← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 124

Sashe 108

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a parlon tin bayan gama lunch ɗinsu jira suke cikin nishaɗi Kawu ya ƙira Abbu sukasha hira Kamal sai dariya yake. Mubina duk hira da ake hankalinta akan Kamal ta wani marerece, abin tausayi. se satar kallonsa take, kunya ta hanata tace ya tashi suje ya ƙira mata ƴan gidansu. Miƙewa tayi cike da ladabi tace da Yumnah da Kawu Jafar"Dady Umma se da safenku zan kwanta kaina ciwo yake bari na shiga wajan Umaimah na kwanta." Ta faɗi tana nufar bedroom ɗin. Kamal ya zaro idanunsa waje ai baisan lokaci da ya miƙeba yace"Muje kisha magani kafin nan ya faɗi yana kamo hannunta. Su Kawu dariya suka masu, Anwar yace"Iye kaji amare kema ya zaki kwana anan wa zaibashi abincin sahur?" Yumna ta mike tana cewa"Yauwa Mubina zo amshi kayan sahur ɗinku na haɗa kome wannan kular abince kwana da yini yake baya hucewa." ta faɗi tana nufar kitchen. Mubina ta janye hannunta tabi bayan Yumna suka shiga kitchen. Wani babban kwandone ta zuba masu kome a ciki harda plate biyu da spoons biyar da su drinks tufa, banana gorar ruwa biyar, masha Allah tamkar wanda zasuyi sati sunaci haka ta haɗo masu kayan sahur, daket Mubina ta iya cira kwandon Yumna tana dariya ta ƙugama Kamal kira ya iso. Tace"Ɗauki kayan nan bazata iya ba." Amsa yayi yana murmushi suka fito. Mubina ta sake masu sai da safe, Anwar yana tsokanarta tayi murmushi ta fice. Kamal na biye da ita bayan yama su Kawu sallama.
Tsaye Mubina tayi jikin kofar har Kamal ya iso ya ajiye kwandon yana buÉ—e kofar, Mubina ta rungumeshi ta baya ta zagaye hannuta saman cikinsa ta kwantar da kanta gadon bayansa. Murmushi ya saki yace.
"Sweetie sakeni mu shaiga ciki ko." A shagwaɓe ta ƙirasa"Habibina" Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya mannenta saman ƙirjinshi ya ɗago da kanta yace"Na'am My sweetie Habibiyata, Oya faɗamin menene?" ya faɗi yana matso da fuskarshi dab da tata yana hura mata iskar bakinsa mai fitar ƙamshi, yana shafa bayanta. Ƙara shigewa jikinsa tayi, ta cinno baki gaba tayi ƙasa da murya tace"Habibina ka bani Umpah mu gaisa wollah ni kuka zan maka yanzu tin ɗazu nakebin kanka kaƙi ka bani, gashi har dare ya fara kuma inason naji lafiya Mamuna da da ummi da Kausar ga Basma ma nayi missing ɗinta, ga yaya Kabeer Aunty Amrah duk, yo kai haka ake daga aurena ka rabani da kowa nawa." ta faɗi a sangarce tana sakar masa kukan zallar shagwaɓa tana ƙara ƙamƙameshi. Kamal yace.
"Ya ilahi haba Sweetie please yi haƙuri wallahi zan baki su kuyi magana muje yanzu ki nutsu na sakaki bacci me daɗi." ya faɗi yana shirin cicciɓarta sama. Fizgewa tayi daga jikinsa, tana kuka ta cire key ɗin kofar tayi wufff ta shige ta banko kofar ta murza key. Idanu Kamal ya zaro ya kama handle ɗin kofar yace"Natuba Habibiya zo buɗe wallahi tallahi yanzu zan ƙira su na baki, bana son kije ki tafko mana ƙwaɓa shiyasa naƙi amman yanzu zan baki, Sorry my sweetiena zo buɗema mijinki kofa Kamal ɗinki nefa, ɗan gurgunki zo haba Mubeen ɗan kurma Deen ɗinki ne fa, zo kiji sweetie please..." Cikin shasheƙar kuka tace "Ni ƙyaleni ba wani nan wlh a waje zaka kwana, bazan buɗe ba ka ƙara harzuƙani, danme zaka cewa Habibina gurgu? Wlh karka sake cewa mijina gurgu..." ta ƙarashe maganar cikin kuka.
Kamal ya dafe kansa Yace
"Oh my God bakisna ya nakejin zafin kukanki wlh." ya faɗi yana dafe da kansa, yanajin zafin kukanta fiye da kome, yayi magiyar duniya ta buɗe masa kofar taƙi. Dubara ta faɗo masa da sauri yace.
"Yauwa ..." *~(Please kuyi manage naso na raka labarin yau amman banajin daɗine...... Nasan ba lallai bama Pagen wannan ya maku sweet, wallahi cikin dauriya nayi typing ɗin.)😲~*

```Ladee me wando😅Ladingo Oummu Fareesa ce🤸🏻‍♀️```

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣

"Umaimah Alhmdllh gwara da Allah ya kawoki, kamamin wannan kwandon muje can É—akinki mu kwana, Matata ta rufemin kofa, ai zaki yarda mu kwanta gado É—aya ko...?"
Kamal ya faɗi yana ƙunshe dariyasa, dan yaji Mubina na tafe da gudu tana cewa"Wallahi zanyi barna ba shegiyar da zata kwanar min da mijina." tana faɗin haka ta buɗe kofar. Tana waige waige, Kamal yay saurin kamota yana dariya ya rungumeta yace.
"Yes seni Mijin Mubina iyayan kishi, wasa fa nake maki gashi cikin sauƙi an buɗemin kofa." ya faɗi yana sumgumarta, ya shige cikin parlo. Abin ma dariya yaba Mubina ta tsayar da kukan ta ƙura masa idanu tana cinno baki, ta ɗora hannunta sumar kansa taja da karfi, a sangarce tace. "Kamal Habibina kasa naji cikina ya murɗa ya zan yarda wata ta kwanarmin da Mijina, Allah ni Habibina karka sake min irin wannan wasan ai kasan wasa nake maka bazan barka ka kwana a wajeba." Ta faɗi tana haɗe face ɗinsu ta kamo ƙasan haɓarsa tana tsotsa still hannunta cikin sumar kansa tana shafawa.
Kamal yace"Ashhh Sweetie zan ƙara fa." ya faɗi yana ƙoƙarin ajiyeta. Mubina ta ririƙeshi ta saki kukan sangarta, tace. "Wollah Habibina naƙiya, sai ka goyani bazan sauka ba." dariya ya fara yana ƙoƙarin ɓanɓareta, ƙiyawa tayi tana maƙaleshi tana kuka.
Bayansa ya saɓata ya goyata, ai kuwa ta shiga ɓangala dariya, ta saƙalo hannunta wuyansa tana cewa"Habibina bayanka daɗi wollah." ta faɗi tana kwantar da kanta gadon bayansa tana dariya. Kamal wani irin farin ciki ya tsinci kansa a ciki ganin yasa Sanyin idaniyarsa dariya.
Bakin kofar parlon ya É—auko kwandon abinci su ya shigo ya murzawa kofar key.
Saman table ya É—ora kwandon, ya jide ruwan da juice É—in ya nufi bedroom É—insu, tana bayansa tana masa surutu, shiko se murmushi yake.
Yana shiga ya buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ya jera ruwan da juice, duk tana bayansa.
Yace"Sweetie sauka muyi wanka mu kwanta ko?" A shagwaɓe tace"Habibina to kaini toilet ɗin a bayanka." murmushi yayi ya nufi toilet ɗin tana bayansa. Kayan jikinta ya cire mata, shima ya cire ya rungumota ya kunna masu shower. Luf Mubina tayi ƙirjinsa ruwan na daukan kansu. Bai tsaya wani wasa da itaba saboda, dare ya fara so yake suyi bacci kafin lokacin sahur. Iya gama masu wanka ya naɗota cikin towel suka fito.
Bayan ya shafeta da body lotion, ya saka mata kayan bacci, ya fesheta da turare, shima ya shirya ya kama hannunta sai baxa ƙamshi suke.
Ƙwantar da ita yayi, kashe kwan ɗakin yay ya ya kwanta, saman ƙirjinsa ya ɗora ya jamasu blanket. Mubina ta narke a ƙirjinsa sosai, ta ɗora hannunta cikin sumar kansa, tana murzawa, ta ƙirasa.
"Habibina." Ƙara zagaye hannunsa bayanta yayi yana murza fatar bayan nata, ya amsa" Sweetie ya akayi ko zaki bani kaɗan na daɗa muji daɗinmu?" laluɓo dantsan hannunsa tayi ta tsinkesa a shagwaɓe tace.
"Wlh bazan badaba kaida kakemin da zafi babu daɗi ko kaɗan ɗazu na kusa amai fa." ta faɗi tana sakar masa kukan sangarta. Kamal yace"Oh my god ok naji Sweetie nah bazaki bayar ba, yi haƙuri muyi baccinmu." ya faɗi yana kai bakinsa kan kunnenta, yana bata kiss. Mubina tayi luf jikinsa tana shafa sumar kansa, tace"Habibina please ka ƙiramin su Umpah kaji sir kangiwa, Honey."ta faɗi tana tura hannunta ƙasan wuyansa tana shafawa. Ɗan zame jikinsa yayi anata ya miƙe zauna ya beƙa hannunsa gefen katifar ya ɗauke wayar. Cikin murna ta zauna kan ciyarsa tana dariya.
Dialing ɗin number ta Umpah Kamal yayi, cikin sa'a kuwa dukansu suna parlo, yana ƙiran Kamal ya ɗaga, tare da sallama.
Cikin girmamawa Kamal ya gaishe da Umpah ya amsa. Mubina ya rungume tsam ƙirjinsa ya manna mata wayar a kunnenta, yana shafa lallausan gashin kanta, yace"Oya yi magana."cikin zumuɗi, tace.
"Umpah na ina yini i miss u ina Mamu na?" Umpah yace"Ah Baby ya gida ya saudiya, fatan kina lfy?" cikin shagwaɓa tace"Lfy lau Umpah sai kewarku, ina Ablah da antyna da yaya Kabeer?" Umpah yace gasu duk muna tare." ya faɗi yana beƙama Mamu wayar. Mubina tace"Mamuna i miss u i love Mamuna."Mamu tayi tace"Me too Baby ya gida da kowa."Mubina ta ƙara shigewa jikin Kamal, a sangarce tace"Mamu ina lfy kowa lfy Mamu anga wata anan gida ko?" Mamu cikin murna jin ɗiyarta lafiya lau daga muryata ma yasa tayi ƴar dariya, tace.
"Auta ai ko bamu ganiba ku kungani bare an gani a ƙauyan doutchi." Haka Mubina tabi ƴan gidansu ɗaya bayan ɗaya sukasha hira, harda laure mai aiki tace a ƙirawo, suka gaisa idan tana hira Kamal ya taɓo mata wani guri sai ta kyalkyale da dariya tana cewa"Wayyo Habibina." Haka suka gama hira iyayanta da ƴan uwanta cikin farin ciki dan sun gano ba ƙaramin kulawa take samu wajan Kamal ba.... Haka ta saka masa number ummi ya ƙirata sukasha hira tana zubawa ummin shagwaɓa. Ta kuma saka masa number Basma ya ƙirata sukasha hira da Mubina harda kukan missing ɗin juna da sukayi. Daga ƙarshe ya ƙira Kausar sukasha hira, Kausar harda kuka...

Shiru kakeji cikin ɗakin sai ƙaran gudun Ac, sun manne waje ɗaya abinsu, Kamal sai yawo yake da hannunsa jikinta yana shafarta a hankali. Cikin kasala da fitar haiyaci ta saki wani nishi mai ƙarfi ta riƙe hannun Kamal a shagwaɓe tace.
"Habibinna ka bari bacci zanyi karmu makara." hannunsa ya xura cikin rigarta, yana murza nipples ɗinta, ƙamƙameshi tayi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali cikin raɗa yace"Oya yi baccinki, ni ban shiryaba." ya faɗi yana haɗe bakinsu yana bata lafiyayyan kissing. Dole Mubina ta barshi yayi ta lagudata yana tsotsarta tana jinsa ta sakarmasa jiki har tayi bacci. Koda suka tashi sahur Kamal ya ciyar da ita sosai tana manne ajikinsa, shima yaci, haka sukacu sukasha, bai bari sun koma bacci sai bayan da sukayi sallar a suba, yanzu kwanciyar basu haɗe jikiba Kamal ya ƙiya, sanin yanda yake mugun jin feeling akan sweetien sa, Mubina dariya ma ya bata shiyasa ta share shi tayi kwanciyarta gefe, se bacci... Tom sai muce Allah ya mashi ibada...
Chapter 108 · 0% Book details