Sashe 57
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka su Abbu har aka sakota kullum safe da yamma se sunje dubata, Safiyya sosai take son Mubina tana ji da ita, tamkar a bata ita suje Kebbi haka take ji. Su Abbu sun sayi galan ɗin manja aka soye aka daka yaji kusan tiya da rabi yaji maggi da bahun agwaluma🤣, suka kawo hospital wai kar ya gabce, aikuwa Mubina se daɗi take ji, shi ne abun shan Mubina shi kadai ne baya sakata amai, yajin kuwa har daddagawa take a yatsa tana lasa tana tandar baki ko ta zuba manja ta zabga abun yaji ta cakuda tana sha, tana sama Ummah da Abbu albarka. Basma ma kullum da ta taso daga makaranta tana hospital gun Mubina, ta sata gaba tana kuka ganin yanda ta dawo, Hajiya Lubah ma da Isma'il sun zo dubata, se dai Lubah kallo ɗaya tama Mubina ta gano cikine da ita, abun ya girgizata bata san lkcn da kuka ya kwace mata ba,. Mamu tinda ta gano taga babu wani ɓoyo, jan Lubah tayi suka keɓe dan Kar Mubina taji, dan sun kasa faɗa mata so suke sai Sunje London, nan tsaf ta bata lbrn kome, Lubah ta tausaya masu, ta bada shawara kawai a kaita London ɗin tayi karatun har ta haihu zata fi samun nutsuwa....
Bayan sun dawo ma dai gidan aman take, se dai tana ƙoƙarin cin taliyar da yaji da agwaluma ɗin, se kuma wake da shinkafa.
Mubina washegarin zauwarsu tayi shirin zuwa makaranta, Umpah ya hanata zuwa makaranta dan yana can ya haɗe takardunta yana shirya masu tafiya London Biza kawai suke jira, ita sam bata da ma labarin tafiyar gashi har jibi zasu ɗaga, amman har Basma ta sani tayi kuka jin abinda ya faru da Mubina kamar ranta zai fita, har zazzaɓi tayi, tana tausayin Mubina ta tsinema Kamal albarka yafi sau dubu dari. Mubina tinda suka dawo yau kwana biyu bata kunna waya ba, kenan sati guda tana ta jinyar kanta bata kunna waya ba, duk da ɗan kurma na cikin ranta, amman ta share wai tayi fushi dashi...
Bangaran Kamal kuwa a kullum se ya kira Mubina amman awitch Off, hankalin sa sam ba a kwance ba, tinda yaga sakonta cewar tana hospital tin ranar da ta masa fishi ta kashe wayar, amman baya son ya takura Sageer har ya gano shine Kamal, shiyasa ya hakura ya share yana me Addu'a Allah yasa lfy take ta warke fushi ne dai kawai ta masa, ya maida hankalinsa gun bautar ubangijin sa tare da Addu'ar Allah ya tona asirin su Mounkaila da Tukur da Iyamu da Leeza, Allah yay masu abinda suka masa...
Misalin karfe biyar na na yamma agogon Saudiya, Kamal ne zaune a cikin haɗaɗɗan parlon sa sanye da 3 qourter se singileti fara cup glass a hannunsa yana kurɓar gahuwa, dan yanzu ya saba da ita sosai yana shanta, yanzu fitowarsa daga Kabah tin sallah la'asar da aka gama yake zaune yana Addu'o'insa, se yanzu shigowarsa ya cire jallabiyar yana hutawa a haɗɗaɗan parlon sa mai masifar kyau, ya ƙurama Tv idanu tashar Al'jazeera, Yau ta kama Jumma'a ne Kamal baya fita gun Aiki wanda Kawunsa Jafar ya samo masa, a Babbar Universityn da ke cikin garin Makka ɗin. Sbd yana tare da manyan ƙasa gashi takardun Kamal zai iya shiga kowa ƙasa a duniya ya koyar da Al'ummah abinda zasu anfana, bai jima ba sosai amman ƴaran larabawa matasa maza da mata najin daɗin yadda yake fahimtar.... Mazan ma najin dadin hakan barin yanda Kamal yake larabci tamkar balarabe, shiyasa yake da farin jini sosai a makarantar, kuma shima yana jin daɗin ganin matan jikinsu a rufe hatta fuskar su shiyasa hankalinsa kwance yake koyar dasu a matsayinsa na lacturer ɗinsu su.
Wayar sace ta ɗauki ringing, jikin sa na rawa ya beƙa hannun saman glass table ɗin gabansa, wanda ke shaƙe da kayan marmari. Sunan *Kawuna* yake yawo saman screen ɗin wayar, Kamal ya lumshe tsumammun idanunsa ya buɗe, a hankali ya firta "Kawuna ne, nazata Mubee ce ta huce ta kirani..." ya karasa maganar yana picking ɗin call ɗin ya kara wayar a kunnen sa bakinsa ɗauke da sallama.
Daga can Jafar yace
"Kamalu ykk da fatan Makkah na lfy yau ana gida ko?" Kamal ya shafi lallausar sumar kansa wacce take luf se sheƙi take ta ɗan zubo gaban goshinsa ka ɗan, yace"Kawu eh yanzu na shigo daga masallaci ina hutawa ne, yasu Mummy suke da Umaimah, zan daure na shigo Madinah ɗin na kwana biyu insha Allahu nayi missing ɗinku..." Jafar yay murmusa yace"Umaimah fa ta dame ni sai an kawota wajanka se da na mata da gaske , nace taya bakada mata zata zo nan fa saudiya muke ko bata ga ta girma ba, wai ah karatunta ne yake shige mata kwana biyu wai ka temaka mata, shine na saya mta waya jiya zan bata number ka nace ta kiraka zaka na koya mata duk abinda ya shige mata..." ya faɗi yana murmushi. Kamal yace"Ai ko Kawu kayi dede wlh nima bazan yadda tazo ba , duk da ƙanwace gareni amman mace da namiji idan suka keɓe na ukun su shaidan ne , kace ta kira ni naga number zan kirta naji matsalar tata, kawu yau kunyi waya da su Abbu kuwa...?" Jafar yace" Eh na kira ina so Na masa mgnr ka se naji tsoron kar ya zargi kana tare dani, se naki masa kuma yaƙi mani mgnr kai de ka zauna zaima min mgnr ya matsu de zai nemaka insha Allahu ba dai shi yace ka nesanta kanka dasu ba? akan abinda baka san taya ya faru kayi ne kan kuskure kuma na yarda dakai bazaka min karya ba , dan haka kaci gaba da haɗa wannan mutanan da Allah wlh se sun wulaƙanta insha Allahu, Se anjima zan fitane yanzu..."
Kamal yace"Kawu nagode bazan taɓa mantawa dakai ba..." Jafar yace"No bana son godiya kai ɗana ne halak malak, se anjima zamuyi waya zuwa dare." ya faɗa yana kashe kiran...
Kamal ya lumshe idanunsa ya dafe kansa, ya buɗe idanunsa yay dailing ɗin number Abbu, bugo ɗaya aka ɗaga da sallama. Kamal jin muyar Abbu raɗau babu wata damuwa ya kashe kiran, ya kira Ummah, lokacin tana gidan su Mubina tazo dubata, suna parlo zaune dasu Mamu da Ablah, wacce hsushin Ummah ya cikata, dan taga kamar son cikin suke. Tana fara ringing Ummah ta ɗauka da sallama. Jin muryata normal se dai muryar Mubina da ya tsinto cikin sanyi tana cewa,"Auntyna ki dafomin taliya idan na shanye wannan agwlumar zanci wlh yunwa nakeji, wayyo cikina yunwa Mamu Nah..." Kamal yaji wata irin faɗuwar gaba, kitt ya kashe kiran, yana cewa"Oh my God *Mubee* ya najiki sanyi haka ko har yanzu bakida lafiya ne? No kina lfy bari najiki yau ko Sageer zanma wayo se nasan yanda nayi ya haɗani dake naji muryaki da kyau , naji damuwarki *Mubee* ." ya faɗi yana miƙewa tsaye ya nufi bedroom yana takunsa mai cike da kuzari irin nasu na ƙarfafan maza. Yana shiga ya nufi kan dirowar gadon, yana zuwa ya duƙa ya buɗe dirowar ya ɗauki wayar da yake kiranta ita da Sageer ya kunnata, tana kunnuwa ya kira numbert switch Off, tsaki yaja yace"Sorry mana *Mubee* ki kunna wayarki, pls" ya faɗi yana kiran Sageer, jin ta shiga ya kashe ya tura masa sako kamar haka,
*Haba Dr Sageer wane irin sakaran Namiji ne kai haka? yarinya ba lfy bazaka kula da ita ba, ka tarairayeta ka bata kulawa ka cire mata damuwa, kai wato ba ruwanka ma ko da baku mgn ta waya ko? Shiyasa wayarta a kashe tsawon sati ɗaya, amman bazaka sata ta kunna ba ko? Daman ƙarayar so kake mata Wlh😒.* Ya tura masa, ya kashe wayar dan yasan
zai kira sa, yafi so yasa ta kunna wayarta, parlon ya dawo ya zauna, ya ɗauki wayar sa ya kira Hafsat a kashe wayar, tsaki yaja, wata number saudiya ta kirasa yaki ɗauka ganin ba sunah, yama miƙe yabar wayar na ringing, ya nufi bedroom ɗinsa, ya zuba hannuwansa cikin Aljihun wandonsa, yana ciza lips ɗinsa...
Sageer na driving yaga sakon ya shigo, ya ɗauki wayar yana dubawa, idanu ya zaro a zafafe yace"Wai uban waye wannan ne ke damun rayuwata da ta Babyna.?" ya faɗa yana karkata ƙan motar ya nufi gidan su Mubina.
Iyamu ce da Leeza tsaye bakin titi suna jiran keke napep, suna mgn ƙasa-ƙasa suna dariya baka jin me suke faɗa ba.
Ibrahim dake duƙe yana duba motar sa da taki tashi, ga suri yake zaije Companyn su Kamal. Karaf a kunnen sa yaji Iyamu tace" Ai kibar ƴan iska wai mu zasu ma wayo, ai tinda na cutar da Sir Kamal to bazan bar kowa ba wlh..." Ibrahim da sauri ya ɗago ya kalle su, se yay saurin barin jikin motar ya fara tafiya, cikin sa'a yaga me Napep ɗin ba kowa, ya tsayar dashi ya shiga gaba, me Napep yace"Alhaji se ina?" Ibrahim yace "Gun matan can zamu zakayi kamar zaka tsaya se kuma ka wuce nasan zasu tsaida kai so ka ɗauke su duk inda sukayi nake so kabi min su, pls zan baka ko nawa kake buƙata , ga motata can a kusan su yanzu zan yi kira azo a ɗauketa but kawai ina son de nasan ina soke." Me Napep yace"Ok an gama fatan ba cutar dasu zakayi ba ko?" Ibrahim yace"Wlh A'A wani zargi nake kuma daman cikin binki ce nake har yanzu ban sami wata kofa ba, so sunan da naji sun ambata ne se naji ko zan sami wata ƴar kofa ta dalilin su." Me Napep ya jinjina kai, yaja Napep ɗinsa ya nufi gun su Iyamu...
*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805*+22796515805**KAMAL NE*
*Book 1*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
3ï¸âƒ£3ï¸âƒ£