← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 124

Sashe 17

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ɓangaran su umpah kuwa suna zuwa company suka taras Kamal baya nan, Abbu yace kawai su wuce police sitetion ɗin. Shine fa suka je, sukama Acp bayanin kome, nan ya haɗasu da ƴan sanda suka zo gida nan suka isko Mubina bata nan se Amrah da Mamu, umpah yake ma Mamu bayanin suna tare da ƴan sanda, nan Mamu ta bashi labarin yadda Basma ta faɗa mata. Mamu tace"Wlh kuma cewar tasha ruwan toilet karya ne irin nata , amma idan baka yarda ba kuje gidan su Basma tana can ta faɗa maka malamin , naji dai Basma tace kangiwa ne..."Nan umpah ya zaro idanu cike da mamaki!! yace" anya kuwa?" bari na kirata naji" nan ya kira number ta a kashe, ya kira wayarsa ta wajanta yaji tana amsa waya. Umpah yace"Tabbas kangiwa ɗayane maradi, Kamalu ne kenan? Tare fa muke yanzu da mahaifinsa Abubakar wannan makocin namu me kirki , amma yau da na tafka abin kunya Nusy abar maganar Baby kenan ashe lfy lau gashi ta fita yawo , bari na sallami yan sandar." ya faɗa yana juyawa. Amrah ta kyalkyale da dariya harda riƙe ciki tace "Wlh idan umpah na biya Baby se ta saka shi jin kunya."Mamu tace"hummm barshi ai tin farin maganar nasan karya take shi marinta dai da yayi har san hannunsa suka fito shine ilar amman ita taja..." Amrah ta miƙe tana dariya tace "bari na leƙa naga ya zaiyi da ƴan sandar." ta faɗa tana ficewa daga parlon.
Umpah kuwa sallamar Æ´an sandar yayi yama Abbu bayanin wai Kamalu nasu ne... Habawa ai kuwa Abbu yace se an kai sa police sitetion sunji dalilin da yasa yaci zalinta. Daket umpah ya ba Abbu hakuri ya hakura nan sukayi sallama da juna Abbu yace masa zuwa dare zasuyi magana me mahimmanci... Da haka de suka rabu umpah ya koma gida, Abbu ya shiga gida shima.

Samha ce zaune a parlo tana waya da Safiyya ƙanwar Abbu cewar hutu gatanan zuwa kebbi... Abbu ya shigo da sallama. Samha ta miƙe tana cewa"mamah ga Abbu ya shigo." ta ƙarasa tana faɗawa jikinsa ta kara masa wayar a kunnesa, ya fara magana"Ah Safiyya ya kebbi?" daga can tace"Yayana lafiya lau yasu goggon mu? Ga zakiyya na fa tafe tace nan zata haihu wlh ba yanda mijin baiba ta haihu nan sbd haihuwar farko ce amma tace niger zata zo gidan kawunta , Mamu ta bata kulawa." ta kai ƙarshen maganar tana dariya. Abbu yace"Gud Safiyya naji dadi sosai to mijin ya kawota da kansa saboda cikin yayi girma sosai ina Muhuseen da iyali? Dazu mun gaisa." Safiyya tace"rabona dashi shekaran jiya naje me sunan goggo ta fadi ta goce." Abbu yace "wh ai da sauƙi Allah bata lfy bari na shiga na ɗan huta." nan suka yi sallama ta kashe kiran. Ya kalli Samha yace"Ina ummah ki ne?" Samha ta saki Abbu tana dariya tace" Tana bacci fa tinda tayi sallah bari nima naje na huta , Abbu ina Yaya "Kamal ne? Ko ya tafi gidan goggo?" Abbu ya shafi kanta yace"Oho masa laifi yayi bari naje na sami mamarki muzanta , na masa mata yau zan nemi izini gun mahaifinta." ya faɗa yana haurawa saman bene. Samha tayi ihu da tsalle tana murna tace"mun kusa raƙashewa a she." ta faɗa tana nufar saman dan ta kwanta ta huta...

Basma ta jima kafin ta fito lokacin Mubina ta shanye frech milk tana gyangyaÉ—i har baccin ya kwasheta, momy ta gyara mata kwanciyarta ta rufa mata mayafinta tana dariya.
Basma ganin Mubina tayi bacci yasa ta kyaleta taje kan dining ta cika cikinta dam, ta ɗan fita kofar parlo tana leƙe taga garin ya fara duhu sosai akwai hadari, cikin farin ciki itama ta kwanta nan parlon sbd tana son ruwan sama sosai tace ma momy ta tasheta idan an fara ruwa... momy itama janye Sakina tayi suka shiga bedroom domin suma su ɗan taɓa barcin...

Kamal baccinsa yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana fitar da numfashi me cike da lafiya. Ameer ne ya murɗa kofar ɗakin, ya shigo da gudu yana ihu yana kiran Kamal"Uncle taso kaga garin an fara duhu kamar dare." ya faɗa yana hayewa saman gadon ya fadawa saman kan Kamal. Firgigit Kamal ya farka salati dauke a bakinsa, yace"Oh yaranan baku barin mutum ya kwanta bari ma na tafi gidan mu kawai." ya faɗa yana janye Ameer daga jikinsa ya sauko daga saman gadon, ya sanya takalminsa ya kwashi wayoyinsa ya zuba aljihu ba tare da ya kunna ba, yana yamutsa fuska sai lumlumshe tsumammun idanunsa yake, ya kama hannun Ameer suka fito. Goggo tace "amman Ameer anyi maras ji , ka tado yayan ka ai kuwa se na faɗama Hafsat." Kamal yace" tsofuwa na gudu se kin jini gobe ina mom Hafsat"? Goggo tace tana ciki wai bacci take , amman a wannan yanayin zaka fita ka bari har a lafa mana." Kamal ya galla mata harara yace "anki ɗin Abbu yanzu haka na nema na duk yasan ban wuce nan ko Company , na tafi se na dawo." ya faɗa yana sakin hannun Ameer ya rankwafa yama goggo kiss ya miƙe yana murmushi ya fice. Ameer ze bishi goggo tace"Maza dawo kasan halin gambo nemi gu zauna idan ta tashi zata kai ka..." Ameer ya dawo ya zauna. Kamal yana fita ya shiga motarsa yaja ya fice daga gidan, a guje saboda yanayin garin...

Mubina baccin ta take me mahaukacin dadi se wani mimmiƙewa take tana ɓaƙaro kirjinta, ai kuwa se gata ta fado daga saman kujera dimm. A firgice ta buɗe manyan idanunta ta zumburo baki gaba tana riƙe ƙugunta tace"Woshhhh bayana Ashhhh naji zafi ya ma akayi na fado? tirrr." ta faɗa tana kallon Basma tana sharara bacci. Tsaki taja ta miƙe tana riƙe da kugunta ta ɗauki wayarta tayi kan Basma ta ɗaga hannunta zata shirga mata ƙulli ko me ta tuna ta fasa, ta saka takalminta ta yane kanta da ɗan gyalan Abayarta ta fice tana yamutsa fuska. Tana fitowa ta zaro idanu ganin garin yayi duhu sosai kamar dare, ga iska kaɗan-kaɗan, har an fara yaiyafi. Da ɗan saurinta ta fara tafiya tana sakin murmushi tace"Wow dama na taso Basma mun tafi gidan Baffa inusa ruwa ya bamu kashi a hanya ina son ruwa sosai , se dai duhun yayi yawa bari nayi sauri na samu adaidaita sahu." ta faɗa tana isowa bakin get ta bude kofar ƙarama ta fice..........

_*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*_
_*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*_
*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Free Page*

🅿️1️⃣3️⃣
Chapter 17 · 0% Book details