← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 124

Sashe 43

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Su umpah barawo bacci ya sace su suna manne da juna, basu farka se bayan gama sallah Asubah, Umpah ya fara tashi yayi saurin sakin Mamu yace"tashi sallah maza baby har yanzu bacci take baiwar Allah." ya faɗa yana miƙewa ya shiga toilet. Mamu ta matsa jikin Mubina ta taɓata tana baccin sam basu ma san lkcn da Dr tazo ta ta cire mata drip ba ta saka mata wata, gashi har ta kusa gamawa, lallai ta yarda asibitin akwai kula da jama'a sosai. Sauka tayi ta isa gadon da Abalah take ta tasheta domin sallah. Umpah yana fitowa ya nufi karamin masallacin da yake cikin asibitin domin yayi sallah duk gari ya waye. Bayan su Mamu sunyi sallah ne ta shirya domin zuwa gida taga yan gida daga can ta dauko kayan sawa, ita da umpah suka tafi suka bar Ablah.

Sageer bayan ya fito daga sallah ya shiga mota bai zame ko ina ba sai gidan goggo. Yana zuwa ya isko Kamal a kofar get yana jiransa, nan yay parking ya fito ya isa gun Kamal ya rungumeshi yana dariya yace"ta samu ne?" Kamal ya janye Sageer ya kama hannunsa suka shiga mota, Kamal yace"Sageer don Allah ina neman alfarma kuma nasan zaka min amman kafin nan ina neman yafiyar ka bisa gonarka da na shiga akan kaddara wada bawa baya tsallaketa, se alfarmar ina so ka auri Amrah wannan abin zakamin nasan kai masoyina ne na haƙiƙa..." ya karasa yana sakin kuka ya rungume Sageer. A rikice Sageer ya ɗagoshi yace"Subahanallahi! Kamal yau kaine kake kuka abinda ban taɓa ganiba kenan me ya faru dakai dan girman Allah ka faɗa mani kar zuciyata ta buga , dan nasan abinda zai sanyaka kuka wlh babba ne ba karami bane ba..." Kamal yace "Sageer nasan kaima bazaka fahimceni ba kamar yadda iyayena sun kasa fahimtata, Sageer kaddara ta afka mini bansa ta yaya nama Mubina fyade ba..."Sageer sbd tsabar rikita ya ture Kamal daga jikinsa yana girgiza kansa yana hawaye yace" Kamal meye kamin haka? meyasa kamin haka? kasan Mubina ita ce kome nawa, duk duniya banida abinso sama da Mubina wato kayi haka ne dan na auri Amrah kai ka auri Mubina ɗin kenan? Ko ya ne abun ya faru? To wlh bazan auri Amrah ba zuciyata Mubina take so duk da naji mugun ciwon abinda ka mata, amman sonta ko dai-dai da kwayar zarra bai fita a zuciyata ba! Dan haka zan tsaya mata kai da fata sai na mallaketa duk da ka mata illah ni bazan ga illaba ni sonta nake ba jikinta nake so ba, amman Kamal ka bani mamaki, wannan abinda kayi ba halinka bane." Sageer ya faɗa yana kecewa da kuka ya rungume Kamal yace"Kome zakamin bazan taɓa rabuwa dakai ba wlh ina sonka da zuciya ɗaya, yanzu muje naga halin da take ciki." Kamal ma kuka yake sosai ya rungume Sageer yana cewa"Ku yafemin haƙiƙa nayi babban kuskure mafi muni a rayuwata sai de ban isa na tsallake kaddarata ba." ya faɗa yana janye jikinsa ana Sageer ya buɗe mota ya fito yana cewa"Ina zuwa bari zan dauko maganin da Dr ta bani." ya faɗa yana nufar get. Yana shiga farlo ya hadu da alhaji tsoho mijin goggo Rumana yace"Ah Kamalu ashe nan ka kwana sai da zani masallaci naga motarka, goggo bata faɗa min ba?" Kamal yace"Eh Alhaji ina kwana" alhaji tsoho yayi mamaki dan yasan Kamal baya ce masa alhaji sak tsokanar sa yakwe sosai. Amsawa yayi yana cewa "Kamalu kana lfy dai ko?" Kamal yace ina lfy Alhaji" ya faɗa yana shigewa. Yana shiga ya ɗauki jallabiyar da ya cire ya ciro maganin ya fito, suka gamu da goggo tace"Ina zaka?" yace"Zanje na duba Mubina ko da a laɓe ne, bazan bari ta ganni ba ga kuma maganinta se na bayar a bata..." goggo ta katse shi tace"Bazaka bari sai anjima ba?" Kamal yace"Goggo kenan anjima ɗin ɗa yanzu duk na Allah ne na tafi." ya faɗa yana fita. Yana zuwa ya shiga motar Sageer bai iya magana ba yaja motar yabar wajan. Saida ya hau tati sosai Kamal ya faɗa masa sunan hospital ɗin, Sageer ya nufi can.

Abbu da Ummah ana gama sallah Asubah suka shirya suka nufi hospital. Da sallama duka shigo, Ablah kadai suka samu zaune tana riƙe da hannun Mubina. Ablah ta amsa sallamar, Abbu ya duƙa ya gaisheta, ta amsa yana tambayar me jiki tace "Gatanan dai sai bacci"Ummah ta zauna kusa da Ablah tana kallon Mubina sai hawaye. Ablah tace"Wlh kubar kuka ai ba laifin ku bane mun rigada mun amshi kaddara." Abbu yaji dadin maganarta sosai, yace"Ina su Umpah ɗin?" Ablah tace sun tafi gida zasu zo yanzu..." Haka dai suna zaune jugum zuciya babu dadi...

Suna zuwa Sageer yay parking ya fito Kamal ma ya fito, suka rankaya ciki. Da sallama suka shigo Abbu ya amsa Sageer ya isa ya gaishe su, Abbu ya amsa bayabo ba fallasa. Ya gaishe da Ablah ta amsa tana cewa"Sagiru ne ko?" Sageer yace"Ablah nine ya hkr?" Kai ta jinjina tace"Hkr se ma'aiki." Kamal kamar kazar da kwai ya fashema a ciki haka ya iso ya duƙa yana gaishe da Abbu da Ummah babu wanda ya amsa. Ya gaishe da Ablah ta amsa a ciki ciki ya ƙurama Mubina idanu yana fitar da hawaye ya ciro maganin yaba Sageer yace"dan Allah a bata tasha da zaran ta farka taci abunci." ya faɗa yana miƙewa har yanzu Mubina yake kallo. Ya juya gun Ummah yace"Ummah ku yafeni nan gaba kadan zaku gane bason rai..."Mari Abbu ya ɗaukeshi dashi yace,"Fita bamu waje kar ta farka ta ganka."Kamal fita yayi kofa ya zauna ya haɗa kai da guiwa, zuwa yanzu ya yanke hukunci ana jimawa karfe tara zai kai kansa kotu gwamma ayi duk wacce za'ayi amasa hukunci kowa ya huta ko iyayansa zasu rage tsanarsa a ransu...

Su Mamu kuwa suna zauwa gida a parlo suka sami su Amrah wacce har yanzu kuka take, Sabeelah na lallashinta. Saida Umpah yasa Laure tayi maza ta haÉ—a masu kayan karin kumallo, lkcn kuwa tuni ta dora daman sanin suna hospital, ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito, lkcn an haÉ—a masu breakfast an jera a kan dining, ya haÉ—a kansu duka cikin wayo da dubara Umpah yasasu gaba kowa saida yay break É—in duk babu wani dadi da kansa yaba Amrah yana kwatanta mata babu me tsallake kaddara sa, su barma Allah kome. Bayan sun gamane yaja masu kunne lallai cewar maganr ta tsaya iya su haka ko Mamu karta kuskaura ta faÉ—ama Baffa inusa da inna ko yayunta ko kanninta su rufama Æ´arsu asiri kawai, haka kaddarata tazo. Kowa yayi na'am da hakan sun yarda daga nan laure ta hado masu abinda zasu tafi dashi hospital, suka fito suka rankaya baki É—ayansu hospital.
Chapter 43 · 0% Book details