Sashe 13
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
maroon, akwai ta laushin fata jikinta lallausa ne tamkar tarwada idan tana juyin rawa ko tafiya, jikinta mai taushi ne haɗe da samtsi, Mubina ta kasance ma'abuciyar tsafta ce da son kamshi gata da son gayu akwai daukan dreesing kuma dole duk namiji me lafiya ya kalleta dan tayi ba karya, se dai sangartatar yarinya ce shagwaɓa ɓa dan Ablah ta kasa ta tsare bata son abinda zai ɓatama mubina rai, bare uwa uba umpah ga son jiki tamkar mage bata iya bacci se jikin mutum, Ablah ta ɓatata idan bata ƙasar dole take dawowa wajan Amrah, dole Amrah ta saba da hakan Mubina akwai son jiki gata irin wannan matan ne masu wata irin muguwar sha'awa abu kaɗan zai sakata cikin halin buƙatuwa shiyasa bata kallon duk wani abun da zai sata cikin wani yanayi dan yanzu zaka ga tana mimmiƙewa tana matsar ƙafafu tana hawaye, ko Mamu tasan da haka shiyasa kullum take cikin Addu'a Allah ya kare mata yarta a duk inda take. Se dai Mubina bata kulla samari asali ma har yau bata ba kowane saurayi fuska ba duk farin jininta dan har manyan al'hazawa harinta suke ansha tinkara umpah da neman auranta yace sam ƴarsa karatu take, se ya cika mata burinta na zama cika kiyar Ƴar jarida. Dole suka hakura dan basu sami shiga gun umpah bare Mubina da ko kallo basu isheta ba. Amrah ma maza basa gabanta sam ta maida hankalinta gun karatunta na bank. Ranar da su Mubina suka gama secondary school ranar suka fara shirin barin Naimey komawa maradi. Mamu dan murna harda kuka tayi dan bata taɓa sa ran haka ba, ashe ba yauba umpah an can ana tamfatsa masu gidaje har biyu a maradi an an gina katon company da hospital ashe katsina hospital tashi ce ya hana ne duniya ta sani. Ranar da suka dawo maradi da zama abin ya burge Mubina dan dama kullun tazo gidan kakaninta hutu kamar karta koma take ji, duk da daman a maradi zata zo tayi university ɗinta. Ashe ko umpah saboda Mubina ya gwamma ce gwara su koma can da zama bazai bar ƴarsa wani gari ba tana karatu gwara ya haɗa kansu ita da Amrah dan haka amrah na 300 leve mataki na 3 umpah ya gyara mata takardunta suka dawo maradi ta karasa a Maryam abacha university. Gidan ɗaya suka zauna wanda yaji kome na rayuwar duniya kafin a gama wancan babban gidan. Mamu dangi se sunturi suke Mubina kamar wasa ta kwarama wata me sunan kuluwa da mijinta lawali basu da aiki kullum suna hanyar gidan ƴarsu ta zumu Allah kyauta. To fa daga nan suka yi sanyi se gulmar Mubina suke wai balaraba batada aiki se wulaƙanta baƙar fata, dan balaraba dangin Mamu suke ce mata. Baffa inusa kakanta kuwa yace tayi dai dai shiyasa yafi santa kaf jikokinsa. Mubina ta shiga *Maryam Abacha American university of Niger* cikin sa'a dan sosai karatu take babu wasa tana karanta mass communcation. Yanzu Mubina na 100 level matakin farko a university, amma suna shirin jarabawa na shiga 200 level mataki na biyu wanda Amrah kuma tana dab da bankwana da makarantar dama matakin ƙarshe take gashi Lameer na damunta kan maganar auran su, duk da bata sonsa amma tana da niyar auransa, kawai ranar kamar a mafarki a fecebook taga wani me suna *KAK* ya turo mata invitation nan tayi confirmer ɗin sa, suke gaisawa se dai sam bata faɗa masa gaskiya ba tace ita ƴar dosso ce shiko ya faɗa mata yana maradi amman bai faɗa mata sunan sa ba ta haka ne har suka shaku. A kwananan. Kuma a wannan ɗan lokacin ne Kamal ya shigo makarantar Maryam Abacha wanda yake koyar dasu Mubina introduction too Business admin. Bayan an kammala gidansu na nan Ali ɗan tsoho an zuba masa uwar dukiya, suka baro can unguwar zaria1 suka dawo Ali ɗan tsoho haɗaɗiyar unguwa me kyan gaske ba ruwan wani da wani, barin ma ɓangaran su Mubina ta masu kudi ce zallah ba kamar sauran layin ba... Ablah bata gari ta tafi Algèrie anyi masu rashi tace se ta dan huta zata dawo. Kabeer ma yana nan tafe ya kammala karatunsa na engineering wannan shine cikaken tarihinsu Mubina, se kuma ku biyo ni jin waye Kamal a next page, kafin mu koma wasan......