← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 124

Sashe 109

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

************** ******* **************
Yau kwanansu Kamal 7 a Madina, hakan yayi dai_dai da azumi 7 sbida yini, Kamal ya kai Mubina tayi ziyara kabarin Ma'aiki, ya kaita masallacin madina, ba laifi yayi yawo da ita sosai a cikin garin Madina tare da su Kawu suke fita, har yanzu dai Mubina taki yarda Kamal ya kusanceta tace sai bayan sallah da zaran ya fara romance nata zata kafa masa kuka wai dan ya gusar mata hankaline, se ya barta daman ba lokaci ya maida hankainsa bautar ubangiji dan ita ya saka A gaba baya bacci tinda watan ramadan ɗin ya kama, sai yayi sallar asuba. Umaiamh kuwa dan taba Mubina haushi sai tayi ta abubuwa wa Kamal amman Mubina ta mayar da ita shara, dan ta gama da ita, tinda tasan mijinta baya sonta, wani ikon Allah ciwonta sam ya kasa tashi ranar har na ƙarya tayi, Kawune ya ganota yaci mata mutunci yace ba ruwansa tinda har ciwon ƙarya take, shine jikinta yayi sanyi, amman ita har yanzu bata cire ran samun Kamal ba...... Sun gama duk shirinsu zasu ɗaga Makkah yau Anwar ne zai kaisu.
Su Iyamu da Leezah an warke saidai rayuwa babu daɗi abin tausayi sunyi nadama sosai bata wasaba tinda watan ramadan ya kama ibada suke tare da neman gafarar ubangiji. Mounkaila da Tukur ba sauƙi ana cikin halin fatara, ga Mounkaila ba lafiya asibiti sun salamesa ga ba gida dole kangon sa me ɗaki ɗaya suka tare, babu wuta babu ruwa, Tukur yace su dawo gidansa haka suka dawo ana jinyar Mounkaila da maganin gargajiya...🤣
Misalin karfe 10 am, zaune take cikin shirin tafiya abayarta mai masifar kyau waya suke da Mamu da Umpah dan itace ta tashesu a bacci. Kamal ya fito cikin shirin tafiya yana janye trolley ya fita ya sake dawowa ya janyo wata trolley ɗin jibgegiya, ya fita ya dawo ya shiga bedroom ya ɗauko mata jakarta ya iso ya zauna dab da ita, ya ƙura mata ido sai zuba surutu take. Tana tsinke ƙiran ta kalleshi tana turo baki, tace.
"Allah ni bana son kallo." Murmushi ya sakar mata ya shafi sajan fuskarsa, yace"An kalleki ɗin bakina kallon ai, marowaciya ki jiƙa kisha." baki ta ɓara zata saka masa kuka tana langwaɓar da kai ya matso dab da ita amman bai taɓa taba yace"Sorry Sweetie riƙe abunki bana so nima." Oya sa niqab mu tafi." Baki ta kuma turowa ta matsa daga kusansa, tace"Naƙi sakamin." ɗan gunti smile ya saki ya matso ya saka mata niqab ɗin ya kama hannunta ta miƙe ya bata jakarta, yace"Oya" Kallonsa tayi tana murmushi tace"Habibina kayi kyau sosai wollah." hannu ta ya kama suka fito. Anwar ya gama saka kayan a mota. Cikin parlon suka shigo da sallama.
Kawu Jafar ya amsa yana miƙewa yace"Ɗiyata sai kwanan makkah ko?" kanta Mubina ta sadda tace"Kawu ina kwana ummu ina kwana." a tare suka amsa mata, Yumnah tace"To kuyi ta haƙuri da junanku Allah ya maku albarka." suka amsa da "Amin" Kawuma faɗan ya masu sosai da nasiya. Umaimah kuwa bacci take bata san wainar da ake toyawa ba, Mubina tace"Ummu ina Uamimah muyi sallama?" Yumna tace"Ai bacci suke da Raihana se sun tashi suga kun tafi."Mubina tace"Naso zuwa wajan Nafisa akwaita ƙirki." dariya sukayi baki ɗayansu.
Kawu yace"kafin ku koma niger ai zaku dawo insha Allah Anwar zai kaiki." Haka suka rakosu har gun mota, sunata masu Addu'ar sauka lfy, Anwar yaja motar ya fice daga kofar gidan.
Mubina tana seat É—in baya tayi kwanciyarta, Kamal na gefen Anwar suna hira, haka suka É—auki hanyar Makkah.

A niger kuwa
Chapter 109 · 0% Book details