← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 124

Sashe 86

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iyamu a baje tsakar gida sai waya take da iyayanta tana basu labarin gobe saurayinta zasuzo da iyayansa neman auranta, daga kebbi. Sallamar da taji ne yasa ta miƙe tana shiga, ɗaki ta dauko mayafi. Leezah da take zaune tace"ya kuma dawowa ko?" iyamu tace.
"Anya bari dai na gani."ta faɗi tana fita. Leezah ta saka ɗan guntin hijabi iya kafaɗarta tace"bari muga waye?" ta faɗi tana ficewa. Iyamu tana buɗe kofar gidan tayi idanu hudu da yan sanda, harda ibrahim atsaye, tace"Angona lafiya....?" bai bari ta ƙarasa ya sauke mata kyawawan maruka biyu yace.
"Ubanki dai ba angonki ba ni ɗan mahaukaciya ne da zan auri karuwa irinki? Na rasa abinda zan kwasa sai annoba." Iyamu wata irin zufa jikinta yake tsatsafowa. ACP Sahabi ne yace"kece Iyamu ko kece Leeza?" iyamu jikinta ya ɗauki ɓari dalilin gigitattun marin da tasha, cike da tsoro tace"Nice iyamu." daidai lokacin Leeza ta iso, ganin ƴan sanda yasa zata juya da gudu, Sahabi yace.
"Wlh kina matsawa zan harbeki a ƙafa, maza ku shiga mota."Rushewa sukayi da kuka a tare suna faɗin.
"Me muka maku?' ibrahim yace"Uwayanku kukayi shegu ɓata gari."Abbu da Umpah suka jinjina kai dan sosai ma sukaga ƙaramtarsu a waje, dan da kaɗan sukafi Mubina da Samha. Tisa keyarsu akayi har cikin mota. Direct daga nan kamfanin su Mounkaila suka nufa.
Can kuwa hospital an daga wajan ceto rayukan Yahanasu da Jamila saboda an shugesu ta karfin tsiya, ba ya jamila, dan É—inki biyar aka mata Yahanasu É—inki hudu, amman dake Allah mai yanda yaso jamilar ta mutu, amman sam likitocin sun gaza faÉ—ama Tukur ganin irin kukan da suke. Mounkaila hospital É—aya akayi katari sukazo room É—inma a jere. Mounkaila yace.
"Tukur wannan wace irin musiba ce muka faɗa an ɓata mana yara biyu lkc ɗaya kuma duka fyade ba yama Jamila ƴar malekiyar Allah..." Direban Mounkaila ne ya iso bakin kofar room ɗin, cike da tausayinsu duba da yanda matansu suke kuka suma sunayi ga wani mugun labarin da yazo masu dashi, cikin dauriya yace.
"Alhaji kamfani babu lafiya fa ga baki ɗaya ya kama da wuta, yanzu manager ya ƙirani fa...."Ihuuuu suka saki a tare suna faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! A gigice Mounkaila yace"kudinmu Tukur muyi ƙoƙarin ceto kuɗinmu..." a guje sukayi waje suna ihuu jama'ar da ke cikin compound ɗin hospital ɗin sai kallonsu suke. Dakyar direban ya kwantar masu da hankali yace.
Muje an a dana kuÉ—in." shiko ina ya sani wayone ya masu, ya samu suka shiga mota yaja suka nufi kamfanin.

Suna zuwa gurin yana cike da mutane wuta naci gadan²ga dandanzon jama'a ga ƴan kwana²sunzu suna famar yanda zasu samu ta lafa. A guje suke ƙoƙarin shiga ciki suna ihu suna cewa"Dukiyarmu millions sittin kadarorinmu sunka million ɗari a ciki..." Riƙesu ake ana basu baki. Su Umpah da ƴan sandar suna gefe, ga baki ɗaya Umpah yayi sanyi da lamarin ganin yanda baki ɗaya kamfani guda yaƙone ƙurmus haka gashi yaji wasu suna faɗin anyima ƴaƴansu fyade. Abbu yace da Sahabi.
Acp a kamasu mana me ake jira tinda sunzo?" Umpah baiyi magana ba, amman shi kansa yana son a kamasu É—in.
Acp yace da sauran Æ´an sandar"Ku kamosu ku saka masu ankwa..." Umpah yace"Please ku barsu kawai." kuma da ya tuno irin wuyar da Mubina taci kawai sai yace.
"ku sa masu ankwa muje kawai." Nan take aka kamasu suna ɓori gaban jama'a aka sasu a mota aka wuce dasu police stetion... Jama'ar gurin sai mamaki suke wannan wasu irin mutanene suna kallonsu cikin wannan ƙuncin suka iya kamasu.? Wanda suka san mugayen halaiyarsu kuwa basuji haushin ƴan sandar ba.

Suna zuwa police stetion ɗin aka fito dasu, Mounkaila sai kuka yake yana cewa"Don Allah ku mana afuwa ko me muka maku kubari muji da rashin lafiyar yaranmu ga dukiyar mu duka ta ƙone." babu wanda ya saurareshi aka shigar dasu ɗakin duhu, su iyamu sai kuka suke harda majina, nan Acp yace a koyama su iyamu hankali. Ai kuwa sunci uban duka babu wasa, da farko da aka tambayesu me yasa suka haɗa Kamal da Mubina suka aikata zina? Gardama sukayi, saida jikinsu ya gaya masu, dan ba ƙaramin duka sukaci ba hannun Safina. Su Mounkaila kuwa Acp da kansa ya musu tambaya kai tsaye suka amsa suna kuka da roƙon a barsu su koma gun ɗiyansu da dukiyarsu. Umpah kuwa bayan an shigar dasu yace da Abbu suje hospital suga halin da ƴaƴan su Tukur suke ciki, Abbu bai musaba, yasaka Acp ya tambayo masu sunan hospital ɗin wajansu Tukur, nan yasa ibrahim ya kaisu. Abinda suka iske ya ɗaga masu hankali dan ɗiyar Tukur ta mutu ga ɗiyar Mounkaila itako ko ta warke zaiyi wuya ta zama normal....
Umpah yace da Abbu"Please mubar wannan shari'a ɗin kalli tin yanzu suna ganin hisabi ƴarsa ta mutu ta hanyar fyade dukiyarsu ƙurmus ta ƙone, shima wannan ƴar tasa an mata fyade kafin ta dawo daidai sai Allah kawai mu janye ƙaran nan sudai matan a ɗan hora mana dasu har sai sunyi nadamar gaske a barsu nan police stetion ɗin, kar muje kotu wlh wannan abin kawai ya ishesu..."Abbu ya jinjina kai, sanin daman ba wai ansan abinda ya faru da yaran nasu bane sai yasu yasu sai kuma yanzu gun ƴan sanda suko ba wai zasu faɗama kowa ba.!!
Abbu yace"Ok babu kome amman mu tara family ɗinmu kowa yaga vedion sai a goge itama a tura mata ta gani."Umpah yace"Ok hakan za'ayi wlh idan mutum ya cuceka kabar ma Allah yafi kome kaga ba'aje ko inaba ga yanda suka zama to ƙaran me zamu shigar kowa yazo yasan meke faruwa." ya faɗi yana ƙiran number Acp. Bugu ɗaya ya ɗaga yace
"Please a sako su suzo suji da iyalansu yanzu haka É—ayan Æ´arsa ta mutm sai uban yazo za'a bada gawar harda Æ´an sanda, fa gashi sun rasa dukiyarsu. Haba zaman duniya ba na lahiraba wlh sunga ishara, kuma nasan duk alhakin Æ´aÆ´anmu ne a sakosu mun yafe masu Allah ya shiryesu, suko matan su zauna ku É—an gana masu azabar da sai sunyi nadama ta gaskiya."daga can Acp Sahabi ya amsa da.
"Ok an gama." Umpah ya tsinke ƙiran suka fito wajan mota, Ibrahim na mamakin samun mutum kamar umpah adali zaiyi wuya ayanzu. Jansu ibrahim yay yana cewa.
"Ina muku nufa?" Abbu yace muje can police stetion mu amshi camera..."Umpah yace"Bakaji nacema da Sahiba ya amso camera É—in wajan D.P.O ya kawo mana yanzu gida mun janye." Abbu yace.
"Ok bari ma na ƙira D.P.O na faɗa masa da kaina mun janye."Umpah ya jinjina kai yace"Gud Abubakar naji daɗin yanda da fahimceni." Abbu nan ya ƙira D.P.O ya faɗa masa sun janye ƙaran abar maganar yaba Sahabi camera ɗin ya kawo masu yanzu gida. Nan ya jinjina kansa ya amsa, dan yasan Abbu sosai suna harakar business, mutumne mai ƙirki. Nan kafinma Sahabin yazo ya ƙirasa ya bashi camera ya kai masu, sanin Sahabi mutum ne mai nagarta. Kai tsaye gida ibrahim ya kaisu lokacin ana ƙiran sallar magarib. Kuma lkcn Sahabi ya kawo camera ya juya bayan sun jadadda masa a ba ƴan matan wuya irinta horo mai tsanani. Gidan Abbu suka shiga sukayi alwalla suka nufi masallaci. Can ciki kuwa Hafsat da Goggo da Sumaiyya sun jima da zauwa suna zaman jiran ibrahim da Abbu.

Ɓangaran su Mounkaila kuwa bayan azabar da Sahabi yasaka akamasu shima ya masu da kansa, ya sallamesu ajigace suka tafi. Bayan sunzo ne Dr ya faɗama Tukur mutuwar ƴarsa, wani irin kuka yake me haɗe da nadamar rayuwarsu da suke ga babu dukiya ta ƙone. Mounkaila kuwa bayan sunzo hospital Kamfani ya koma ya iske ƙurmus kome sai abinda ba arasa, ya tambaya ko an adana masu kuɗinsu? Kowa yace wa zai shiga wuta.... Nan ya faɗi sumamme, aka kwasa akayi hospital. Tukur kuwa tashin hankali ya masa yawa baya ta dukiya yafi jin mutuwar ƴarsa, a lkcn aka basu gawar ƴarsu bayan an gyarata, yana kuka ya ƙira ƴan uwansa a kaje aka mata sallah aka kaita gidanta na gaskiya, yaƙi yarda sai gobe, ana magarib aka binneta. Mahaifiyarta kamar tayi hauka. Kafin kace kwabo garin maradi ya cika da labarin gobarar kamfanin su Miunkaila ya ƙone ƙurmus, da fyaden da akayi ƴaƴansu, har ɗaya ta rasu. Wasu su jajanta wanda suka san halinsu suce calama....
Chapter 86 · 0% Book details