← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 124

Sashe 30

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*************** ******** ***************
*Bayan sati hudu*
Masha Allah su Mubina sun gama jarabawar su lfy sakammako yayi kyau ita da Basma sun shiga 200 level mataki na biyu, Mubina tana karatu sosai ɗuk iskancin da ke damunta, dan yanzu kusan kullum se ta taɓo mgn a makaranta. Mubina da Sageer sun fara soyayya babu laifi tana kula shi sosai, sbd yana mata duk abinda take so yana riritata, Sageer yana mugun son Mubina ya mutu sosai a kanta, shiyasa take ji dashi dan bata kula kowane namiji se shi duk ko yadda maza suke mata dafifi bata ko kallan su, dan Lameer ma da yaji labarin za'a ma Amrah aure har bikin ya matso gun Mubuna ya dawo, tako masa fitsara tas tace bata sonsa. shiyasa Sageer ya zage ɗanze ya kara himma wajan kyautata mata, a yanzu har su umpah sun san son da Sageer yake ma Mubina umpah yace mutiƙar tana sonsa da zaran ta kammala karatunta zai aura masa ita ya bashi amanarta. Kamal kuwa zuwa wannan lokacin shakuwa me karfi ta shiga tsakanin sa da Amrah, dan suna kula da juna suna son junan su, se dai yayi mamakin bata sake masa irin wannan sangarta da shagwaɓar da ta masa ranar nan ba, shine ranar ya tambayeta akayi katari Mubina na manne jikinta, tana jin kome tama Amrah raɗa ta kawo ta tayata hira ɗa irin muryata, Amrah na dariya ta bata Mubina tako kashe murya suka fara hira da Kamal se sangarta take zuba masa, shiko yana lallaɓata yace tana masa mgn da wannan murya tafi zaki. To wannan shine sanaɗin shakuwar Kamal da Mubina ta waya ba tare shi yasan ita bace, dan har wayar take sacewa idan ta faki idanun Amrah ta kira sa suna hira tana wani lumshewa tana mimmiƙewa tana zuba masa sangarta, harda kukan shagwaɓa sji kuma Kamal duk ya gigice yana tambayata me take so? Amman har yau bai gano cewar ba Amrah bace, shiyasa idan suna hira Amrah se yana jin wani banbarakwai yace ta masa mgn da waccen murya mai daɗin sauraro, nan zata yi dariya dan ta gano iskancin Mubina ne, dole take zagewa tana lankwashe murya ba laifi tana masa irin tata. Mubina ta fita batun Kamal karatun ta take, se ta wayar Amrah kadai ne take kulashi tana masa iskanci ba tare da ya sani ba. Haka shima ko ya shigo gaishe dasu umpah bata masa magana se Mamu ta ƙaniyeta take gai shesa tana turo baki.
Kabeer bayan yazo da sati É—aya ya huta sosai kullum suna tare da yan gidan su Mubina ko nan da can bata gusawa se idan tana makaranta. yana cika sati ya kama aikin sa a nan *BIA Bank* sosai sun shaku da Basma duk ba soyayya suke ba.
Zakiyya ta haihu sati uku da suka wuce, ta sami ƴarta mace taci sunan Ummah Fatima, sosai Kamal yaji dadi yarinyar nashan gata, yan kebbi sun zo suna sosai akai shagali, cikin dangi. Amrah da Mubina da Basma nan suka yini ranar sunan. Auren Kamal da Amrah ya gaba to saura 10 days sai gyara amarya ake ciki da bai ɗinta, sosai Mamu take tsuma ta da gyarata har an fara mata murza jikinta se sheƙi da kamshi da santsi yake, Mubina tace bata yarda har ita ake gyaran, amman baika na Amrah ba haka kayan shaye-shayen ma sata take tana bankama cikinta, ranar da Mamu ta kamata se ɗa taci duka ba kadan ba. Umpah ya fara masifa yana faɗa seda Mamu ta faɗa masa ilar abin idan ya ratsata ba tare da za'a mata aure nan kusa ba, dan na amare ne... Su Mamu da danginta se shirye-shirye ake kullum cikin siyayya ake, wasu irin kayan kitchen da gadaje umpah yasa aka ma Amrah odar su daga dubai ita ma... Haka wajan su Ummah ma se shirye-shirye ake odar Kamal ta iso daga dubai ta kayan lefe, wai akwaiti ne set 3 wanda su kadai ka kalla kasan bana kananan kuɗi bane ba! Kaya kuwa ba'a maganar dangi se son barka suke. Jibi za a kai lefen. Tamfatsetsan gudan sa wanda yake nan cikin *Zaria 2* kusa da Kalla transa mall, gidana na kece raini ya hadu ba karya, an gama fanti ɗin ruwan toka da fari wai gidan ya hadu ba karya Suwwing pool a gefen dama gabaki ɗayan gidan dauke yake da shukar plowers me ƙayatarwa iri iri masu bada wani irin launin kamshi na musamman, ga wani tafkeken lambu ga rumfar shan isaka gefe ta ajiye motoci se ɗakin megadi dana meba shuka ruwa suna haɗe da wanda zai rinƙa wankin kaya, ya tanadi duk masu masa aikinsa, saura masu girkin su dana ma'aikatan gidan kawai ya rage, gidan Kamal duk wanda ya masa kallo ɗaya se ya sake...

Misalin karfe uku na yamma Kamal ne zaune cikin hadadɗan Office ɗinsa na company, saman wata lumtsumemiyar kujera, sanye yake da 3qourter da rigarsa iri ɗaya ruwan kwai sun masa mugun kyau sai wani sansanyan kamshi ke tashi a jikinsa, gashin kansa iska na kaɗawa, farin glass manne kan kyakyawar fuskarsa me ɗauke da saja wanda ya zagaye fuskar, haɗe da ƴar ƙasumba hakan ba karamin kyau yay ba... Waye manne a kunnesa yana magana yana danna laptop alamar ana faɗa masa mgn yana rubutawa a jikin laptop ɗin. Kusan 20 munites ya cire wayar daga kunnesa ya ajiye saman table ɗin ya shiga duba takardu yana dube-dube, can ya dafe kai yace"Oh my god na manta a Office ɗin makaranta." ya faɗa yana miƙewa tsaye, wayarsa ta ɗauki ringing, ya ɗauka yana mgn,dayar ma ta ɗauki ringing ya ɗauka ya saka aljihun wandon sa ya fito. Sakatarensa ya miƙe yana cewa"yallaɓai kana da baƙi har biyu fa." Kamal ya murzawa kofar key ya tsinke wayar yace" Ok kace su dawo karfe biyar yanzu inada wani babban aiki banida lkc gsky na tafi na dawo yanzu." ya faɗa yana ficewa yana takunsa mai cike da dattaku haɗe da izza, se ƴar ɗingisawar da ta zame masa kamar ado. Yana fitowa ma'aikatan companyn suka fra kwasar gaisuwa yana ɗaga masu hannun ya buɗe zafgegiyar motar sa fara kal kirar venza 2020 ya shige yay mata key ya fizgeta ya fice a guje. Anutse yake driving wayar sa ta sake ɗaukan ruri ya cirota a aljihu, yaga Amrah ce, picking yay ya kara a kunne yana sakin murmushi yace"Uhm my sweetheart ykk ina driving ne zan shiga makaranta ki bani 30 munites na nutsu zan kira ki pls kina min mgn da waccen muryar shagwaɓar taki pls my angel amaryar Kamal." ya faɗa yana bata kiss me zafi yace "bye se na kiraki wasu takardu zan ɗauko a Office." Amrah ta narkar da murya cikin sanyinta tace" Angona kaga kullum cikin gyara ake min yau fa saura 10 days amman kamar yaune bikin ok Angona kar na cikaka da surutu a sauka lfy i love u se na jiki bye." ta faɗa tana shirin tsinke kiran yace"Sweetheart kiss me mana ke wlh kamar me jinnu wata rana ki narke min ki sani wani yanayi kina abubuwa masu dadi ko ban saki ba , watarana kuma kawai kina kauyanci kuma na faɗa maki ina son rayuwa ina son love fa" ya faɗa mata a shwgwaɓe. Amrah tace" My Hubbina wlh ba fa ni..." Ko me ta tuna se tace ba naki maka bane watara kunya nake ji fa." ta faɗa tana sakar masa kiss ɗin ta tsinke kiran tana dariya. Kamal ya girgiza kai yace" Sweetheart zan cire miki kunyar nan wlh muyi rayuwar mu." ya faɗa yana maida hakalinsa kan driving.
Chapter 30 · 0% Book details