Sashe 18
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Mubina cikin nutsuwa take tafiyarta, tana waige-waige tsoro ya ɗan shigeta kaɗan, saboda yanda layin yake shiru ba jama'a sbd garin yakar ɗe da hadari, yayi duhu sosai baka ganin abu da kyau, ga iska ga ɗan yaiyafi anayi gashi zowa bakin titi da ɗan ja. Cikin ikon Allah ta shanyo kwana se ga me adaidaita sahu zai nufi bakin titi, cikin murna Mubina ta fara ɗaga masa hannunta sbd an fara ruwa. Cikin sa'a kuwa ya hangota tinda nan gabanta yake tinka rowa, kuma fitilar adaidaitar a kunne ya haske ta, yana ƙoƙarin ƙarasowa. Mubina ta ja mayafinta ta rufe fuskarta tana jan tsaki tai maga iya saman lips ɗinta, tace"Kaji iskanci aikin banza kawai wlh badan a tsorace nake ba ga gari yayi duhu da sai na koya maka hankali , haka kawai ka haske min fuska..." daidai me adaidaitar ya iso yana washe baki yace"Hajiya se ina amma zaki bada jaka biyu sbd kin san halin da ake ba kowa zai ɗauki mutum yanzu ba , nima na kawo matar da zan aura ce can ƙasa sai na hayo tudun manya.." Mubina cikin jin haushin sa ta buɗe mayafin fuskarta ta kalleshi, idanu Harun niga ya zaro!! yace"Kan uba kece wlh ko me zaki bani bazan ɗauke kiba muguwar yarinya baƙar kadara , anya ke mutum ce kuwa?" ya fada yana ƙokarin tashin a daidaitar shi ya fece.
Ai kuwa jin abinda harun niga ya faɗa ya kuma tsorata!! ga Mubina ma atsora ce! take, amma se taga ta sami dama ko ba kome zata amshe adeɗetar, ta tuƙa da kanta bayan nan zata masa sufar ita ba mutum bace ba ta cinma burinta na tuƙa adedeta, taje har kofar gidan Baffa a bati ba ko sisi. Da sauri ta sanya hannunta saman fatar idanunta, ta juye fatar idanun suka bultso waje, ma'ana fatar idanunta ta sama ta juyo ta ciki ta dawo waje irin dai na yarinta da ake, nasan wasun makaranta ɗayawa zasu gane nufi na... Ta cire mayafin kanta ta daure ƙugunta, ta nasa phone ɗinta cikin bra ɗinta, ta saki gashinta yayi buzu-buzu, Mubina ta zaro idanu ta gwalo harshe waje, ta koma sufa abin tsoro! ta damƙe kwalar niga tana wata irin dariya tace"Hhhhhhh Niga ne ko yaron da ya yaso yama jikanyar tattaɓa kunne na fyade ko? Hhhhhh yau irin ku muke nema zamu yanka ku muba ɗangwandarau jininku ana bikin cika shekarun sa dubu biyu." ta faɗa tana gwagwalo harshe tana zazaro masa idanu, ga idanunta sun tara kwalla dan zafi take ji yanda ta burkita su ɗin. Harun niga cikin matsane cin tashin hanali yace"ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba , wlh bani bane nama jikanyar tattaɓa kunnen ki fyade ki taimaka ya mai girma aljana na tuba..." ɗauke shi Mubina tayi da mari, cikin wata irin murya tace"ka yarda yanzu na kaika gidan da abin ya faru harda kawarta ɗiyar dogarin sarkin aljanun Ethoipia , har jikanta yaje ya ceceta , bari muje kaga gidan daga can se mu kaika gurin sarkin yanka ya maka sallatu a maka askin mutuwa , dan bama kashewa se an ma mutum kaciya da askin mutuwa , maza koma baya bani gaban na tuka muje gidan da kaso kama jikanyar tattaɓa kunnena fyaɗe , maza shiga baya zauna wlh idan kayi ƙoƙarin guduwa zamu lauye ka mu maido ma mafitsaraka goshinka ." ta faɗa tana sakin sa tana gwagwalo masa idanu da harshe.
Niga wanda ya gama rikita cikin rawar jiki ya miƙe ya dira bayan adedeta jikinsa na kyarrrrrma.
Mubina ta gyara idanunta tana kumshe dariyarta, ta kunna adedeta sahun ta fizgeta da karfin gaske ta tafi a guje, ta nufi bakin titi. kuma a lokacin aka saki ruwan sama me karfin gaske irin me iskar nan sosai. Harun banda rawar jiki da zufa da take keto masa babu abinda yake har ya fara ɗigar fitsari, saboda yadda Mubina take tukin bada wasaba tana magana ita ɗaya tana cewa"Sarkin wanzanman aljanun arewa maso kudu ka gyara askarka mun kamo kwarton jikanyar tattaba kunne na , za'a masa sallatu da aski kafin mun kashe shi." ta faɗa tana ƙoƙarin shan kwana ta hau saman titi, dan bata ganin gabanta sosai saboda ruwan da ake zabgawa ga duhu tamkar dare... A daidai lokacin kuma Kamal ya danno hancin motar sa kwanar, idanu ya zaro ganin mace na tuƙa adedeta, ƙoƙarin kaucewa yake daket ya samu ya ɗan kauce ya basu guri su wuce. ganin harda namiji... Ai kuwa Mubina itama sai ƙoƙarin jan burki take adedeta taki tsayawa, ta fasa ihuuuu tana ƙoƙarin direwa ƙasa. Niga yace"don Allah karki kasheni tinda ke ko kinyi hatsarin ba mutuwa zakiyi ba." ya faɗa yana wutsulowa waje. Mubina kuwa tayi muguwar tsorata! ta gigice ta rasa abin yi, saboda faɗuwar gaban da tayi ganin adedetar taki tsawa kuma niga ya dire ya fadi ƙasa, se kiran umpah da Mamu da Amrah da yaya Kabeer da Baffa inusa take, tana ƙoƙarin tsayar da adedetar tama rasa ta ya zata dire irin yanda niga yay... Kamal yayi saurin yin baya da motar yana zaro idanu ganin Mubina ce, ya furta"Ya Salam Allah me iko mai halitta kala-kala anya kuwa yarinyar n..." bai idasa maganar ba ta bugi motar sa da adedeta sahun, ta fasa ihuuuu! tayi baya ta faɗi bata ko motsi... Niga ya dora hannuwa akai yace"Allah ka fitar dani wlh zaiyi wuya nakai gobe , ganin hatsarin mutanan ɓoye ba abu bane me kyau." ya faɗa jikinsa na kyarma. Kamal ya ɗauki bazara ya budeta ya fito ya shiga duba gaban motarsa inda ta buga har ta ɗan lankwasa kaɗan, yaja tsaki ya nufo gunsu. Niga ya ƙarema Kamal kallo yace" wa'innahu sulemanu wa'innahu bissmillahir rahamanir rahim, don Allah ku rabu dani , jikanta karka cutar dani wlh ban ma kakarka kome ba." ya faɗa yana zube ƙasa sumamme fitsari na tsiyaya, amma bazaka ganeba saboda ruwan sama da ake ya jiƙashi jagab.