← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 124

Sashe 1

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[08/07, 2:23 PM] +234 803 238 4602: *💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Wannan labari Kirkiraran labarine ba wai ya faru a gaske bane, idan kinji ko kaji yayi dai-dai da naku arashine, banyi dan cin zarafin wani ko wata ba*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Page 1️⃣*

.... *ALI ÆŠAN TSOHO*

Unguwace ta masu kudi a cikin garin maradi, wasu mahaukatan gidaje ne guda biyu, suna kallon juna kai kana kallon gidajan kasan masu shi sunci sun tada kai da kudi, ko cikin unguwar ma wannan ɓangaran ya fita daban, saboda wajan shiru babu hayaniya kowa na sabgar gabansa cikin gidajan su, sai kukan tsuntsaye da sansanyan kamshin frannai me dadi kakeji cikin hancin ka.
Ɗayan gidan me kallon gabas na kutsa kai ciki, ina shiga na kara tabbatar da lallai akwai arziki, saboda yadda gidan ya tsaru babu karya, tamkar ba a ƙasar hausa ba, ko ina franni ne kore shar me haɗe da pink colour, duk sun kewaye cikin maƙareran gidan mai girman gaske, ga ma'aikata nan na kai komo, ɓangaran ajiye motoci na kalla na jinjina kai saboda a ƙalla motoci sunkai 20 kala-kala babu kalar da babu, wada naga me wanke motocin gidan ya cire mata riga yana gogewa ce ta tafi da imanina, saboda kyanta baƙa ce sudik kirar *range rover 2020* baƙin sai sheki yake, baki na riƙe ina so naga mamallakin motar ko nace wanda zai shiga motar nan, da sauri na kutsa kaina ciki kofar wani hamshaƙin parlo na tsaya ina karema kofar glass ɗin kallo ta yadda zan iya bude wannan kofar ta glass, wani ɗan madanin baƙi na gani jikin glass ɗin a manne, nayi saurin dannawa ai kuwa kofar glass ta bude haka ya nuna min cewar daga ciki ba a saka mata security ba.

Kai na danna cikin parlon sai da numfashina ya kusa ɗaukewa saboda Wani irin sanyi da wani carpet da ƙafata ta shige, da kuma sassanyan kamshin dadi da ya daki hancina...
Tunani na ya katse dai-dai lokacin da nayi tozali da wani hadaddan gay, a ƙalla zai kai kima nin 30 years sanye cikin Suit baƙake, wanda suka masa mahaukacin kyau, yana saukowa daga saman wani haɗadɗan bene, cikin kuzari da zafin nama yake taka matattakalar bene ɗin, hannunsa riƙe da wayoyi masu tsada guda biyu, yana kallon tsadaddan ɓaƙin agogon hannunsa na zallar fata, haka takalmin ƙafarsa baƙi ne shima na zallar fatane wanda ake masa adon zamani sai mahaukacin kudi, dan yana ra'ayin irinsa duk da ɗingisawar da yake, sai ka lura zaka gane yana ɗingisawa, ma'ana duk haduwarsa ƙafarsa ɗaya da rabi ce, amma yana ƙoƙarin take hakan dogo ne ƙaƙarfa me murɗadɗan jiki, ba fari bane tas haka zalika ba baƙi bane, wato chocolet colour ne yanayin sa tamkar ɗan ƙasar Ethiopia, yanada manyan idanu da gashin girar ido gazar-gazar, yanada dogon hanci me dan fadi kaɗan, bakinsa madedeci me ɗan fadi shi ba karami ba shi ba babba ba, lips dinsa ya ɗan sa Ja kaɗan, kyakyawar fuskarsa kewaye take da saja ga wata yar ƙasummba gashi ma'abucin fara'a wanda hakan yay mugun ƙara ma kyakyawar fuskarsa kyau...

Yana dab da saukowa naji murya wata mata tana tafa hannuwa cikin muryata mai dadin sauraro, tana cewa"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Yanzu *Kamaludeen* saboda Allah saukowar ganganci kake , baka duba yanda kafarka take salon ka gangaro ka samu tashin hankali haba ɗa ɗaya tamkar da dubu..." Da gudun sa ya ƙaraso yana sakin murmushin da ya zame masa jiki, dan sam shi bayada tsuke fuska mutum ne mai faram-faram da jama'a. matsalarsa ɗaya tsani raini ƙo dede da kwayar zarra, baya zama waje ɗaya da mutumin da zai rainashi ko wanene.

Jikinta ya fada ya rungumeta cikin amon muryashi me daÉ—in sauraro yace"Oh my Umma nah É—anki jarumine fa , good morning ummah..."Abbu ne ya katse masa magana, ta hanyar dora masa cup É—in hadaddan tea a baki yana murmushi yace"Oya sha wlh baka fita haka ba dan naga kayi lati." baki Kamal ya turo yana lumshe tsumammun idanunsa ya kurbi tea É—in kaÉ—an..
Dariyar wata matashiyar budurwa ce kyakywa me kyan diri tana kama da Kamal sosai sai de ita baƙa ce, itace ta katse su tana tafa hannuwa, itace ta dawo dasu daga duniyar lallashin Kamal da suke,
Ummah ta janye shi jikinta ta kamo hannunsa tana dariya tace"Samha kin fiye sa idanu wlh." Samha ta zumburo baki tana bubbuga ƙafa tace"Allah nima se an lallasheni zanyi breakfast." Kamal ya watsa mata wani shu'umin kallo na yarinya nasha gabanki, ya mata gwalo, baki ta turo gaba tana kallon Abbu zata fara kuka.
Abbu ya kama hannunta yace"Haba Samha nah Oya muje kiyi breakfast kema." ya faÉ—a yana janye da hannunta, suna biye dasu Kamal har kan wani makeken dining are.
Suna isa ummah ta zaunar dashi cikin dubara da Abbu suka samu yasha tea ɗin kadai Samha kuwa sai da taji ba guri, tana tsokanar Kamal baibi ta kanta ba ya miƙe saboda ya makara, ya rungume iyayansa yay masu kiss yayi masu sallama ya fita, a gaggauce.
Samha ma ciki ta shiga ta fara shirin tafiya school..

*Kamal* yana fitowa ma'aikatan gidan suka fara kwasar gaisuwa, ya rinƙa amsa masu cikin sakin fuska.
Kai tsaye gun motar da Garba ya goge masa ya nufa cikin takunsa na kasaitaccan namiji, Garba na biye dashi yana cewa"takawarka lafiya ƙasaitaccan namiji Jika ga Amadu jinin Ali zaki ɗa ɗaya tilo ga *Alhaji Abubakar kan giwa mai Nasara*, zanso naga wace mai sa'arce Allah zai kashe ya bata tauraron Miji abin nunama sa'a..." Kamal hannunsa ɗaya ya ɗaga masa alamar dakatar dashi, ɗayan hannunsa ya tura cikin lallausar sumar kansa yana sakin murmushi yace"uhumm Garba Allah shiryeka , Oya buɗe min mota na wuce irin wannan koɗawa haka..."Wayarsa ta katse masa magana, sakamakon ringing ɗin da take, ya kalli screen ɗin wayar yaga sunan *Sageer* na yawo saman screen ɗin wayar, picking ɗin call ɗin yay ya kara a kunnensa.

Garba ya bude masa motar yana cewa"Yallaɓai ko dai na kirawo dire ba?" Kamal bai masa magana ya shige ya rufe motar yay mata key ya fizgeta da karfin gaske kamar zai tashi sama, ya nufi bakin tamƙameman get ɗin gidan yana horn.

Ya'u ya gaishe sa ya buÉ—e masa kofa a guje ya fice daga gidan.
Dirving yake sosai kamar ya tashi sama ransa ya ɓaci jin cewar yay lati har dalibansa sun fara shiga aji bai iso ba abinda ya tsana kenan a rayuwarsa.

*Maryam Abacha American University Of Niger*

Ciki Kamal ya danna hancin motarsa, iya haduwa University nan ta hadu ba karya kallo ɗaya zakai maya kasan ta haɗa ƴaƴan manya da kuma akasin hakan, babu ƴan ƙasar da babu cikin Makarantar nan ƙabila daban-daban.
Yana shiga ya nufi parking spece yay parking ya kwashi wayoyinsa da laptop ya fito ya rufe motarsa ko Office É—insa bai nufa ba ya nufi ajin da yake koyarwa yau direct ya shiga, dan ba wani jimawa zai ba 1 hours kawai ke gare shi..

Can ko cikin ajin da Kamal zai zo, class ɗin hayaniya ce ta ɓarke sai ihu da shewa kakeji, tamkar ba yan Jami'a ba sai kace wasu ƴan JSS 3 saboda Hatsabiɓiyar yarinyar nan dake ajinsu sam bata ganin ta girma.
*Mubina* matashiyar budurwa ce kyakyawa, tsaye take tana kwatanta tafiyar *Kangiwa* sai ihu suke suna zugata, farace sul ƴar siririya doguwa kyakyawa mai diraran jiki ga hips da boobs ƴar kimanin 20 years, masha Allah kyakywace sosai kallo ɗaya zaka mata kasan ta haɗa jini da larabawa, tanada doguwar fuska me ɗauke da dogon hanci da karamin baki, idanunta dara-dara farare tas lumsassu tamkar tana jin bacci, gashin idanunta gazar-gazar haka zalika girata me kyau, tanada gashi amma ba dogo ba sosai ya dai sauko kafadarta gashi da santsi, tana da dimples sharan kumcinta na dama wanda ko magana take sai ya loɓa duk inda kake neman kyakyawa *Mubina* takai, saide ta cika siririya sam batada jiki ko misƙala zarratin, saide akwai kyan diri da surah idan ka kalli hips ɗinta da boobs ɗinta zakasha mamki, suna tsantsar kama da muny roy ƴar india tamkar an tsaga kara, banban cinsu da muny tafi ta fari kaɗan da gashi dan Mubina batada dogon gashi sosai ya dai sauka kafadarta kuma ba baƙi bane ba maroon colour ne.

Sanye take da wani tsadaddan material baƙi ɗinkin doguwar riga yayi mata kyau matuka, gashin kanta yasha kwalliya wasu irin ribbon ta ɗaure rabi rabin ta zubo shi saman fuskarta.
Ƙafarta sanye da wani hills mai mutikar tsini tasha kunshin jan lalle yayi mata mugun kyau, zakayi mamakin yadda take takunta cikin nutsuwa hankali kwance da wannan takalmin me uban tsini..
Chapter 1 · 0% Book details