Sashe 83
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Æangaran Ibrahim kuwa gidansu Iyamu ya nufa, yana zuwa yay parking kofar gidansu, ya Æ™irata. Iyamu tana zaune a tsakar gida tayi tagumi, Leezah kuwa na sha'anin gabanta. Wayarta da take gefe a ajiye, ta É—auki ringing, da sauri ta kalli wayar ganin Æ™iran ibrahim ne yasa ta É—auki wayar cikin rawar jiki, tai picking É—in call É—inta ta kara wayar a kunnenta, tace.
"Angone ina ka shiga na kiraka yafi sau ɗari?' Ibrahim yace mata" Sorry amaryata 8na busy ne gani kofar gidanku zo mana."Iyamu cikin zaƙuwa ta miƙe cikin murna, tana cewa"haba dan Allah! Ok gani nan yanzu."ta faɗi tana nufar cikin ɗaki da gudu. Leezah tabita da harara tana cewa"Shegiya wlh bazaki aureshi ba, sai nayi maganinku ." ta faɗi ta muƙewa, ta nufi kofar gidan. Iyamu cikin sauri ta shirya ta fito. A kusan kofa suka haɗu da Leezah, iyamu tace"Ina kikaje?" Leezah tace"Ina kuwa zani leƙe nake naga waye kikema rawar ƙafa haka." ta faɗa tana tafi. Iyamu murmushi tayi ta fice.
A cikin mota ta isko Ibrahim. BuÉ—e mata yayi ta shiga ta zauna, cikin kunya tace"Angon ina yini." murmushi yay yace.
"Lfy lau ykk ya jin daɗi ya shirye shiryen aurenmu?" murmushi tayi ta rufe fusksrta, tace" ina tayi." ta faɗi tana cire camera ɗin daga cikin rigarta, ta beƙama ibrahim, ya amsa yana cew"Wow amaryata, kice yau zamuga ƴan iska a fili...?" ya amsa ya faɗin haka. Iyamu dariya tayi dan bata gane me yake nufi ba. Kunnawa yayi ya fara cikin karo da munanan kalaman su Alhaji Mounkaila da Tukur, babu ko riga ajikinsu cikin ɗiyan cikinsu, suna faɗin abinda Kamal yay Mubina ta yadda suka ba su Iyamu maganin ƙarfin sha'awa da na maye, da duk yanda abin ya kasance suna dariya. Ibrahim dakyar ya ɓoye ɓacin ransa, da tashin hankalin da ya shiga.
Ya jinjina kai yace"bari na goge wannan shirman kai amman nayi sa'ar mata tagari yanzu bari naje office na kammala wani ɗan aiki sai na ƙiraki ki faɗamana inda zamu neman auran gobe." cikin murna iyamu tace.
"Tnx angona haƙiƙa kai masoyine nagari, duk mugun halina zaka aureni, ni nayi babbar sa'a a duniya." ta faɗa tana hawayen farin ciki. Ibrahim yace"Ai ke ɗin abar soce, yanzu shiga gida sai munyi waya anjima." motar ta buɗe ta fito, kiranta yay ta juyo yace"Ngd sosai da temakonki gareni naji daɗin yanda kika bani haɗinkai har zamuyi aure." kunya taji ta nufi cikin gida da gudu. Ibrahim yace, "zakuci ubanku yau ba gobe ba, a hannun iko zaku kwana." ya faɗi yana motar key, ya fizgeta yabar kofar gidansu iyamu, kai tsaye *Kamaluddeen Kan Giwa Mai Nasara,* ibrahim ya nufa, yana sharara gudu ya ƙura Goggo Rumana yana faɗa mata, nan tace gatanan zuwa gidan Abbu, ya ƙira Hafsat da Sumaiyya ya faɗa masu, cikin murna kowace ta fara shiri daga gidanta zuwa gidan Abbu.
Abbu kuwa bayan ya fito sallar la'asar yana zaune, a cikin office ya janyo wayarsa ya kunna data yaga ko Kamal yana online, dan ta whatsapp suke hira yaƙi yarda ya ƙira aga number london. Abbu yana buɗewa yaga sakon Mubina, yay murmushi yace.
"Ah Mubina vedion me na samu, ne?" ya faÉ—a yana buÉ—e vedion, ganin tanad aÉ—an nauyi ya danna voice note É—in ya fara saurara. Idanunwa Abbu ya zaro, ya danna vedio É—in ya fara kallo, ga Kamal tsaye yana rattabo bayanai yana son Mubina ta amince itako ba'a ganinta sai dariya take tana cewa"Kan Giwa" shi kadai akeji nata. Abbu ya dafe kansa yace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Kamal! Oh ni Abubakar me zan gani? Yanzu daman da gaske yake london ya iske ƴar mutane, ba Germany ɗin yajeba ba? Shiyasa baya ƙira sai whatsapp? Yanzu itako yarinyar nan har ta manta abinda yaron nan ya mata har ta iya tsayawa kusansa ta iya buɗar baki cewar mu yafe masa na faɗama mahaifinta a aure mata Kamal...?" Abbu ya faɗa yana miƙewa zufa ta keto masa sam baima san mai zaiyi ba! Key ɗin mota ya ɗauka ya fito da office ɗinsa, yace masa sakataransa.
"Zanje gida idan anzo nema kar jirani ba lallai na dawo ba ma sai gobe." yana gama faÉ—in hakan ya fice, sakataran nashi na amsa masa cikin girmamawa. Mota Abbu ya shiga direct, ya nufi gidansa.
Umpah A ɓangaransa shima yana gida tin bayan dawowarsu gida da Mamu bai fita ba, suna zaune a parlo suna shan hira, shida Zubairu dasu Ablah, Amrah na kusansa zaune, Umpah yace da Zubairu.
Eh ai abokina ne mahaifinta, kuma yarinyar itace ƙawar Mubina ce, insha Allahu munyi mgn gobe zamu nema masa auranta." Ablah tace"Allah ya kaimu da ran da lfy gwara a haɗamin jikokina duka uku a aurar dasu." Mamu murmushi tayi tana jin daɗi sosai auran ɗiyanta duka uku ake son haɗawa lkc ɗaya. Amrah ta amshi wayar Umpah tana dannawa tace"Umpah yau kun gaisa da jikar Ablah kuwa?" ta faɗi tana kunna datar Umpah ɗin. Murmushi yayi yace.
"Eh sosai ma kuwa."Ablah tace"Wlh Amarah ki fita a idanuna fa." Amrah kuwa ganin saƙonni suna shigowa harda na Mubina yasa tace"Lah Umpah amshi ƴar gidanka ta turo maka sako."ta faɗi tana bashi wayar, Umpah ya amsa ya shiga duba sakon yana cewa.
"Ta koma gida kenan?"
Ya faɗa yana danna voice note ɗin.... Idanuwa Umpah ya zaro tin a farkon jin kalaman Mubina, yana zuwa ƙarshen jin ta ambaci Kamal takeso ya aura mata suna tare a london, ya kawo mata ziyara Umpah, ya miƙe tsaya cak yana zaro idanu, yace.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ya faɗi yana buɗe video ɗin. Mamu da Amrah da Ablah kusan tare suka miƙe hankalinsu a tashe suka haɗa baku wajan cewa.
"Me ya faru da Mubina ɗin....?" Umpah baiyi magana ba, saboda zubar da take keto masa a jikinsa, dakyar ya iya cewa"Ku matso mu kalla tare." ya faɗi yana kunna video ɗin. Zubairu yace, "Meke faruwa ne?" Umpah baiyi magana. Idanuwansu suka zuba kan wayar suna kallon ikon Allah. Mamu ce ta fashe da kuka tace"Na shiga uku binta london yayi kuma? Yanzu Mubina ce ke ɗaukarshi har tana dariya? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ablah kuka ta saki tace"Shikenan ya kuma wlh ya kuma mata wani cikin mun shiga uku, wallahi ya mata asiri ya haɗata manya manya matsafa, taya Mubina zata iya magana wannan shegen yaron mai zubin samudawa, wlh ya kaima manya matsafa sunanta..." Umpah ya goge zufar goshina, ya kunna masu voice ɗin da tayi da bakinta. Mamu dabas ta zauna ƙasa hawaye na kwarara daga kan fuskarta, ta kasa magana.
Zubairu yajinjina kai, ya kalli Ablah dake famar faɗin ya tsafeta. Yace"Ablah kuyi hakuri don Allah wannan fa barinsu gari ɗaya hatsarine, ni abinda nagani shine kawai mu ɗaura masu auran, tunda suka nema kokuma a tisa ƴar gidan jiya..."Ablah tace da Zubairu, "Amshi nan kaci gidanku Zabai wlh bazata auri wannan ɗan banza yaron ba..." Amrah kuka kawai take tamkar an aiko da mutuwa. Umpah da idanu yake binsu zucuyarsa na wani irin bugawa, tsoron lamarin yaran ya shigeshi, sai yanzu yayi nadama tin farkon da Abbu yazo nema masa auranta yace tayi ƙarama karatu zatayi.