Makaranta ya nufa gashi ana yayyafi, yana zuwa bai jimaba yayi abunda ya kaishi, ya fito ya nufi Company sai murna suke Oga ya fito nan ya saki fuska suka gaisa, yana zagaya ko wane guri É—aya bayan É—aya, ya sami Manager sukayi mgn yace zaiyi tafiya kwana uku rak, nan Manager yay masa fatan alheri yace daman Umpah ya faÉ—a masa... Kamal na fitowa daga Company ya kama hanya, Yanma ya nufa wato hanyar Naimey yay yana kwarara gudu sosai, Kamal a sauka lfy babban birnin Naimey.
Su Mubina suna zuwa gida ta faɗa jikin Mamu tana kuka tana faɗa mata abinda ya faru. Nan Mamu hankalinta ya tashi tace"Wlh a yanzu karyasa tayi karya..."Umpah yace"Nusaiba ki fa saurare ni, Baby ta firgita ne bari kiji abinda ya faru." Nan suka faɗa mata kome shida Amrah. Ablah tace"Ai wlh dole idan maciji ya tsareka sau ɗaya idan kaga baƙin tsinma ka gudu..."Mamu ta ɗago Mubina zatayi magana taga bacci ma take tana sauke numfashi a sannu sannu ta lafe luf jikin Mamu. Mamu tace "baiwar Allah dole Kiyi bacci."ta faɗa tana kwantar ta saman doguwar kujera ta gyara mata kwanciya ta, tace"Amrah ɗauko wancan hijab ɗin rufa mata." Amrah ta dauko ta rufa mata.
Umpah yaba Abalah dabinon yaba Mamu tsarabarta da Sabeela yana cewa"Wai ina Majeed ya shiga da Aleem?"Sabeela tace"suna fa gun Kabeer yau sun kai masa ziyara." Ablah tace"Abdul Allah yayi albarka bari naje na adana kar wannan barauniyar ta sace."ta fafa tana nuna Amrah. Amrah tayi dariya tace"ga barauniyar ki nan dai na bacci." Umpah ya miƙe jin ana kiran sallah la'asar, ya shiga yayi alwalla. Nan suko suka kama hira, ba jimawa Baba megadi yayi sallama ana kiran Amrah. Amrah ta zaro idanun tace"Wlh ba dai niba tab sai de Mubina..."Mamu ta buge mata baki tace"Ba Mubina ba dai! Mubina me ruwanta? Tashi maza kije." Amrah ta miƙe tana kumburo-kumbure ta fice. Ablah tace"Ja'ira ko dafata zamuyi muci ai aure dole zakiyi aure ba kanki farau ba." Ablah ta faɗa tana miƙewa, ta nufi cikin bedroom ɗinta domin yin sallah. Sabeela tace "Allah yasa nagari ne"Mamu tace "Ameen"Sabeela tace"da Umpah ya yarda me zai hana a haɗata da Majeed taje London tai zamanta tinda Saleem bayada ra'ayin koda yayi ritaya mu dawo sai ganin gida tinda Allah ya malaka masa gida a can..." Mamu tace"Ai naga kamar fa da kaɗan ya girme mata? To amman wannan shawara kuyi da ɗan uwanki Sabeela..." Mamu ta faɗa tana miƙewa tace"Muje muyi sallah."Sabeela ta miƙe guiwa a sake ganin kamar Mamu batayi na'am ba.
Amrah na zuwa bakin get taga Lameer tsaye bakin mota ya haɗe cikin shadda me kyau ruwan ƙasa. Masha Allah ba laifi Lameer yana da ɗan kyansa dai dai misali gayan akwai ɗaukar wanka.
Karasowa tayi tana cicin magani ta masa sallama, Lameer yace"Amincin Allah su tabbata a gareki dan Allah kiyi hkr wlh na ganku a Super market ne, so daman naji ƙishin ƙishin ɗin an fasa auranki, ban yarda ba sai yau yanayin shigarki ya tare da ƴan gidan ku ya tabbatar min bakiyi aure ba! Pls ki bani dama wannan karon nazo da karfina dan Allah My Amrah nah?" Amrah tace"Ok zanyi shawara insha Allah zaka ji ni zan kiraka idan naji hakan yamin , zan nemi zaɓin Allah cikin lamarin Ngd zan shiga ciki..." ta faɗa tana juyawa. Lameer ya mata godiya ya shiga mota ya tafi itama ta shige gida.
Kamal sai karfe goma na dare ya sauka babban birnin Naimey, haÉ—adÉ—iyar Hotel ya kama bayan yayi wanka yayi sallah isha, dan sauran yayi kan hanya, ya saka aka kawo masa coffee kawai da cake mai rai da lfy yaci bayan ya gama yayi kiran wata number meyace meyace oho ya jima dai yana wayar kafin ya gama kashe wayoyinsa duka, ya saka kayan bacci yabi lafiyar gado, bai jima ba sai bacci... Washegari ma cikin hada hada ya yini tinkur, Sageer da ya dame sa da kira idan ya É—auka yana tambayar sa ina ya shiga? Ya faÉ—a masa yana Naimey gobe zai dawo. Saida Kamal ya kwana uku Naimey ya gama abinda yake gamawa tsaf...