← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 124

Sashe 72

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iyamu sam bata gane shi bane sbd glass motar me duhu ne sai da ya janye glass ɗin, motar ya leƙo yana murmushi ta waro idanu ta isa gaban motar tana dariya tace"My hasband nawa." murmushi yay ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Leezah ta cika tayi fam sai hararasu take a ɓiye. Ibrahim kuwa ya lura sarai da ita. Yace "Hajiya Leezah shiga mana na sauke ku a gida."murmushin dole ta ƙaƙalo ta shiga seat ɗin baya ta zauna tana cewa.
"Ina yini" Ibrahim yace"lfy lau ya jin daɗinki?" murmushi Leezah tayi tace"Jin daɗi babu ku ai banzane." iyamu ta juyo tana kallonta. Leezah tayi saurin cewa, "Yes jin daɗi sai da maza mana." dariya iyamu tayi. Shide driving ɗinsa yake bai saurare suba. A kofar gidansu yay parking, Leezah ta fita. Iyamu ta fara masa zubar banza. Yace"kinsa abinda nakeso dake matar?" iyamu cikin zaƙuwa tace "A,a yace.
"A gida ne an matsa min na fito da matar aure ni kuma gaskiya ke nake so dan haka kiyi ƙoƙarin koda ƙiransu ne su dawo ki nuna a matse kike dasu kuma bakya iya ba kowa kanki sai Tukur, ki dai san yanda zakiyi suzo cikin kwana ɗaya ko biyu , idan kin ɗauko min video na gani da gaske sune suka sakaki aikata wannan abun sai na turo gidanku tambaya, dan ina tantama gaskiya, manyan mutane su iya haɗa makirci haka..." Iyamu ta riƙe hannunsa tace"ka yarda dani Wlh sune amnan zanyi yanda kace insha Allahu ka bani kwana biyu."Ibrahim yace.
"Ok ina jiranki zan wuce sai zuwa gobe zan kiraki musha hira." cikin murna iyamu ta fito ta rufe masa kofar tana ɗaga masa hannun. Motar yama key a guje yabar kofar gidan nasu. Cikin murna ya kira Hafsat ya fada mata da Abbu, sosai sukayi murna dan suna son kome yazo ƙarshe.

Daga wanka ya fito yana ɗaure da towel kirjinsa mai yalwar gashi na ɗigar da ruwa, ɗan guntun towel ɗin hannunsa ya saka ya goge lallausar sumar kansa wacce ke jiƙe da ruwa, kafin ya goge jikinsa, ya isa gaban dreesing mirror ya tsaya, ya shiga murje murɗaɗɗan jikinsa mai laushi da lotion iri-iri masu sanyin daɗi, sai ƙamshi ƙe tashi wata ƴar ƙaramar kwalba mai kyan gaske ya ɗauka ya buɗe ya shiga shafe gahin da ke kwance saman faffaɗan kirjinsa. Bayan ya gama ya gyara sumar kansa mai yalwa tamkar ta larabawa, luf a kwance sai sheƙi take, ya shafa mata wani man kai mai azabar kamshi, kan ya ɗauki walƙiya, ya gyara sajan fuskarsa da ƴar ƙasumbar da ya tara, Kamal yayi wani irin kyau da sheƙi, sai wani fitinanan ƙamshi yake tashi ajikinsa. Ya nufi wardrobe ɗinsa ya buɗe ya ƙurama kayan idanu yana ɗan waro lumsassun idanunsa, ya beƙa hannunsa, ya zaro faral jallabiya sabuwa dal mai masifar kyau da tsada ya saka, wow gabaki ɗaya shigar larabawa yay abinka da yanda fatarsa ta ƙara goge yayi haske sosai ga madarar kyau zaka zaji irin larabawan nan ne da basu cika fari ba sosai, barin hiramin da ya saka masha Allah, ya dawo ya ɗauki perfumes ɗinsa masu shegen daɗi ya fesa ya manna farin galss ɗinsa kan fuskarshi. Wayarsa da take manne a charge ta soma ringing yay saurin zuwa gareta ya cirota a charge ganin mai ƙiran yasaka Kamal ɗauka da sauri ya manna saman kunnensa, cikin daddaɗar muryashi da harshen turanci ya fara magana yace.
"Holle makel meye lbr please?" ya faɗi yana lumshe tsumammun idanunsa. kusan second 30 Kamal yay idanunsa a lumshe kafin ya buɗe ko me A ka ce masa ta wayar, yace"Ok gud tnx Makel bye." ya faɗi yana tsinke ƙiran, wayar ya ƙurama tsumammun idanunsa, yana sakin wani sihirtaccen murmushi. Kafin ya saka wayar cikin aljihunsa ya ɗauki ɗayar Wayar ya saka aljihun yaja trolly ɗinsa wacce babu abinda bai zuba ba wanda zai buƙata ya fito ya murzama kofar parlo key ya nufi compound , se da ya buɗe gate ya dawo ya shiga cikin haɗdaɗiyar fara motarsa ya mata key ya cinna hancin motar waje. A kofar gidan yay parking ya fito ya ƙarƙamama gidan kwado, yana murmushi yace" bye sai nan da 5 days zan dawo maka da baƙuwa i miss u sai na dawo." ya faɗi yana murmushi. Ya nufi mota ya shiga yay mata key ya fizgeta da karfin gaske, ya ciro wayarsa ya saka mata earpiece ya manna a kunnensa ya kira kawu Jafar cewar ya taso zauwa Madinah yana hanya. Nan ya masa Addu'a cike da murna, Umaimah da take kusa kawun nasa saida ta amshi wayar suka yi hira yace mata yana driving har ya iso, ya kashe yana dariya....

Goggo Rumana na zaune tana tsefe kanta ita ɗaya a parlo, su daga inda take tana jiyo hayaniyar ƴan jikokin nata A compound, da sukazo weekend. Wayarta ta ɗauki ringing, ta duba taga Kamalu ne, tai picking ɗin call ɗin ganin Kamal ne dan yanzu sosai suke hira. A kunnenta ta kara tare da sallama tana cewa"Kai!! Wlh Kamalu ka dawo gida kaci gaba da kama companynka kai ko tausayin Abubakar bakayi, koda ke nan da ƴan kwanaki , idan yazo saudiya ɗin bayan auranku da Umaimatu dole ka dawo ƙasar ku..." Kamal yace ke!! Goggo mai fura shiru! da wannan bakin naki mai cike da goro , kiji labari kinsa me?" Goggo tace ni ban saniba..." Kamal yay murmushi yace.
"Yanzu ina kan hanyar zuwa Madinah bari har na sauka zan gayamaki barnar da zanyi wollah..." goggo Rumana tace" Kaci gidan ku barnar me?" Kamal ya bushe da dariya har steering motar na neman ƙwace masa. Daket ya taka burki da karfi. Muryasa can ƙasa yace"da kin kasheni da dariya yanzu dai bari kiji wata magana , kuma Amana idan kika faɗi ma wani wollah Amana sai ta ciki kuma zance kece kika bani shawara." ya faɗi yana murmushi. Goggo Rumana da ta ƙosa taji meye tace"Tafi can ancema ni anajin mutuwar sarki a bakina ne....?" Sauran maganar tace ta laƙe jin abinda Kamal ɗin ya faɗi mata yana yanke ƙiran yana kyalkyata dariya. Goggo ta zaro idanu tana cewa"Kai!! Kamalu Wallahi....!"
Afuwa ba Editing sosai ina busy😌

```Rahma ce ummu Fareesa Real Laɗingo😍```

*KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣&4️⃣

"Kamalu kafa kiyayeni ko gama sauka mahaifinka baiyi ba, zaka sake ɗauko masa magana wallahi ni dai ba'a haka dani, zan ƙirana na faɗa masa tin wuri, kai ko tsoro baka ji ne wai...?" ta faɗi tana kasa kunnuwa taji maganar Kamal.
Shirun da Goggo taji ne ya saka ta ciro wayar daga kunnenta, taga wayam ba ƙiran Kamal ya tsinke ƙiran. Tace "Tab amana ta cika yaro ni ba'a haka dani, bari na kira mahaifinka yanzu yanzu yaci mutuncin ka." goggo ta faɗi tana lalubo number Abbu ta danna masa ƙira taji yana amsa ƙira. Kamal kuwa yana tsinke kiran yana dariya yace.
"Haba goggo ai ban fito ba se da na shirya , nake yarda ki datsemin nufina." ya faɗi yana lalubo number Abbu. Lkcn kuwa Abbu yana company, suna gudanar da wani taro, haka ya tsame cikin mutane ya amsa ƙiran, ganin Kamal ne. sallama Abbu ya masa yace. "Kamalu ya saudiya ɗin?" Kamal yace.
Abbu muna lafiya yanzu haka ina hanyar xuwa Madinah ne gobe zamu Germany gun taro, na kira goggo ina fa tsokanarta wollah ta rikice wai ta zata iya gaskiyata nake faÉ—a mata , niko tsokana ce." ya faÉ—a yana murmushin mugunta, dan yasan ya gama É—aure goggon.
Abbu yace" Kamalu kaci gidan ku, ka rikitamin uwa kaga ni zan koma muna taro ne Allah ya sauke ka lafiya ka gaishemin da kawunka da Yumnah da Umaimah da, Raihana auta ai Anwar yace idan naje tare zamu zo zanyi É—a." Kamal yace"Ok bye." ya faÉ—i yana tsinke kiran. Ya ajiye wayar ya maida hankalinsa kan driving, yana ciza lips É—insa a ransa yana cewa"Yarinya Sai na koya maki hankali wollah..."
Abbu kuwa yana juyawa zai koma gun taron, ƙiran goggo ya shigo, picking ɗin call ɗin yay ya kara wayar A kunnensa, yana shirin sallama. Goggo tace.
Abubakari wallahi ka gaggauta ƙiran Kamaluddin ka jamasa kunne, ya kama hanya zai tafi lindon ko ina gun yarinyar nan wai kasan ma me yace min?" Abbu yayi dariya yace" Ummu nah yana janki ne Madina ya tafi gobe zasu Germany gun taro, ya ƙira ya faɗamin kome fa." Goggo ta sauke ajiyar zuciya, tace " Kaji ja'irin yaro ko zan kamashi ne." Abbu yace" Ai kuwa karki masa ta sauƙi, Goggo zan shiga gun taro ana jirana." Goggo ta masa fatan Alheri sukayi sallama.
Chapter 72 · 0% Book details