← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 124

Sashe 4

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai lokacin Kamal da Basma suka shigo a guje jin ihun niga.
Kamal yace"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ke kika ce za'a mata fyade ko zatayi fyade dai ko?" ya faɗi yana isa da gudu yana cewa"Ke sake shi karki kashesa mana, wannan wace irin macace haka." ya idasa gurin ya sanyan hannunsa duka biyu ya janyeta amma taki sai lokacin niga ya fara fita haiyacinsa daket Kamal ya ɓanɓareta niga kafin Kamal yake tarosa har yakai ƙasa sumamme, ya saketa ya nufi gun niga, Mubina jin an saketa tasa a ranta gun niga zaije a zuciyarta tace wlh yau naji kunya nice wandona a ƙasa sai riga iya guiwa ga wani kato yazo temakon kwarto to bari na jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, bazan bari ka temaka masa ba gwara ya mutu kwarton banza wai ashe abun maza haka yake da tauri da taushi gasu kaya guda, ni baƙin cikina bansan wannan mutumin wane ƙazami bane har ya taɓamin jiki amma bazan buɗe idona ba bare na juyo na kallesa har baƙin cikin ya kasheni, amma kamshinsa akwai ɗan dadi ba laifi, haka zan gama iskancin sumar karya.... Daidai lokacin Basma ta iso ta sunkuya ta ja mata wandonta ta saki uɓan ihuuuuu, wanda yasa Kamal dawowa baya, tayi luuuuu idanunta suna lumshewa zata faɗi rubda ciki saman wani katon dutsi, Kamal yace "Subahanalllahi" yay saurin tarota ta fado kirjinsa ya rungumeta gam yana ƙoƙarin leƙen fuskarta yaga wata yarinya ce wannan ɗiyar waye, anya ma tana hankali, sai yaga tana masa kama da maras kunyar yarinyar nan banbancin su ita bata saka manyan kaya haka. Mubina kuwa lafewa tayi kirjinsa tana shaƙuwa, Basma tana ganin Kamal na kokarin ɗago da Mubina yaga fuskarta idan ya gano Mubina ce bazai temaka mata ba da sauri ta nufo gun Kamal tace"Sir a...............✍🏻
*Real ladingo sweet Baby ce💋*

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*[08/07, 2:23 PM] +234 803 238 4602: *💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Page 3️⃣*

.....Ceci rayukan su da gaggawa idan Baby ta suma dadewa take bata farka ba , kaga yanzu da sauran numfashinta , bari na riƙeta ka samo ruwa a zuba masu ita da wannan mugun, kar ya wuce." ta faɗa tana kama Mubina, wacce take shaƙuwar iya shege ta wani mannewa jikin Kamal.
Da sauri Kamal ɗin ya ɓanɓareta jikinsa, yana faɗin "Ok riƙetan naje mota na ɗauko robar ruwa."Basma tace"Ok Sir mun gode" ta faɗi tana ƙoƙarin zama a ƙasa, ta zauna dirshin ta kifa kan Mubina a cinyarta ta boye kanta, itako sai shaƙuwa take.

Kamal da sauri yay waje Mubina tana jin fitarsa ta bushe da dariya, ta fizge kanta da sauri cikin daddar muryata tace"Bari na ƙarasa ɗan iskan nigan nan, gobe ya kara wama wata ƙoƙarin fyade." ta faɗi tana nufar gun niga da yake sheme a ƙasa.
Basma cikin tsoro!! Da tashin hankali ta miƙe tana cewa"Mubina dan Allah ki rufa mana asiri kar kiyi kisan kai , baicin haka ma Sir Kamal zai temake mu kalli duhu ya kawo idan ya gane ki fasawa zai yi dan Allah ki ɓoye kanki na tuba badan halina ba..."Mubina ta juyo ranta a mugun ɓace ta kafe Basma da shanyayyun idanunta, tace"Kina nufin *Kangiwa gurgu ne* na runguma jikinmu ya hadu waje ɗaya shine ya ganni da riga iya guiwa? Kan uban can , to wlh tallahi bazan ɓoye kaina ba asali ma sai na zub masa tijara yanzu nan..."Basma ce ta rufe mata bakinta tana girgiza kai, tace"dan Allah kimin wannan alfarmar ko da zata zama ta karshe a duniya kiyi hakuri kar Sir ya gano ki , bana son ya miki wata fassara daban ki temake ni dan girman Allah kibari idan yaso ko da gabaya ne ni zan rakaki har Office ɗinsa kima tijarar , amma yanzu domin Allah ki hakura muje gida cikin salama karki nunama sir kece pls kawata tun yarinta kimin wannan alfarmr." ta idar da maganar tana kece mata da kuka.

Mubina jikinta ya danyi sanyi kaɗan amma haushin Kamal ne fal a zuciyarta, kuma ta ɗauki alkawalin gobe sai taji dalilinsa na rungumarta da yayi, cikin haushin Basmar tace "naji zan miki wannan alfarmar amma gobe wlh sai naje har Office ɗinsa naji dalilin sa na rungumata , ni bana son shishigi gurgun mage kawai kuma wlh yanzu ya kuskura ya taɓani sai na wanwanka masa mari babu ruwana da wani sir😏..."Tafiyar da sukaji ne yasa Basma saurin rufema Mubina baki, ta boye kanta a jikinta tana bubbuga bayan Mubina tana mata sannu, amma Mubina taki yin shaƙuwar.

Kamal kuwa da sauri ya isa gunsu ya buÉ—e robar ruwan, ya sunkuyo yana shirin kama Mubina, Basma tayi saurin amasar robar ruwan bakinta na rawa tace"Sir... Zan...bata...kaje...ka..
zu...ba...ma...wancan."ta karasa maganar tana ƙoƙarin kara ɓoye Mubina, duk da duhu ya fara sosai.
Kamal ya nufi gun niga ya budo robar ruwan me sanyi ya fara kwarara masa a fuskarsa zuwa maza kuntarsa da tasha a zaba.
Firgigit ya farka yana sauke ajiayar zuciya, jikinsa na rawa yace"Wlh taso kasheni wannan yarinyar anyi tsinaniya Marar mutunci maras tarbiyya..." Aikuwa Mubina ta zabura zatayi magana Basma ta damƙeta da karfin gaske ta rufe mata baki.
Kamal ganin niga ya tashi yasa bai sake wata magana ba, ya ciro katinsa aljihunsa ya ba niga yace"Idan ka sami sauƙi ka neme ni ina son ganinka , Allah yasa wannan yazama darasi a wajanka." yana kai karshen maganar bai sake ko kallonsa ba ya juyo yace da Basma"Oya muje na ajiye ku gida." yana faɗi mata haƙa yasa kai ya fice.
Ai niga yana ga Kamal ya fita ya miƙe cikin zafin nama ko takalmi bai jira ɗauka ba ya nufi hanyar waje dan ya shiga tsoron yarinyar.
Basma ta cire mayafin jikinta ta rufama Mubina ta kama hannunta sai bubbuÉ—e hanci take tana Jan tsaki, Basma bata kulata ba tasan tunda tace zata mata alfarmar zata mata.
Lokacin da suka iso bakin motar Kamal na ciki ransa duk a ɓace ya rasa sallah magarib yayi abun nan ne saboda Basma kawai.
Mubina tace"Yanzu motar gurgu zamu shiga karfa ya kifar damu wlh..." Basma tace"ki tuna kinmin alkawali kuma cika shi shine mutum dan haka shiru shiga mota muje."ta faÉ—i tana isa gun gyalan Mubina ta É—auka ta dawo tA buÉ—e motar... Kamal yace"Ke dawo gaba ni ba direban kowa bane."ya faÉ—i yana kunna motar.
Da sauri Basma ta tura Mubina bayan motar ta rufo kofar gabanta na ɗar-ɗar kar tayi abin kunya, ta buɗe gaban ta shiga ta rufo ya fizgi motar a dari da ƙaniya ya bar lungun..
Niga da yake cikin Adaidaita Sahunsa yana kallonsu ya fito yana cewa"Wlh yarinyar nan ba Æ´ar albarka bace , kaga shegiyar yarinya taso ta aikani lahira ban ajiye ko É—an da zaimun Addu'a ba , insha Allahu yadda kika bani wahala kema sai kin shata a rayuwarki kuma da izinin Allah sai an miki fyaden da bakiso insha Allahu shegiya mace yawa sanda ba nama." haka yayi ta surutu shi kadai yaja Adaidaitar ya nufi cikin É—an gidan ya rufo kofa ya kira wata number a kawo masa abunci É—a maganin ciwon jiki, dan bazai iya fita ba yaji jiki sosai, se dai ya É—auki alwashin bazai kuma kwatanta ma mace fyade ba..

Mubina da take bayan mota haushi da baƙin ciki sun isheta, ga gudun da Kamal yake zubawa. Cikin rashin kunya tace"Kai kankura kayi drving a sannu , mutanene ka ɗauko ba dabbobi ba dama mutum gashi ga kamarsa haka kawai a naka sani kenan ayi biyu babu ba madu ba sau , yo idan ba kini ɓibiba irin na gura... Ai Basma bata bari ta idasa ba, sai gata ta wuntsulo bayan motar ta rufe mata baki tana cewa"Sir kayi hakuri dan Allah."Kamal yayi matuƙar mamaki abinda yarinyar take masa me haɗinsa da ita daga temko shine ya zama aibu har take aibata shi shine harda kiransa gurgu, tabbas in dai duka mata halinsu kenan zai jima baiyi aure ba kuwa, yau kadai mace biyu tace masa gurgu gobe baisan mata nawa zasu ce masa ba...
Katseta yay ta hanyar cewa"Ke karki damu duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau ya gyara." bai sake magana ba yaci gaba da drving É—insa.
Mubina kuwa Basma na riƙe da bakinta tana kwatanta ma Kamal gidan da zai ajiye su cike da mamaki yake nufar dab da gidansu, har ya iso yay parking gidan nan me kallon nasu Kamla.
Yana parking ko gama tsayawa baiba Mubina ta ɓalle murfin mota ta fice bata ce kome ba dan so take gobe ta iskeshi har Office ɗinsa ta masa tijara, kai tasa ta nufi get ɗin gidan su da gudu.
Basma tace" Sir kayi hakuri dan Allah." Kai ya É—aga yace"Oya jeki" da sauri Basma ta É—auki jakokin su ta fito daga motar ta rufe masa ta nufi cikin gidan su Mubina É—in.
Kamal yaja motar sa ya nufi get ɗinsu yana horn tin karfi, megadi ya buɗe masa kofa ya shige a guje, direct tamƙamemiyar rumfar ajiye motoci ya nufa yay parking, garba ya iso ya buɗe masa yana washe baki yace"Ah *Kangiwa* namiji duniya sannu da isowa." Kamal ya fito yana kallon sa yace"Uhm garba barka da gida bari nayi sallah." ya faɗa yana nufar cikin gida da dan sauri har ɗingisawar sa ta fito kaɗan.
Yana shiga bai nemi kowa ba yay alwalla ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiya ya nufi massalaci..
Chapter 4 · 0% Book details