← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 124

Sashe 94

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kawu Jafar kusa da Umaimah zaune yana riƙe da hannunta Yumnah taje gida tazo. Anwar yace"Dady to shi Kamal ɗin yace bazai aureta bane?" Jafar ya buɗe baki zaiyi magana Umaimah ta farka tana ɗan fizge² tana ƙiran"Yaya Kamal ina sonka ɗan Allah ka saketa ka aureni zan mutu wallahi zan kashe kaina akanka." ta faɗi da ƙarfi tana kecewa da kuka.
Kawu ya riƙeta shida Anwar suna ƙiran sunanta. Idanu ta buɗe ganin dadynta ta ƙara sautin kuka tana ƙiran Kamal. Dakyar Suka samu suka shayo kanta cikin wayo da cewa ai Kamal yaji batada lafiya ya tashi hankalinsa yace a bata haƙuri yana tafe duk abinda takeso ya mata. To hakan yasa Umaimah farin ciki tayi shiru, Anwar ya ƙira nurse ta dubata aka cire mata drip Anwar ya temaka mata ta sauko ya akita har kofar toilet tayi fitsari ta wanke bakinta ta dawo, amman ba yanda basuyi ba taci abunci taƙi, saida Kawu yay ƙiran ƙarya kamar yana waya da Kamal akan taƙi cin abinci, to shine suka samu taci sosai aka bata magani tasha sai bacci. Bayan 2 hours aka sallamesu, tare da ƙwakwaran kasheɗi subita asannu zuciyarta ta kamu da ciwo sama sama amman idan ba'a mata abinda take so ba ko fasa ɓata mata rai zata iya shiga matakin da ba aso ta shiga. Kawu Jafar ya shiga tashin hankali shida Yumna da Anwar, gashi da zaran ya faɗama Abbu zai saka Kamal dole ya aureta, amman yasa aransa zai roƙi Kamal da kansa ya auri ƙanwarsa kar ta rasa ranta....
Ɓangaran Kamal kuwa yana tsinke ƙiran, ya kalli Makel bayan ya gama parking ɗin, ya shafi sumar kansa yace.
"Oya muje ciki na taho da matata." Makel yayi murmushi, ya fito Kamal ma ya fito ya rufe gefan da ya fito, suka nufi cikin gidan.
Mubina kuwa bayan kuɗin sun gama, ƙiran ya katse ta tsame hannunta daga indomie ɗin tana matsar ƙwalla. Kausar tace"Ah sahiba keda waye?" Mubina tace.
"Yo ba Kamal bane yace ma su Umpah wai zamuje saudiya ni bana zuwa karatuna fa, kuma ni banafa sonshi, kawai ƙwawarsa ce fa."ta faɗi a sangarce. Kausar tayi dariya ta miƙe tana suɗe hannunta taje ta wanko hannunta tace"Tom ni kam bansan me zance ba tinda mijinki ne, dare fa yayi sosai shaɗaya ta wuce, muje yaya Majeed ya kaini gida."Mubina taje ta wanko hannunta ta ɗauki hijabi ta ɗora saman haɗadɗiyar rigata tace"Muje to ko mukwana anan mana tinda gobe ba school?" Kausar tace"A'a gobe ki tambayi mijinki kizo mu wuni." Mubina takai mata duka suka fito parlo.
Papa nama Ummi maganar tafiyarsu Mubinan saudiya yanda Umpah ya faɗa masa kome. Ummi tace"Ai na faɗa daman bazai barta ba tayi karatunan..."Mubina ta ƙaraso jikin ummi tace.
"Ummi wace?" ummi tace"Wata" Kausar tayi masu sallama. Mubina tace"Ummi ina yaya Majeed ya kaita gida?" Ummi tace"Ai kuwa ya fita Kausar bazaki kwana anan ba?"Kausar tace"Ummi Aunty tace kar na kwana shiyasa, ai zan sami texi bari na wuce kar dare ya kuma." Papa yace.
" Bari a ƙira Majeed mana yazo ya kaiki." Kausar tace"Papa zan hau texi ai ba nisa sosai." ta faɗi tana kama hannun Mubina. Mubina tace"Ummi ki fitomin da wayata zan ƙira Mamu, idan na rakata nazo yanzu." ta faɗi suna nufar kofar parlo. Ummi tayi dariya, dan Mubina dariya ma take bata... Handle ɗin kofar Mubina ta kama tana buɗewa sai zuba zuba takema Kausar, sam bata luraba taji ta fado saman jikin mutum. Daddaɗan ƙamshin turaransa ya kai mata farmaki cikin hancinta. Da sauri ta ɗago suka haɗa idanu da Kamal. Daga bayanta taji muryar Kausar tana cewa"Tsarki ya tabbata da ubangijin wannan maƙerin bawan kyakywa wow Sahiba...! Ki ɗagashi mana karone kukayi. Kamal ya ɗan matsa gefen kofar da Mubina a jikinsa, ya rungume tsam ƙirjinsa, cikin cool voice ɗinsa yace"Wow ƴan mata kema kuwa kin haɗu sosai anan gidan kike please?" Mubina ta ɗago da kanta tana ƙoƙarin fizge jikinta, har kyarma yake A zafafe tace "Kausar! Mijina ne fa kike yabo haka? Kan bala'i." ta faɗi tana watsama Kamal mugun kallo cikin masifa ta bugi ƙirjinsa da karfi, tace"Kai! Kuma da kake..." Kausar ta katse Mubina, ta matso tana dariya tace"Mubina da wasa kike ko da gaske wannan haɗaddaɗan gayan ne mijinki? kuma bakya sonsa, kamar yanda kika faɗamin yanzu a ciki...?" Mubina ta ɗago suka haɗa idanu da Kamal, ya mata wani irin shegen kallon da ya birkitamata lisafi, ya lumshe mata tsumammun idanunsa, yace"Yes Sweetie bata amsa, kinga sai ta shigo da karfinta. Mubina manya idanunta ta waro waje, tace"Kan bala'i ina zata shigo....?" Ta faɗi a masifance tana sakin Kamal ɗin...!

*Timnit Welday😉*

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣
Chapter 94 · 0% Book details