Sashe 54
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamu ta ƙurama Mubina idanu tana kallon yadda yarinyar take wani uban fari da kyau da ƴar ƙiba. Mamu ta janye hijabin Mubina, tana kare mata kallo gabanta na wani irin mahaukacin bugo da karfin gaske, cikin tashin hankali tace ma Mubina "Baby me kike ji na damunki? Yause rabonki da da al'ada?" Mubina ta tunzuro baki gaba tace " Mamu ni bana son ko wane ƙamshi se wancan na jikin rigar, se jarabar yawu tin jiya da ya addabeni se zazzaɓi da tashin zuciya ke damuna, ni tinda wannan azalumin ya zalumceni banyi peroad ba ,ni de Mamu bana son magani zan warke."ta faɗa tana shigewa jikin Mamu ɗin tana ririƙeta.
Mamu da tayi mutuwar tsaye jikinta ya ɗauki rawa, nan take taji guntun fitsari na neman zubo mata, ga wata uwar zufa da take keto mata. Tayi saurin janye Mubina daga jikinta, ta janye hijabin ta dora hannu saman cikinta tayi ƙasan marata ta ɗan danna Mubina ta zabura ta ruƙunƙume Mamu ta saki ɗan ihu.
Mamu tace" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Allahumma Ajirni fi musibatin wa'akilli khairan Minha!" Na shiga uku ni Nusaibah." Mamu ta faÉ—a tana fashewa da kuka tana cewa"Ya Allah kabamu ikon cinye wannan jabawa da kake mana, Allah ka dubemu ni da É—iyata ka tausaya mata."ta faÉ—a tana kecewa da wani irin kuka, ta rungume Mubina gam.
Mubina cikin kidima da mugun tsoro!! Ganin Mamu na kuka, yasa ta fashe da kuka tana cewa"Mamu me na miki to meye ya sameni Mamu...?" Su Umpah ne shida Amrah suka shigo da sallama. Ganin Mamu da Mubina cikin wannan tashin hankalin, yasa Umpah ya ƙara sowa da gudu a mugun rikice! yana cewa"Nusaiba me ya faru kuke kuka?"Amrah tayi jifa da ledar agwalima ɗin ta kece da kuka ta rungume su Mamu ɗun tana cewa"Mamu me ya sami Mubina ɗin...?" Mamu ta kasa magana kuka kawai take.
Mubina ta saki Mamu ta rike Umpah tace"Umpah ko mutuwa zanyi dai? me ya sameni Mamu take cewa Allah ya dubeni ya jiƙaina...?" ta faɗa tana wani irin kuka wanda take wani irin amai yazo mata tana ƙoƙarin sunkuyawa Umpah ya riƙota suka yi toilet amman ina nan ta fara kelaya aman kamar zata amaye hanjin cikinta, Umpah ya riƙeta yana mata sannu yana buga bayanta. Amrah ta kamata suka shiga toilet tana kuka ta wanke mata bakinta, suka fito. Mubina ta faɗa jikin umpah tana maida numfashi jikinta ya dauki wani irin zafi sai karkawa take hakoran ta suna gamewa.
Umpah rungumeta ya cire mata hijabin, yace"Nusaiba dauko wani a samata." Mamu ta dauko hijabin ta saka mata. Mubina sai rawar sanyi take ta ruƙumƙume Mamu. Umpah yace "Wai meke faruwa ne...?"Wayar Mubina ce ta ɗauki ringing, Mamu tayi saurin ɗauka tana ga Sageer ne tayi picking ta kara a kunnenta, ta danne kukanta tace"Sageer pls mun yarda dakai dari bisa dari dan haka bisa Amana zamu zo yanzu ka kaimu hospital ka duba mana Mubina."Bata bari yayi mgn ba ta tsinke kiran.
Umpah yace"meke faruwa ne?"Mamu tace"Abban Mubina masifa bata kare mana ba, jarabawar Allah nada yawa kaddara Mubina mummunar kaddara ce Allah yabamu ikon cinyewa, duk yadda mutum yaso ɓuye abinda Allah yaso fito dashi to babu shakka se Allah ya cika alkawalinsa, yayi yanda yake so, da bayinsa domin ya sake gwada imanin su, mun ɓuye fyade ga babban fyade zai baiyana, muje hospital a duba mana ita."ta karasa mgnr cikin kuka ta kama Mubina suka nufi kofar fita. Umpah cikin tashin hankali yace"Wani ciwon ya goga mata ko zargi ne kawai kike ne.?"
Mamu bata sake mgn ba tana riƙe da hannun Mubina suka sauko. Umpah da Amrah suna biye dasu. Suna sauka Mamu ta ɗauko hijab ta saka, Ablah tace"Nusy lfy kuwa?" Mamu tace"Baby ke zazzaɓi zamu likita mu dawo, Amrah zauna gun Ablah bari mu dawo." Ablah tace"Baby sannu Allah ya baki lfy, tin faruwar abin nan bakida cikakiyar lfy." Amrah ta share hawayenta ta ɗaga kai. Mamu tace"Ablah kiyi hkr zata warke idan mun beƙa lamarin mu wajan Allah mun sake amsar kaddara." ta faɗa tana goge kwalla a ɓoye. Umpah ya kama hannu Mubina da yake hannun Mamu yace"Muje gabana faɗuwa yake Allah kasa yarinyar nan na cikin koshin lfy Amin." ya faɗa yana jan Mubina Mamu tabi bayansu tana share hawaye. Mubina binsu kawai take tana jin mahaukacin faɗuwar gaba. Ablah tace" Amrah me ke faruwa ne wai?' Amrah ta rungume Ablah tace"Nima ina cikin duhu, ban saniba." Ablah tace"Allah ya kawo su lfy Allah yasa ba zargina bane zai tabbata." ta faɗa tana rafka tagumi. Amrah shiru tayi tana jin matsaneciyar faɗuwar gaba dan ta gano suna nufin Mubina nada ciki ko me...? Kuka ta fashe dashi tana rungume Ablah. Ablah se lallashinta take.
Anan farfajiyar gidan Sageer ya shigo da motar tin lkcn da Mamu ta faÉ—a masa zasu hospital. Suna fitowa Sageer ya tare su yana gaishe su, amman ganin yanayin su yasa gaban sa faÉ—uwa. Umpah ya nufi rumfar motoci zai É—auko mota, Sageer ya bishi yace"Umpah tinda gaggawa ake muje kawai a motata mana a duba lafiyar ta." Umpah baice kome ba ya juya yabi bayan Sageer ya buÉ—e masa gidan gaba su Mamu suka zauna a seat É—in baya. Yaja motar yanufi get yana horn, megadi ya wamgame masa get ya sulala motar waje.
Mubina kuwa jikin Mamu ta lafe tana maida numfashi muryata can ƙasa tace"Mamu nah me ya same ni Mamu zan zubar da yawu." Mamu ta fashe da kuka ta buɗe glass ɗin motar ta ɗago Mubina ta riƙe kanta sosai yadda zataj i dadin zubar da yawun, ta zubar ta maidata jikinta ta kwanta ta rufe glass ɗin ta rungume Mubina gam, tana jinjina kai tana kuka. Umpah yace"Don Allah Nusaiba kar ki tarwatsamin zuciyata pls, ni bansan me ke damun yarinyar nan ba kin ki faɗa kin kwasomu mun taho kina kuka ita nayi wanne zanji aciki." ya faɗa cikin wani irin yanayi. Mamu tayi shiru tace"Kayi hkr na kyale na barwa Allah ikon sa..." Bata sake mgn ba har suka iso hospital ɗin.
Bayan sun shiga ciki Sageer yace"Mummy akan wani ciwo ne za'ayi binci ken?" Mamu tace"Akan ciki ne..." Dukan su sai da suka girgiza, Umpah ya rufeta da masifa yana cewa"Aniyarki ta biki Nusaiba wane irin ciki kuma?" Mubina ta shiga ja da baya tana girgiza kai ta kece da kuka. Mamu ta kamata tace"Ba lallai shi bane gwaji za'ayi Sageer ku shiga." ta faÉ—a tana bashi hannun Mubina ya kama suka shiga room É—in da zai mata gwajin tana kuka. Umpah nan ya daskare kamar gumki baya ko kwakwaran motsi, duk Addu'ar da tazo bakinsa azuciyar sa yi yake.
Sageer suna shiga ya kurama Mubina idanu ya kama hannunta yana kallon tafin hannunta, ya gwala idanunta, nan gabansa ya faɗi. A gurguje ya ɗauki jininta ya bata ƴar roba taje tayi fitsari ya zaunar da ita saman kujera. Da kansa yaje yayi duk abinda ya kamata, cikin 40 munites ya gama komai. Sai ga shi ya fito yana goge zufi ya kalli Mubina wacce take bacci saman kujera ta takure se rawar sanyi take, sai sauke ajiyar zuciya take. Fashewa yayi da kuka yana girgiza kansa ya isa bakin kujera yayi saurin daukarta cak ya nufi saman gado ya kwantar da ita, ya taɓa jikinta zafi rau ya luluɓeta da bargo, yace"Ina sonki koda ƴaƴa nawa zaki haifa shegu tinda ba da sonki haka ta faru ba, bawa baya tsallake kaddara sa." ya faɗa yana goge hawayen fuskarsa ya buɗe kofar ya fice.
Mamu na ganin Sageer ita da Umpah rigai-rigai suka nufoshi. Tiris Mamu tayi ganin Sageer na zubar da hawaye. Umpah yace"Me ya sami Mubina ɗin.?" Sageer yace"Mu amshi Kaddara Daddy Mubina na dauke da ciki tsawon sati 6 a jikinta..." Umpah Nan take ya zube ƙasa ya fashe da kuka, Mamu ta faɗa kansa.........
*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805*
*👉ðŸ»+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*
*Book 1*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
3ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Mamu ta rungume Umpah ta fashe da wani rikitaccen kuka, tana cewa"ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar, da muke ciki..." Haka suka kasan ce Mamu kuka Umpah kuka, Sageer kuka ba mai lallashin wani a cikin su.
Sageer yay karfin halin cewar, "Dady mom don Allah mu fauwalawa Allah lamarin mu amshi kaddara , wallahi ina sonta sbd Allah, kome Mubina ta zama nayi alkawalin auranta da zuciya ɗaya , kuma ina son cikin jikinta bashi da uban da ya fini har abadan..." Umpah ya katse shi ta hanyar cewa, "No Sageer hakan ba mai yuwa bane ba ta sauƙi..... Ta yaya zaka amshi ɗan wani kace kaine ubansa ka dora laifin wani bisa kanka, dole zamu faɗama iyayan yaron su san a halin da ake ciki, kuma insha Allahu bazan fasa baka auranta ba! A duk inda take, se dai ina so zan fara shirye-shiryan kaita London ta zauna can hannun ƙanwata har Allah ya sauketa lfy, ta karasa karatun ta acan..." ya faɗa yana janye Mamu daga jikinsa ya miƙe yana hawaye, ya kama Mamu ta miƙe tsaye banda kuka babu abinda take...
Umpah yace"Kiyi hkr mu bar ma Allah ikon sa Nusaiba, Allah shi kadai yasan abinda yasa yayi hakan... So mu amshi kaddara da hannu biyu, muje mu ganta."
Sageer yace "Umpah bacci take jikinta akwai zazzaɓi mu shiga na haɗa allurai irin nasu na saka a drip na ɗaura mata dole sai ta kwana munga jikin nata." Umpah yace"Ok Sageer Allah ya maka Albarka." Sageer.
Yace "Ameen."
Suka shiga ciki suka zauna bakin gadon, Mamu ta janye bargon da Sageer ya rufa mata, ta kama hannunta ta zuba mata idanu, hawaye na kwaranya kan fuskarta, tana me tausayin ƴar tata. Umpah ya shafa fuskarta yace"Mubina kina ganin rayuwa yarinyar ki ƙarama, Allah ya bamu hakurin cin jarabar damu dake baki ɗaya."
Mamu tace"Ameen"