← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 124

Sashe 100

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummah suna zaune a parlo ita da Abbu wanda yake shirin fita, Ibrahim ne ya shigo yana waya sai dariya yake yana cewa.
"Ai gani na shigo ma." ya faɗi yana zama kusan Abbu, ya beƙama Abbu wayar, ya kalleshi yace"Kai dawaye?" Ya faɗi yana karawa a kunnensa.
Kamal daga can yayi dariya yace" Abbuna mai sona ɗankane Kamal, good morning my Abbuna." Ummah tayi dariya tace" Waye ka kawo mana?" Ibrahim yace"Kamaluddin ne, yarona sai da ya cafke matar sa a hannun yasan inda nake yau ya kwaɗamin ƙira, anyi katari ina hanya, Abbu yace nazo muje police station gun yarancan marasa kamun kai, shine naca gani kan hanyar zauwa gidanku." Ummah tayi dariya tace.
"Ai nima kuwa tin ɗazu ya ƙirani munsha hira, ɗan albarka, gobe zai wuce saudiya, da matarsa. Kamal daga can yace"Yauwa Ummata i love u so much, Abbun kamin magana mana." Abbu murmushi yayi yace"Ni wato bazaka ƙirani ba sai anbani a maƙwabta ko? Humm ka kyauta ango." Kamal dariya yayi, yace"Abbuna ina rabin raina Samha ko bata zoba?" Abbu yace"Eh tana gidan Goggo..." Wayar Abbun ce ta ɗauki ringing yaba ibrahim wayar yace"Kai da ɗanka ku ƙarata." wayar ya ɗaga ganin Umpah ne yace"Har ka fito ko?" kome Umpah yace, Abbu yace"Ok gamunan da ibrahim na iyamu." Abbu ya katse ƙiran yana dariya. Ummah dariya take tace"Ai kam ka cika mata alƙawalinta." Ibrahim yace"Muje dan Allah wannan matar bakya kishin mijinki ko?" Dariya Abbu yayi, yama Ummah sallama suka tafi. Ummah ta miƙe fuskarta cike da walwala ta haye sama ta rumtsa....

Umpah suna zaune A parlo Ablah tace"Kawai a turasu gidan maza Æ´an banza yara su horu da kyau. Mamu tace.
"Allah dai ya kyauta ai Ablah aikin gama ya gama suje kawai zasuga sakaiyya a gaba." Umpah ya miƙe yana ba Mamu cup ɗin shayin da yasha yace"Tom na fita sai na dawo Amrah baccin ne ko? Na leƙa naji jikin ba zazzaɓi." Mamu tace"Eh Allah tsare sai ka dawo." Ablah baki ta riƙe tana dariya, tace"Abdul a dawo lafiya." Mamu kunya taji ta nufi kitchen tana murmushi tace.
Bari nazo na ƙira autata."Ablah tace"Nusaiba zo ɗaukomin dabino na tauna." To" tace ta ida shige kitchen...

Umpah na fitowa Haladu jashi a mota, su Abbu na mota haka suka jera zuwa police station ɗin. Suna zuwa ba jimawa a ka fito dasu. Iyamu anyi baki an rame jiki duk taɓon bugu, haka Leezah. Gaban Abbu da Umpah suka zube suna rusar kuka suna cewa"Don Allah karku kaimu kotu mun tuba wlh bazamu sake ba mun tuba ƙasar ma zamu bari mu koma gida, daman ba ilimi ne damuba, munsa iyayanmu asara, wlh mun tuba mun koma ga Allah, zamu nemi gafarar su Mubina."Iyamu tace"Wlh na tuba ko ɗan faskare gwara naje na aura, yafimin a kaini gidan yari..."Ibrahim yace.
"Dallah can munafuka, shi ɗan faskaran uwayansa baki suka masa ne...?" Abbu yace "No ba hakaba, ayi haƙuri naga nadama ƙarara a fuskarsu, kuma bama haka ba, suci gaba mana duniyace fa, ba sunga yanda Allah yayi da su Alhaji Tukur ba, sukuma yaran da kuka haɗa masu makircin sun zama ma'aurata masoya na gaskiya, suna can london sai abinda sukeso zasu yi, sai ƙasar da sukaga dama zasu suyi rayuwar auransu bazamu hanasu ba..."Nan Umpah da Abbu suka saka hannu sun janye ƙaran aka sakesu, takalmansu a hannu suka fice daga police station ɗin, ibrahim sai dariya yake, Abbu ya kai masa bugun wasa. Ai fa Iyamu suna zuwa gida suka shiga haɗa kayan barin gari...🤣

Kwance yake a parlo saman kujera bacci ya fara ɗaukanshi, aka fara knocking ɗin kofar, a hankali ya buɗe idanunsa, da suka fara canza launi ya miƙe yana ɗaukar wayarshi, yaga 12:00 idanu Kamal ya zaro yace.
"Ya salam nayi bacci sosai Sweetienah bata tashi ba tin breakfast?" ya faɗi yana nufar kofar ya buɗema Makel, ya shigo ya bashi hannu suka gaisa. Kujera Makel ya zauna Kamal ya shiga ciki. Kwance take tana baccinta cikin nutsuwa. Bakin gadon ya iso ya rankwafo ya sayan hannunsa ya ɗauketa cak yana ƙiranta.
"Sweetie buɗe idanunki."A hankali na buɗe idanuna na kalleshi, lumshe idanuwana nayi, muryata can ƙasa nace"Kamal zansha ruwa kuma ka kaini gida kaji."murmushi ya sakarmin me ratsa zuciya yace"Ok Sanyin idaniyata, bari na shiryaki Makel na jiranmu zamu kaiki gida, ki shiyar kayanki ai zaki bini saudiya muyi azumi acan da an gama sai na dawo dake kiyi karatunki uhm Sweetie...?"kallonsa nayi ina turo baki nace"To Kamal har wata amman baza sake min kome bako?"na faɗi cikin sangarta da son yin kuka, ina ɓoye kaina a ƙirjinshi. Lallaɓani yayi tayi yace bazai min komeba har mudawo ko hannuna bazai taɓa ba, haka ya shiryani cikin wata ɗoguwar riga maroon mai shegen kyau ba tare da ya taɓamin kome na jikina ba, ya samin takalmi ma sabo, sakamin ƙaton hijabin, ya kamo hannuna muka fito parlo. Gaisawa mukayi da Makel, nan ya zaunar dani ya bani cake naci nasha yoghourt ya kunna wayata ya bani muka fito ya rufe kofar. Ina seat ɗin baya suna gaba muka nufi gida.
Makel na tsayawa na buɗe motar na fito Kamal ya fito, na shagwaɓe fuska nace"Ka tafi to kar ummi ta gane tare muke."Murmushi yayi yace"Ok Sweetie shiga ciki sai na tafi..." ban bari ya ƙarasa ba na fara tafiya wacce ba dai dai ba ce. Ban waiwayo ba naji yace" I love u sweetie Mubee."Kafaɗa na maƙale naki waiwaye har na buɗe gate na shige. Kamal motar ya shiga suka tafi suna hirasu.
Da sallama na shigo parlon, da ummi muka haɗa idanu, na ƙaraso na faɗa jikinta ina dariya, nace"Ummi barka da rana ina papa?" Ummi tayi dariya tace"Ai ya fita ya amarcin?" kunya ta luluɓeni na miƙe ina gunguni nace"Yo ummi ni ina nasani yanzu fa mijin auntyn Kausar ya kawoni tace a gaisheki."na faɗi ina saurin shigewa bedroom. Ummi dariya tayi ta miƙe ta nufi kitchen...

Karfe biyar na yamma papa Saleem ya amso takardun Mubina na makaranta, a gunta ya amshi number Kamal ya ƙirashi, karfe shida Kamal yazo ya amshi takardun, Mubina kamar da ɗaya duniya bata taɓa sanin saba, a falon sabgarsu suke itada Kausar dasu Azeema haka ya ƙari hirashi da papa da ummi saida aka ƙira magarib ya masu sallama ya tafi. Mubina ko rakiya... Da dare kuwa Mubina ta ƙira su Umpah da mamu su Amrah da Kabeer wanda dirowarsa kenan garin, sukasha hira, Kamal da ya ƙirata yace ta shiyar fa gobe zasu tafi, bata musaba ta shirya kome nata tsaf, a haka tayi bacci suna waya, saukar numfashinta yasa ya kashe ƙiran daga can.
Washegari misalin karfe tara na dare Kamal yazo ɗaukar Mubina dakyar ta rabu dasu ummi da Kausar sai rizgar kuka take, ummin ma harda ƙwalla nan tace ma Kamal ta bashi amanar Mubina, yace ya amsa.
Majeed ma ya saki ranshi shida papa Saleem suka rakasu har Airport. Acan Kamal ya ƙira Abbu ya masu sallama yaba Mubina ma dakyar ta amsa sai fushi take. Ya ƙira Umpah ma yaba Mubina duk tayi waya da ƴan gidansu, Kamal yama makel alheri sosai wanda baxai manta dashi ba, Makel harda kukansa na rabuwa da Kamal. Suna gurin sunce sai jirgin ya tashi zasu tafi, Aleem da Azeema sunsha kuka a Airport seda Majeed ya zare masu. Karfe shabiyun dare jirginsu Mubina ya fara shirin tashi, sosai Kamal yayi murna ba'aga wata ba yau kenan sai gobe suna saudiya sun huta zasu ɗauki azumi. Kamal ya ƙira kawunsa jirginsu zai taso yanzu, sosai yayi murna aka shiga gyara kayan tarbar baƙi nagobe da safe, Umaimah kamar janyo jirgin takeji dan murna sai kyale kyale take....

Mubina jin jirgin Ya fara alamun cirawa ta fara ƙamƙame jikinta. Kamal ya sake manneta ƙirjinshi yake ya luluɓeta ruf da towel ɗin jirgin yana shafa bayanta yace"Sweetie nah bacci ko?" kai ta ɗaga masa. Ta ƙirasa"Kamal" Kanshi ya sayo cikin towel ɗin ya haɗe face ɗinsu yace.
"Baby sweetie menene? ga Kamal ɗinki kusa dake kinji."ya faɗi yana shafa bayanta zuwa fuskarta yana hura mata iskar bakinsa. Lamo tayi cikin ƙirjinshi, har jirginsu ya ɗaga ya fara tafiya har ya keta hazo ya shige gajimare. Mubina sai bacci... Tom Allah ya saukeku lafiya....!

Sweet Ladingo Timint Welday ce🤍😘

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣

Karfe 6 dai² jirginsu Kamal ya dira ƙasa mai tsarki. Mubina tin ɗan baccin farin da tayi bai fi na 1 hour ba, ta farka bata sake bacci ba.
Kanta saman kafaɗar Kamal tana riƙe da hannunsa ɗaya ta zubama jansin mutanen iri² dake ta ficewa a cikin jirgin idanunta, kasancewar a tsakiyar kujeru suke.
Saida mutane suka rage sosai Kamal ya miƙar da ita ya saka mata niqab, ya kama hannunta suka bi jerin yan baya.
Su kawu Jafar da Anwar da Umaimah tin 4 suke Airport ɗin zaune, suna juransu. Anutse yana saƙale da hannunta cikin nashi suke taka matataƙar jirgin, har suka sauko. Mubina ta ƙara riƙe hannun Kamal tace.
"Wow brother Kamal wallahi tin airport Saudiya ta haɗu sosai zaka kaini Kabah ɗakin Allah ka kaini madina garin manzu nayi ziyara ko Yayana?" ta faɗi a shagwaɓe. Kamal a hankali yace"Ke waye yayan naki kunji Sweetie da wayo." ya faɗi yana murmushi. Hannunta ta fizge tana turo baki ta cikin niqab ɗin.
Bayan sun gama duk abinda ya kamata, sukaje gun kayansu trolley biyu ne nashi da nata wanda suke shaƙe da kaya, cikin abin tura kaya ya saka yana turawa Mubina gefensa, suka nufi gun da ake tarbar baƙi.
Chapter 100 · 0% Book details