← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 124

Sashe 44

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa hospital suka firfito Umpah na riƙe da hannun Amrah suna gaba sauran na biye dasu suka shige ciki. A kofar room ɗin Umpah yaga Kamal ya haɗa kai da guiwa. Umpah ya tsaya yace"Kamalu oya tashi mana dan me zaka zauna anan ba aciki ba?" Amrah taja tsaki ta kauda kanta ta saki hannun Umpah tabi su Mamu dan ba wanda ya tsaya. Kamal ya ɗago yace"Umpah ina kwana dan Allah ku yafemin natuba..." Umpah ya sunkuya ya kamashi yace"Tashi muje ciki inada mgn dakai." ya faɗa yana riƙe da hannun Kamal suka shiga ciki. Su Mamu na zazzaune bayan sun gama gaisawa dasu Abbu. Umpah yana riƙe da hannun Kamal suka shigo da sallama. Abbu ya miƙe yana ba umpah hannu sukayi musabaha. Uammah ta gaushesa ya amsa, Sageer ya gaishesa cike da girmamawa, Umpah ya amsa, Kamal ya saki hannun Umpah ya duƙa yana gaishe da Mamu ta amsa fuska ba alamun rahma. Abbu yace "Kai fitar mana anan maza..."Umpah ya katseshi yace"A'A nine na kawoshi yanzu magana zamuyi ta fahimta kaima Sageer naji dadi kana nan nasan kanada amana bazaka fallasa mana sirri waje ba, har mutane suji." ya faɗa yana zama bakin gadan da Mubina take ya kama hannunta yana kallonta, ya juyo ya kalli Kamal yace zo zauna Kamalu" Kamal cike dajin kaunya ya karasa ya zauna ƙasa kusa da ƙafafaun Umpah. Ablah da Mamu ta haɗamata tea tana sha, ta ƙurama Umpah idanu tana jira taga ikon Allah. Umpah yayi gyaran murya yace"Don Allah don Annabi abinda nake so daku mu rufe maganar nan iya mu ɗinan karta fita waje rayuwar ƴata zata tagaiyara zata zama abin kyama a idanun maza da sauran mata ƴan uwanta, karatun ta zai sami tangarɗa, haka shima Kamalu a waje yarone mai jama'a da nagarta mutum ne wanda yasan ciwon kansa yasan me yake to bana son a masa kallon banza, tabbas wannan lamarin kaddararene gun Allah tin ranar gini ranar zane, Allah ya kaddara Kamal da Mubina bazasu tsallake wannan kaddara ba... So dan haka banga anfanin zuwa kotu ba, tonon asiri ana ɗaukarmu kafofin yaɗa labarai, mutunci na ya zube na ƴata ya zube na Abbu ya zube na Kamalu ya zube, dan haka ni na yafe maka Kamalu kuma Mubina ma zansa ta yafe maka da zaran raɗaɗin abun ya barta kuma Mamu na ari bakinta ta yafe maka, seda maganar nan iyakarmu Amana kar najita waje bana buƙata ko dangina bakin wa'innan kadai ne suka sani, haka Mamu ma na hanata faɗama kowa nata mu kashe mu binne wannan maganar ba mai sake ji se ranar da Allah yaba Mubina miji idan zan aurar da ita na faɗa masa bisa amana bayan yamin alkawali..." Umpah ya karasa maganar yana hawaye. Kowa jikinsa yayi sanyi kowa kwalla yake, Mamu ce ta fashe da kuka ita da Amrah, haka Kamal ma yana me tsanar kansa. Ya riƙe Umpah yace"Ngd umpah Ngd..." ya faɗa yana sakin umpah, ya ɗago yana kallin Mubina ya juya ya kalli Mamu se hararasa take, ya sadda kansa. Sageer ya kama ƙafafun Umpah yace"Umpah wlh ina son Mubina har yanzu zan jira ta gama karatunta idan zaka bani auranta wlh zan aureta bisa amana ni ita nake ba wani abu nata ba..." Umpah cike da farin ciki yace"Ngd Sageer Allah ya maka albarka wlh ka wanke min guntun bakin cikin da nake ciki, dan bana fushi da hukuncin Allah... Nagode." ya faɗa yana ɗagowa ya kalli Abbu yace"Abokina kaga yaro me halalci ko? Kamalu kaima karka saka damuwa a ranka ka bari kome ya lafa ka fito da mata wannan kanya abarsu nan hannu na daga gidana za'a kai su insha Allahu zumunci na nan..."Mamu tace Abdul wai lfy kake kuwa?" bai kulataba yace da Abbu "Abokna ka yafema Kamal don Allah" Abbu ya girgiza kai yana kwalla dan Umpah ya nuna masa halacci, bai taɓa zaton haka ba daga gare sa. Abbu ya matso ya rungume Sageer yace"Allah yama albarka mun gode sosai da halaccin ka" ya kalli Umpah yace"Abbu ɗaya zai sa na huce naga Kamal baya kusa dani yabar garin kawai, abun na biyu naga Mubina ta dawo normal tana rayuwa kamar baya ta auri Sageer suna zaune lfy wlh na gama kwanciyar hankali maybe lkcn na huce amman idan ba haka ba, wlh dab dake da tsinema Kamal..." dede lkcn Mubina ta farka tana kiran"Umpah Kamal ne shine wlh ba laifi na bane karku tsaneni karku koreni fyade ne yamin..." Kamal da sauri ya miƙe ya fice yana rumtse idanunsa zuciyarsa na wani irin bugo da karfi ya done kunnensa, ya koma bayan window ya laɓe ya zuba mata idanu yana hawaye yana kallon bakinta na motsi. Mamu ta kamata da sauri Umpah ya temaka suka jinginata jik<n gado, yace"Auta buɗe idonki Umpah ne" Mubina tace"No Kamal ne." ta fada tana ƙoƙarin fizgewa idanunta a rufe tana kuka zabura ɗa tayi taji wani irin zafi a ƙasanta ta saki kuka da karfi. Mamu tace"Baby nice Mamunki fa ga Ablah ga Amrah ga momynki Sabeelah ga yayanki Majeed ko kin fasa binsa London ɗin kiyi aikin jarida a can...?" Mubina jin muryar Mamu ras yasa ta Ƙamƙameta Mamu gam ta saki ajiyar zuciya tana mgn can ƙasan makoshi cikin kuka, tace"Mamu Kamal ne yamin haka Mamu zanyi fitsari Umpah nah fitsari zanyi." ta faɗa tana fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka mata nauyi a hankali take budewa har suka buɗe tar....

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin**KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣5️⃣

A hankali ta sabke idanunta kan Mamu tana shasheƙar kuka, take kallon Mamu ɗin. Umpah ya kamata yace"Auta sannu yi hkr kinji taso muje na kai ki toilet kiyi fitsari." ya faɗa yana ɗaukanta. Se lokacin ta ɗago shanyayun idanunta, wanda suka rune sukayi jajur tana kallon jama'ar dake cikin ɗakin ɗaya bayan ɗaya, ta sabke idanunta kan Sageer, dede lkcn Umpah ya tsaya da ita ta fasa ihu jikinta yana karrrma, ta ririƙe umpah tace"Umpah zafi kace wannan shima ya fita anan banson ganinsa."ta faɗa daket tana rufe idanunta. Umpah ya ɗauketa ya nufi toilet, yana cema Mamu"ɗauko kayanta maza zo ki gyarata ki mata wanka."ya faɗa yana shigewa toilet. Mamu ta ɗauki doguwar riga ta atamfa da hijab da sabulu da mai tabi bayan umpah. Abbu yace"Sageer tashi kaje kabari har kome ya lafa yanzu kai kanka bazata saurare ka ba." ya faɗa ya kama Sageer da yake fitar da hawaye. Sageer ya beƙama Ablah maganin yace masu"Na tafi sai zuwa yamma zan leƙo."ya faɗa yana ficewa. Abbu yace "Allah ya kaimu." Umpah Mamu na shigowa ta kama Mubina shi ya fita.

Amrah ta kifa kanta saman cinyarta tana kuka. Umpah ya zauna ya rungumota jikinsa yace "Amrah kiyi hkr muna so mu nuna mata rashin damuwar mu a fuska haka zai saka ta saki ranta, har Allah ya baya lfy ta koma karatun ta , amman tana ganinmu a damuwa kullum cikin kunci zata zauna, dan haka kiyi hakuri dan Allah kibarma Allah kome kinji Amrah nah." ya faɗa yana mata cakulkuli ta saki murmushi. Umpah yace "yauwa Majeed Sabeela Amrah kuje gida kawai ku zauna dan Allah ku saki ranku. "Ke Sabeela kece uwarsu amman bakya nuna masu suyi tawakali? Kuje gida kawai, Azeeam Aleem maza aje ayi game ok..." Aleem da Azeema suka ce"Yes daddy ummi mu tafi gida." Sabeela tace to bari su Mamu su fito." Umpah yace"No kuje zuwa dare se ku dawo." ya faɗa ya janye Amrah daga jikinsa ya kama hannunta da na Aleem, Sabeela ta kama Azeema Majeed na gaba daman suka ma su Ummah da Abbu sallama suka fito. Kamal da ke laɓe a window yana kallon yana mai jin haushin kansa, ya zube nan ƙasa yana hawaye. Sageer kuwa yana fitowa ya shiga neman Kamal bai gansa ba ya nufi bayan ɗakin da aka kwantar da Mubina, ya tsinkayo shi yayi tagumi, Sageer ya karasa da sauri ya kamashi ya miƙe yace"Haba Kamal dan Allah ka rage damuwa kaddara kace tazo a haka bata yanda zaka tsallake, farin cikina daya iyayanta sun yafe maka , kuma nima ban riƙe ka ba wlh, muje gida ka samu kayi wanka kaci wani abun." ya faɗa yana kama hannunsa suka nufi gun mota.

Lkcn Umpah ya dawo daga rakiyar su Sabeelah zai shiga ya gansu. Ya tsaya yace"Yauwa kuje ya samu yayi wanka yayi breakfast, Kamal dan Allah kayi wanka ka nutsu ka fita aiki kaga abin nan ba wanda ya sanshi so dan haka ka ajiye hankalin ka kaji." Kamal daket ya buda baki yace"Naji umpah" Umpah yace"to kuje." Sageer ya kama shi suka nufi mota, umpah ya shiga gun su Mubina.

Mubina sai kuka take tana zabura ta riƙe Mamu gam tana cewa"Mamu Kamal ne ni bani da laifi Mamu na tsani Kamal bazan yafe mashi ba..." Mamu ta riƙeta tana ƙoƙarin cire mata riga tace"yi hkr Baby ki amshi kaddara haƙiƙa ya cutar damu, amman Allah ya kaddaro hakan bari kukan kinji jikin ki zafi rau." ta faɗa tana zuge mata zip rigar ta cire riga, wajan cire siket ma daket se kuka take tana kiran umpah... Haka Mamu ta lallaɓata ta mata wanka bayan ta gasata da ruwan gumi tana ihu da kuka.

Bayan ta idar mata wanka ta wanke mata bakinta ta mata alwalla, ta goge mata jikinta ta shafa mata mai ta saka mata doguwar rigar atamfa tasa mata hijab, tace"Taka mugani baby"Mubina ta kasa ko tsayuwa bare tafiya sai kuka. Mamu ta dauketa suka fito.
Chapter 44 · 0% Book details