← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 124

Sashe 79

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zama tayi can tsinin kujera tana raraba idanu tana hawaye ko wacce irin Addu'a tazo bakinta yi take. Kamal ya zauna É—an nesa da ita, dan sam baya jure zama kusa da ita a yanzu. Ya ambaci sunanta cikin wata siririyar murya.
*"Mubeena"* ya ƙirata yana tsareta da tsumammun idanunsa. Mubina kin amsawa tayi ta zumburo baki gaba tace"Faɗi inaji ka maidani gida." Kamal ya lumshe idanunsa yana jin anya zai jure zamansu da Mubina waje ɗaya ba muharaman juna ba? Da ɗan karfi yace.
No im possible wlh! Zan cutu ko shaiɗan yay galaba a kaina No bana son hakan, sam bazan iya cutar da ita bazan aikata sabon Allah sam." ya faɗi yana dafe kansa. Mubina ta ɗago da kanta ta ƙura masa manyan idanunta tana hawaye, tace" Nidai tashi ka kaini gida don Allah." ta faɗi tana rushe masa da kuka.
Kamal ya É—ago cikin masifa ya daka mata tsawa yace.
"Ke!! Wlh kiyi gaggawar haɗiye kukanki ko yanzu na baki mamaki barauniya kawai bakida aiki sai jaraba da satar zuciyar jama'a..." ya faɗi yana hararanta. Mubina ta ɗago ta kallesa suna haɗa ido ta kawar da kanta saboda mugun kwarjinin da yake mata, sam bata jure kallonsa wani abune aƙwayar idanunsa, da yake fizgarta. Cikin kuka tace"Allah ne kadai zai sakamin tsakanina da kai ni wallahi ko Umpah da Mmau sunsan bana ɗaukar kayan kowa a ɓoye, amnan kai ko har saceni kasa akayi ka kaini wani waje ka rabani da kimata da darajar da Allah yay min ta ƴa mace, ka sakani tashin hankali nida iyayena da iyayanka, amman har kace min barsuniya, ba gwara barawo ba da kwarto, tunda barawo sai yagani yake ɗauka."ta faɗi tana kuka.
Kamal jikinsa yayi sanyi ya lankwasa murya yace"Am sorry Mubee nasan nan gaba zaki gane ba da gangan na miki kome ba! Kuma ina nufin na kamu da matsanecin so da kauna tin lkcn muna chart a matsayina na kurma, ke bakiji kina son É—an kurman bane Uhm sanyin Idaniyata?" ya faÉ—i yana kallonta cikin zallar kaunarta.
Mubina ta zumburo baki ta hararesa ƙasa-ƙasa ba tare da ta yarda sun haɗa idanu ba, a shagwaɓe tace"Eh ni bana wani sonka Allah ma ya kiyaye wollah tufff." ta faɗa tana tofar da yawu.
Kamal ya shafi sajan fuskarshi yace"very gud naji daɗin hakan, so abinda zamuyi yanzu shine zamu ƙulla aminci dake Ki nutsu kiji abinda zan faɗa maki, idan ko kinki kika ƙiya zan wuce dake saudiya gobe..." A tsorace! Ta kalleshi jikinta na rawa. Kamal ya ɗaga mata gira yana watsa mata wani sihirtaccan murmushi, mai narka zuciya, yace"Yes Sanyin idaniyata wallahi da gaske nake kuma zan maki tsirara nayi vedio na turama ƴan gida nace ke kikace muyi tsirara dan su gani muna son juna amana aure ko mu idasa lalacewa..." Mubina ta ƙara sautin kukanta ta ɗora hannunta a kai tace.
"Nashiga uku Allah ka kareni da kariyarka daga mugun bawanka, wlh *Kan Giwa* na tsaneka mugun Gurgu kawai, Allah ya isarmani." Kamal yace.
"Ameen ya Rabbi, bazaki fasa faɗin gurguba? So yanzu dai ina son a ɗaura mana auren yarjajeniya, na tsawon sati ɗaya kawai a matsayina na kurma bazan taɓa maki mgn ba sai ta kurame da zaran kin cika sati a gidana idan har baki soni ba zan sakeki kuma na yafe cikina da kika zubar min, ba sai na maki wani, idan ko kinki zan maki ta ƙarfi babu auran na ƙaro maki cikin shege na kuma gudu dake shikenan kinyi asara karatunki ga su Umpah zasuyi fushi dake ba wanda zai ƙara yarda dake, daman cewa zasuyi na farkoma da sonki mukayi..." Mubina jikinta har ɓari yake ta miƙe ta iso gaban Kamal ta zuɓe saman guiwowinta, tana kuka ta riƙe ƙafafunsa jikinta na rawa, tace.
"Wai me na tsare maka a duniya kake son ganin ƙarshena? Ya zaka haɗani da iyayena ka kuma tozartani a karo na biyu, amman ba kome, na yarda wallahi ko shekara zamuyi, bazan taɓa sonka ba, yanzu dai auran sati ɗaya kawai zamuyi ba tare da ko mgn ta haɗamuba, zaka sakeni ba tare da ka saceni ba ka aikata wani abu a gareni ba ko...?" Kamal yace"Yes sa karmin ƙafafuna, karki sake taɓani daga nan har muyi aure mu rabu."da sauri Mubina ta saki ƙafafunsa taja baya ta kwanta saman carpet tana kuka tace.
"Naji na amince in dai zan tsira da mutuncina, amman da sharaɗin zaka mayar dani gun su ummi ko?" Kamal yace" Saboda a gidan Samha ƙanwata na girma ba! Ai yanzu zaki fara aikinki idan kinga nabarki an cika sati kuma an ɗaura mana auran satin ya cika idan an ɗaura a gobe ma nine zan kaiki makaranta bazakiyi missing karatunki ba na gobe, har sati ya cika na koraki nayi gaba naje my umaimata tana jirana."Ya faɗi yana kallonta yana ɗaga mata gira. Mubina ta miƙe zaune tana hawaye tace.
"Ok na yarda yanzu me zan cema ummi da su Umpah da my one Sageer?" Kamal ya taɓe baki yace"Ba my one ba dai my 1000 ne ma ba ruwana, kuma cikin dokokin auranmu babu maganar wani ƙato ki bari har mu rabu can ku ƙarata ba ruwana." ya faɗi yana zabga mata harara. Mubina ta murguda masa baki cikin tsiwa tace"To faɗamin ni abinda zance dan bana wani son wata ɗoguwar mgn dakai wlh." Kamal yace "Yauwa matar yanzu ina wayarki kunnata ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki ki ɗauro alwalla lokacin magarib yayi zan ɗan fita, bayan munyi sallah zan faɗa maki kome yanda zaki faɗama kowa ya fahimceki kinji." Hararasa tayi ta kauda kanta ta miƙe ta nufi toilet ɗin.
Murmushi Kamal ya bita dashi a ƙasan makoshi yace"Yaro yarone koda ɗan giwane."ya faɗa yana miƙewa ya buɗe jakarta ya fara zazzagewa yaga possport ɗinta a ciki, da wayarta ya ɗauka ya danna yaga missed calls ɗin Sageer 12, na Majeed 5 na Umpah 3, tsaki yaja ya nasa wayar aljihunsa yace.
"Sorry Umpah." ya faÉ—a yana rufe mata jakarta ya É—auki wayarsa yayi dialing É—in number Makel, bugo É—aya ya É—aga, Kamal yace"Makel zo yanzu mana ina waje, zanyi sallah." ya faÉ—i yana tsinke kiran. Ya nufi kofa ya zaro key, daga cikin aljihunsa ya buÉ—e kofar ya fice ya rufeta daga waje sanin halinta zata iya fita....

Ɓangaran Majeed kuwa bayan yazo makarantar su Mubina, batanan yana ƙiranta tana ringing bata ɗauka, ya ƙira Kausar wayarta a rufe, hankalinsa a tashe ya nufi gidansu Kausar ɗin, dan sau biyu yana kawo Kausar ɗin idan taje gun Mubee weekend. Yana zuwa bayan sun gaisa da megadi, yace ya masa sallama da Kausar, nan yace masa ai sun fita ita da Auntynta da kuma ƙawarta gun barkar haihuwa..... Nan Majeed ya sauke ajiyar zuciya jin Mubina na tare da Kausar, bayan ya koma gun aiki ya ƙira ummi ya faɗa mata Mubina na tare da kausar. Jin hakan bata damuba dan watarana daga makaranta can take wucewa sai dare mijin Auntyn Kausar da Kausar su kawota....
Mubina kuwa bayan bayan ta ɗauro alwalla ta fito, taga Kamal baya parlon, idanu ta fara rarabawa tana neman sallaya bata samu ba.!!! Sai ta nufi bedroom ɗin, tana shiga taga trolley ɗin Kamal kusan bed, sallaya a shimfiɗe gefe. Cikin mugunta ta nufi trolley ɗin nasa ta buɗe ta zazzage duka kayansa saman carpet, wani irin ɗaddaɗan ƙamshin turaransa ya cika mata hanci, taja tsaki tace.
"Aikin banza da na wofi ɗan iska kwarto bani zaka auraba sati ɗaya sai na koya maka hankali, cikin satin kan mu rabu, tinda a dokar auran bazaka min mgn ba kurma ne, wayoyinka zan sace na ɓoye, sai naga da uwar da zaka na min mgn nayi ta maka iskanci iri-iri bakada bakin mgn." ta faɗi tana fatowa da tsadaddun kayansa na sakawa tana watsi dasu tsakiyar ɗakin ta cire laptop ɗinsa ta ajiye gefe, ta ɗauki wata jallabiya fara ƙal ta sanya saman kayanta tana done hanci, tace.
"Wannan warin bazan iya ba bari nayi manage da banzan binta sudan ɗin turarensa." ta faɗi ta sunkuyawa ta ɗauki turarensa wanda tayi watsi dasu tsakiyar ɗakin, mai shigen daɗi ta feshe jikinta ta buga kwalaɓar turaran ƙasa ta tarwatse, tana murguda baki, ta dauki hiraminsa ta yane kanta ta koma wajan darduma ta tayar da sallar, magarib..... Bayan ta gama sallah ta miƙe ta ƙarasa fatali da kayansa ta ɗauki laptop ɗinsa ta fito, bata cire masa jallabiyasa ba ta sallah. Har yanzu shiru bai zoba, buga laptop ɗin tayi a ƙasa ta nufi kofar ta murda handle ɗin taji a rufe ƙwaƙwaɓe fuska tayi ta fara ƙwalla tana dukan kofar tana kiransa.
"Kamal Kan giwa ni kazo ka fitar dani mugu kawai." Haka take ta masifa da dukan kofa taji shiru. Nan ta kwanta kofar parlon ta fashe da kuka tana birgima...
Chapter 79 · 0% Book details