← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 124

Sashe 51

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin karfe biyu suka shigo da sallama farlon su Mamu na zaune, suna magana da Kabeer, Mubina ta fado jikin Mamu ta rungumeta tana lumshe idanu. Masha Allah ta kara kyau da fari ta ciko kaɗan, dole namiji mai lafiya zai so kasancewa tare da Mubina, gata dai ba ƙiba amman yadda kirjinta ya kuma cikowa da mazaunanta haɗe da hips, zaka so mallakarta cikin gaggawa, shiyasa Sageer yake mugun kishinta a yanzu, dan kwana biyu hijabi take sawa, ba yanda ta iya bata son ɓata masa yana faranta mata rai...

Basma ta zauna tana cewa"Mamu ina yini, yaya Kabeer ina yini." Kabeer ya amsa yana murmushi ya ƙura mata idanu, ta sadda kanta tana murmushi. Mamu tace"Kai ni karki karya ni daga ina kuke Basma? Haladu yaje ɗaukota bata nan Umpah yayi ta kirta masa faɗa, se da ya kirata tace kuna can gidan ku wai?" Basma tace"Eh Wlh Mamu can muka tafi se da muka yi sallah muka ci abinci tace muzo daga nan anjima se mu wuce school ɗin."

Mamu tace"Ayya yasu Lubah kwana biyu bamu haɗu ba?" Basma tace lfy lau."Mubina tabi ta ninniƙe Mamu tana famar nishi jikinta ya ɗauki rawar sanyi. Mamu tace"Ke baby wai lafiyar ki kuwa naji jikin ki gumi? Tashi to muje kiyi wanka kisha magani kafin lkcn zuwa school yayi." Mubina ta kwakwaɓe fuska tace"Ni bana sha magani, bari nayi wanka." Mamu tayi dariya tace"Eh jeki maza kiyi." ta faɗa tana kamata ta miƙe tana riƙe da ita suka nufi saman bene. Kabeer yace"My love ykk?" Basma ta zaro idanu ganin Ablah dake fitowa ta tsare su da idanu, ta miƙe da gudu ta haye sama. Ablah tace"Munahiki kace baka da budurwa?" Kabeer yace"Ai wannan ce ƴar gulma kawai." dariya tayi ta zauna tace"Ina su baby ba naji mgnr su ba...?" Kabeer yace tana sama ko zazzaɓi ma yake son kamata." Ablah tace"Abakin ka ja irin yaro..."

Mamu suna hawa sama ta saka Mubina tayi wanka ta fito daga ita sai towel ta faÉ—a saman gado ta rufe idanunta tace"Mamu ki rufeni da bargo na sami bacci kaÉ—an kafin mu wuce makaranta." Mamu ta rufeta tana cewa "baby masha Allah kin fara É—an kumari har naji daÉ—i wlh..." Basma tayi É—ariya tace"Wlh kuwa Mamu nima na faÉ—a mata, se ta dokeni."Mubina dai bata ce masu kome ba tana naÉ—e cikin bargo, dan sanyi take ji ga wani irin feelings na taso mata.

Mamu tace "Au dukan ki tayi......? Wayar Mubina ce ta ɗauki ringing, wace take cikin jaka Mamu ta beƙa hannu ta janyo jakar ta fito da wayar......

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*[03/08, 7:55 pm] +234 904 365 8619: *KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣9️⃣

Mamu ta kalli screen ɗin wayar taga baƙuwar number ce ba suna, ta waje ce tace"Baby amshi ki ɗaga naga number waje ce ba suna, waye?" ta faɗa tana janye bargon ta beƙa ma Mubina wayar. Mubina ta amsa tana lumshe idanu. Mamu ta fice tana cewa"Basma karki barta ta fara barcin nata fa." ta karasa mgnr tana ficewa daga ɗakin. Basma ta amsa da"to Mamu" tana kwanciya kusan Mubina.

Mubina kuwa ganin irin number da take kiran Sageer ne, yasa da zaƙuwa tai picking ta manna wayar kunnenta, cikin sanyin murya me haɗe da alamun rashin lfy tace"Hello waye pls?" shiru ba ayi mgn ba. Ashagwaɓe tace"pls mana ayi mgn ni ina jin bacci" ta karasa mgnr kamar zatayi kuka tana dan tari." tsinke kiran akayi, kitt. Mubina ta ciro wayar daga kunnenta taga an kashe kiran, tsaki taja ta ajiye wayar ta lumshe idanunta ja bargo ta luluɓe jikinta duka tana fitar da numfashi a hakanli.

Basma ta kara matsowa jikin Mubina ta ɗan janye lallausan bargon tana taɓa jikinta, tace"Kina da zazzaɓi fa Mubee kisha magani..." Mubina ta matsa jikin Basma ta maƙalƙaleta gam tana turo ɗan karamin bakinta gaba, tace"Ni bazan shaba, zan warke ai." ta faɗa tana hucin zazzaɓi. Basma tace"Ok sannu ɗan rumtsa kaɗan kafin mu tafi." kai Mubina ta ɗaga. Wayar karan sako ya shigo, amman sam bacci take ji taki buɗe idanunta. Basma tace"kin sami sako fa"Mubina tayi shiru dan bacci yana fizgarta.

Basma bata sake mgn ba ko kwakwaran motsi Mubina ta hanata, ta wani manneta kamar zata shige cikinta. A haka bacci ya É—auketa Basma kuwa idnunta biyu, so biyu ana kiran Mubina amman bata É—auka ba...... Se karfe uku da rabi suka tafi makaranta, shima daket Mubina ta tashi.

Abbu yana fitowa daga masallaci na nan cikin company wayarshi ta É—auki ruri, ya zarota yaga number Saudiya ce dai, murmushi yayi yace"Jafar bazan É—aga ba tinda Æ´ar zolaya ce." ya faÉ—a yana kashe kiran ya shiga cikin Office. Yana zama aka sake kira, ya É—auka yace"Allah ya shirya ka Jafar"yana faÉ—in haja ya kashe kiran, yana aikin gaban sa.

Ummah zaune a cikin parlo tana kallon Tv tashar télé Sahel, Samha na kwance tayi matashi da cinyarta, tana mata mita yayanta Kamal shiru...? Sumaiyya ce da Hafsat tare da safiyya kamar daga sama suka shigo da sallama. Ummah

tace"Lah me zan gani kamar Safiyya? "

Samha ta miƙe tayi kanta a guje tana ihuuuu"Oyoyo mummy nah tazo." ta faɗa tana maƙalƙaleta. Safiyya tace"Wayyo dota karki karya mama to."Sumaiyya tace"Samha mu banda mu ko?" Samha tana murna tace"Ai har ku fa momy." ta faɗa tana saki Safiyya, suka nufi gun kujerun.

Safiya tace'"Wlh Aunty Fati cewa nayi bazata zan ma Yayana , kawai se kun gani." Ummah ta miƙe tana cewa"sannu Safiyya ya hanya? Ai kuwa yau ke da yayan ki ne, kika taho baki fada masa ba ashe bazata kika mana, sannu da zuwa ina Muhseen?" ta faɗa tana kama hannun Suhailat ƴarta wacce zata kai 7 year.
Tace "Suhailat yan matan Kebbi sannu da zuwa zaki zauna niger ko? Wai da ita É—aya kika zo ne?"

Safiyya tace "Eh Aunty ai wlh banida kwanciyar hankali ne, dole sai nazo Kamal baya gari, kuma ba'a san inda yake ba, Zakiyya kuka take uncle baya nan, wlh ba shiri nace bari nazo naji me aka masa haka...?" ta faÉ—a tana kallon Ummah.

Ummah tace"Wlh Safiyya ba kome kawai dai, Æ´ar matsala ne suka samu da Abbu, to Allah dai ya kyauta, ina ma yarona Addu'a kuma naji a jikina yana lfy, insha Allah."ta faÉ—a tana jan hannun Suhailat suka nufi kitchen. Sumaiyya tace" Wlh Abbu ma ya damu ni kam na rasa me ke faruwa haka? Ga auran an fasa ida an tambayi Abbu yace Allah ne baiyi ba." ta faÉ—a tana tagumi.

Hafsat tace"Humm wlh Kamal yana lfy insha Allahu zai dawo gida amman ba yanzu ba..." Samha ta riƙeta tace" Momy kinsan inda yake ne?" Hafsat tace"ni ban saniba ki tambayi wan suka kora shi mana Samha." Safiyya tace"Anya kuwa Hafsat?" Ummah suka iso tare da Rahila me aiki, babban tire shaƙe da kayan motsa baki da ruwa da lemo, ajiyewa tayi kan table ɗin tana gaishe su. Sumaiyya tace"Rahila kwana biyu ya gida?" tace"lfy lau Sumaiyya ya yaran, bakuwa sannunku." ta faɗa tana juyawa.

Hafsat tace"Ai ni tana burgeni ba ruwanta."Ummah tace" ai fa to yanzu dai bismillah ku." Safiyya tace"Hummn wlh sai kun faɗamin inda yarona yake..." Ummah ta jinjina kai tace"Ok naji sha ruwan sanyi dai." Samha ta miƙe ta ja akwatin ta haura sama ta ajiye. Nan ta suka dan sha ruwa da lemon suka dan saki jiki suna hira kafin Abbu ya shigo suyi ta dan sun haɗa baki sai ya faɗa masu dalilin da ya kori Kamal...

Karfe shida su Mubina suka fito daga class, suna fitowa suka ga motar gidan su kowa anzo É—aukar sa, suka yi sallama kowa ya nufi motar gidan su.
Mubina na bayan mota zaune Idanunta lumshe, bata jin jikinta ga yawu na tarun mata a baki, dauriya kawai take, tana jin Haladu na mata mgn tayi banza dashi.

Wayarta dake cikin jaketa ta É—auki ruri, shnyayyun idanunta ta buÉ—e a hankali, tana yamutsa fuska buÉ—e zip É—in jakar ta ciro wayar, taga number É—azu ce tayi picking É—in call É—in, ta kara a kunnenta cikin sanyin muryata me daÉ—in sauraro tace,

"Hello waye ne pls ayi mgn mana?" ta karasa faÉ—a cikin Æ´ar tsiwa. Ba'ayi mgn ba aka tsinke kiran. Mubina ta ciro wayar daga kunnenta, taga an tsinke kiran, tace"kuji rainin hankali se a kira a kashe to bazan ske É—auka ba se na faÉ—ama my one." ta faÉ—a tana jan tsaki, zata maida wayar jaka, taga sako ya shigo ta buda taga ```Please ki bani amsa tambayata ta É—azu??.```

Idanu ta zaro tana duba sakon da taji karansa tin kafin su koma makaranta. ```Babyn Sageer pls meke damunki jikina ya bani bakida lfy naji muryaki wani iri,don Allah faÉ—amin meke damun ki pls Mubee???. ```

Idanu Mubina ta zaro ta sake karanta sakon har sau uku, tace"Waye wannan? Ya akayi yasan bana jin dadi? Ya akayi yasan Sageer na cemin Baby?" ta faÉ—a cike da mamaki.

Da sauri Mubina tai dailing É—in number. Bugu É—aya aka É—aga ba ayi mgn ba, Mubina tace"Hello pls waye ne? Ya kasan banida lfy? Ya kuma kasan Sageer na ce mani Baby to??" ta faÉ—a a É—an sangarce.
Wani sansanyan murmushi aka sakar mata aka tsinke kiran. Mubina kuwa, tinda sansanyar murmushin sa ya daki dodon kunnenta, ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya, tana jin wani irin kasala. Jin karan sako ta zabura ta buɗe idanunta ta ciro wayar daga kunnenta ta ƙura mata idanu tana buɗe sakon taga kamar haka,
Chapter 51 · 0% Book details