← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 124

Sashe 76

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can Makel yace "good morning sir, fatan ka tashi lfy?" Kamal ya saki murmushi ya shafi kansa, yace "Sorry Makel sai yanzu na tashi a bacci, yunwa nakeji ka kawomim breakfast mara nauyi." Makel yace " Ok sir an gama ka buɗe kofar ina ta yanzu, nati kira da buga kofar shiru." Ok Kamal yace ya katse kiran yana murmushi ya nufi window yana leƙen ƙasa, matan torawa ya gani maza da mata suna zafgogin gabansu. Wata ƴar baturiya suna zaune bakin suwwing pool, suna manne da juna ita da surayinta sai kissing ɗin juna suke.
Kamal ya kawar da kansa ya lumshe tsumamun idanunsa, ya girgiza kai yace" Uhm turawa kenan kowa rayuwarsa yake yadda yake so, ba ruwan wani da wani, hum kaga masoya." ya faÉ—i yana sakin murmushi, ya buÉ—e idanunsa, cikin nutsuwa ya nufi kofar parlon. Yana zuwa ya murza key ya buÉ—e kofar ya dawo ya zauna nan parlo.
Yana zama da kamar 5 munite sai ga Makel ya turo kofar ya shigo da kayan breakfast. Kamal ya waro idanu yace"Duk ni dawa wannan?" Makel yay dariya ya janyo yable gaban Kamal ya ajiye masa katon tire shaƙe da abubuwa iri iri. Makel yace"Sir duk kai ɗaya." Kamal yay murmushi haɗin tea mai daɗi ya fara sha, yaci cake kaɗan su kadai ya iya sakama cikin sa. Kamal yace.
Oya bani labarin Mubina ina muka tsaya?" Kamal ya tambayi Makel ya tsaresa da manyan idanunsa. Makel yace"Sir ai babu wani abu a yanzu komai ya kammala fa, zamu iya tafiya kaga makarantar da take ma, matsala ɗayace, possport ɗinta shi zai ɓata mana lkc." Kamal ya nisa yace.
"No karka damu wannan ba matsala bace, nasan halin yarinyar tana yawo da duk wani abu mai mahimmanci a tare da ita, so nakega zata iya yuwa yana cikin jakarta ta makaranta, amman fa ba wai lallai bane insha Allahu Addu'o'in da nake bazasu tashi a banza ba! Insha Allah zamu sameta tare da possport É—inta , so ka ga ranar da muka tashi É—aukarta zamu yi nasara samunsa a jakarta." ya faÉ—i yana sakin tattausan murmushi yana shafa kyakyawan sajan fuskarshi.
Makel yace"Ok sir Allah yasa gakani É—in, idan babu kuwa zaman london ya kamaka." Kamal yace "Ameen bazan zauna ba fa zamu sna yanda zamuyi." Makel yace"Sir mu É—an zaga kaga gari, daga can muje kaganta." Kamal yace.
"Ok."
Fitowa sukayi suka sauko ƙasa, a nutsu suka tafiya Kamal yana takunsa na isassun maza masu ji da kome kyau kuɗi cikar hallata irin ta jaruman maza. Ga uwa uba ɗingishin da ya zame masa kamar taƙama ko yanga, bazaka taɓa cewa gurguntaka bace. Tunda su Kamal suka fito wasu ƴan matan turawa suke kallonsa suna yabawa da kyansa, da kyan halittarsa, da takunsa na isassun maza. Kamal kuwa duk abinda suke faɗi karaf a kan kunnesa, face ya haɗe ko kallon inda suke bai ba suka nufi mota, Kamal na gefen Makel a zaune Makel ya ma motar key yaja ya nufi gate, yana isa bakin geta aka buɗe masu gate Makel ya fice a guje.
Sosai Kamal garin na london yayi masa kyau, duk da wannan ne zuwansa na biyar, amman wannan karon yafi ganin kyan london, Makel sai hira yake masa Kamal shiko na sakin murmushi, dan yana cikin shaukin zashi ganin Mubina.....
Nesa da makarantar Makel yay parking, suna kallon gate ɗin makarantar. Kamal yace"Wow makarantar su Mubee masha Allah."Makel yace" Sir saima ka shiga ciki." Murmushi Kamal yayi mai ƙayatarwa ya lumshe narkakun idanunsa. basu wuce 10 minutes ba.!
Cikin ikon Allah sai gasu Mubina sun nufo gate, sanye take da riga da siket na less maroon coulor mai shigen kyau, ya karɓi jikinta sosai, hips ɗinta ya fito, kirjinta mai cike da dukiyar fulani tamtsam tamtsam, se girgiza suke tayi kyau iya kyau, anutse take takunta na cikakiyar budurwa mai ji da kome, wani takalmine mai masifar tsayi a ƙafarta, ko ina jinkita na motsawa, kanta babu mayafi sai dankwalin less ɗin da ta masa ɗaurin ture kaga tsiya.
Kamal a hankali ya ƙura mata tsumammun idanunsa, ko kiftawa bayayi yanajin wani irin shauki, na ɗibarsa, wani abu na shiga cikin jikinsa, na ratsa duk wata gaɓa ta jikinsa. A hankali ya furta"Wow Baby Mubee." ya faɗi yana lumshe tsumammun idanunsa, ya sauke ajiyar zuciya ya fesar da iska mai zafi waje. Ransa yayi mugun ɓaci, yanda take yawo cikin turawa. Sai hirasu suke a nutse Mubina na sakin murmushi, tana danna phone ɗinta. Suna hira da kausar. Kamal ya juyo ya kalli Makel yace.
" Makel kana nufin kullum haka take yawo cikin turawa kome nata a waje suna kallonta? Dole zanyi gaggawar ɗauketa, wlh bata isaba." ya faɗi a zafafe. Saida Makel ya ɗan tsorata. Mubina yaga ta ɗaga waya tana magana a sakalce, tana diddira ƙafafunta, tana zumburo baki gaba, ta ciro wayar daga saman kunnenta tana murmushi suna mgn da kausar. Kamar 3 minute sai ga mota tazo ta faka, gabansu Mubina tayi dariya ta kama hannun Kausar tana gaya mata wata mgn ta saketa ta buɗe motar gidan gaba ta shiga ta zauna Kausar na ɗaga mata hannun, Majeed yaja motar suka tafi. Ba jimawa aka zo ɗaukar Kausar.

Kamal ya ciza lips ɗinsa na ƙasa yace"Mubina anata gantali da nuna surah cikin yahudawa." Makel dai murmushi yaja motar suka bar gurin....

*Niger* Ɓangaran iyamu kuwa tinda Ibrahim ya mata zancan aure, take cike da walwala da farin ciki, burinta kawai tama su Alhaji Tukur wayo su dawo, tin a ranar ta kirasu bata samunsu.
Kwance take saman katifa ta gaji yanzu suka dawo daga makaranta, se danna waya take, Leezah tace"Sister kinada damuwa ne?" Iyamu tace"No me kika gani kawai murna ce ta isheni , na kusa zama matar aure, Ibrahim ya kusa zuwa kaduna yaga iyayena..."ta faɗi tana kiran number Tukur, cikin sa'a kuwa ta shiga, tana fara ringing ya ɗauka, Iyamu ta kwantar da murya tace"masoyi ina ka shiga imiss u wlh ina buƙatarka fa. Kome yace mata tace"Gsky yayi yawa kazo gobe kawai idan ka dade jibi." haka suka ajiye akan jibi zasu dawo iyamu murna, Leezah ma tana murna dan batada kuɗi, nan iyamu fice ta laɓe tai kiran ibrahim tana faɗa masa yanda sukayi, yaji daɗi yace tayi ƙoƙari jibin ta kuma ɗauko kome da kyau yan agani washegari zasuje kaduna ayi maganar auransu zai kawo mata camera....

Ummah na zaune tinda ta gama sallah, isha tana lazimi Samha ta shigo bedroom É—in tana kiran "Ummahta kina ina?" ta faÉ—i tana zama, kusan Ummah ta rungumeta ta baya, tana dariya.
Ummah tayi Addu'a ta shafa ta juyo tana cewa" Samha lafiyar kuwa ni sakeni kinzo kin maƙaleni kina dariya kamar zarariya." Cikin jin kunya tace.

"To Ummah ba yaya Anwar bane ya kirani wai meye da meye."

Ta faɗi tana dariya ta ɓoye kanta jikin Ummah ɗin. Ummah ta riƙe baki tace"Meye yace to?" Samha ta saki Ummah ta miƙe ta bar ɗakin da gudu, tana dariya. Ummah ta miƙe ta cire ƙaton hijabin ta ajiye ta fito ta sauko parlo. Bataga Samha ba, sai Abbu zaune yana waya, kusansa ta zauna taji akan business ɗinsa ne yake mgn. Sageer ne yayi sallama kofar parlo. Ummah tace"Sageer ƙaraso mana." Sageer ya shigo yana sake sallama. Ummah ta amsa tana kiran Samha. Kusan Abbu ya tsugunna cike da ladabi yace"Abbu Ummah ina yini." Ummah tace.
" lafiya lau Sageer ya wajansu Nini fatan suna lafiya?" Sageer yace lafiya lau Ummah." ya faÉ—i yana ajiye ledar hannunsa. Abbu yay sallama da wanda suke waya, yace"ah Sageer ango kai tafe a daran nan?" Sageer yay murmushi ya sake gaida Abbu. abbu yace"Ya Abokin naka yau bamu gaisa ya tafi Germany." Sageer yace"Eh Abbu nima bamu gaisaba, maybe sai ya sayi layin can" ya faÉ—i yana jinjina lamarin Kamal da ya canza masa akan mace.
Samha ce ta sauko tana cewa.
"Oyoyo brother nah."
Sageer yay murmushi yace"Ƙanwata ya karatu?" Samha ta zauna tana dariya tace "Muna sha yayana." Ummah tace"Tashi maza kawo masa ruwa ko lemo..."Sageer ya miƙe yace"Ummah ta barshi zan wuce ma Abbu sai anjimanku."ya faɗi yana miƙewa. Abbu yace"sannu yaron kirki Allah ya maka albarka." Ummah tace"harda wahala haka sannu Sageer, Samha rakashi mana."
Samha ta miƙe tana bin bayan Sageer tana cewa" yayana ina Mubina amaryarmu?" Su Abbu da kejinta dariya sukayi. Ummah tace"jiyama kuwa ta kirani munyi hira."Abbu yace.
"Nima na kirata baiwar Allah."Ummah ta jinjina kai tana buÉ—e ledar da Sageer ya kawo masu. Samha har bakin gate jikin mota takai Sageer, yana bata amsar Mubee na lfy... Haka sukayi sallama ya nufi gate É—in gidansu Mubina.

Zaune suke a parlo Mamu na damama Umpah furah, Ablah nacin tufa tana kallon tashar RTT Tv ana nuno labaran hausa. Amrah kusan Umpah a zaune. Kabeer yace"Umpah mun gama magana fa da Basma tace ko yaushe aje dadynta ya sani..." Umpah zaiyi magana Ablah tace.
Alhmdllh haka daman nake son ji a haÉ—a auran jikokina uku rana É—aya ayi shagali ayi bidiri bireÉ—e."ta faÉ—i tana cin tufa É—in. Mamu kuwa kallon Ablah take tace, "ummu wai yau kun gaisa da tawajanki kuwa?" Ablah tace"Eh sosai ma kuwa." Umpah yace"Ok babu matsala zamuyi mgn da kawunku yanzu ya kwanta ciwon kai yake har zuwa gobe." cikin farin ciki Kabeer yace" Allah ya kaimu."
Ablah da Mamu sukace "Ameen" Amrah zatayi magana tana dariya Sageer yay sallama kofar parlo. Suka amsa, Kabeer ya miƙe ya masa iso. Sageer ya shigo da katuwar leda a hannunsa, suka ƙaraso cikin farlon. Sageer ya gaishe dasu Umpah cikin girmamawa. Ablah tace.
"Sageeru yaron albarka." Sageer yay murmushi, Umpah yace"ya gida da tsaffi?" Sageer yace"kowa lafiya Umpah." Amrah ta gaishesa tana miƙewa saboda ƙiranta da akayi, tana amsa waya. Ablah tace"Yo haka zar." Umpah yayi murmushi. Sageer ya ɗan jima ya masu sallama suka fito da Kabeer ya rakashi har mota, ya shiga ya tafi shiko ya nufi gidansu Basma, zai kai mata sako. Umpah yaga irin siyayyar da Sageer ya masu yana sa masa albarka, dan yasan yayi
sa'ar suruki bazai taɓa yarda ya kubce masa ba! Shiyasa ya basa auran Mubina ....

*London*
Chapter 76 · 0% Book details