← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 124

Sashe 107

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ɓangaran su iyamu kuwa anata kwasar jinya sunyi nadamar abinda suka aikata arayuwarsu babu adadi, burunsu su warke su nemi number Kamal da Mubina su yafe masu, dan sunsan sun cutar dasu haƙiƙa, sai gashi yanzu sun fisu shiga ƙunci da tashin hankali, suba ga karatun ba su ba ga aure ba sun banzatar da kansu, gashi ƙarshensu ƙaton ɗan fashi ya masu cin karnuka.... Ɓangaransu Mounkaila da Tukur abin sai godiyar Allah, dan Mounkaila yayi shanyewar ɓarin jiki, kome sai an masa, ɗan kuɗin motocin biyu da aka siyar sun kusa ƙarewa, ƴarsa ta fara samun sauƙi, saide gidan da suke ciki an badu kwana uku su tashi, saboda Amaryasa da ta gudu da takardun gidan ta siyar da gidan. Susai uwar gidansa ta shiga tashin hankali ga daman shine gidansa ginanne sauran kangone.... Tukur dai da ɗan sauƙi sedai ba shi banda kuɗin motar da aka siyar to bashida ko sisi a ƙasa, saboda kuɗin bank duk dasu suka yashe suka ƙara zuba kayan aiki a kamfani, to ribar da ta fito ce wuta ta cinye, basu kai su ga bank ba....

Bayan sallar isha labarin ganin wata ya bazu a ko ina birni da kauye, jama'a se murna suke suna ƙiran ƴan uwa d aabokan arziki ana neman gafar juna.
Ummah ce zaune kusan Abbu, Samha na gefe Ummah tace"Yaron nan bazai ƙira bama yace sunga wata, oh ni Fatima." Samha tayi dariya tace"Kai Ummah yaya Kamal fa kullum ƙira yake yau ɗaya a masa uziri mana..." Abbu yayi murmushinsu na manya yace.
"Kai Fatima akwai gaggawa shi ya fara ƙirana yace suna masallaci anga wata, zai ƙira anjima yace a gaisheki fa." Ummah tace"Yo to ina nasani nazata bai ƙiraka ba ai, Goggo ta sani kuwa?" Abbu ya kalleta yace"Kai Wannan mata to me zai hana ta sani ta sani mana, naje can gidan ai..." Sallamar Sageer ce ta katse masa magana. Abbu ya amsa yana cewa"Ah Sageer bismillah."
Cikin ladabi ya ƙaraso parlon ya tsugunna har ƙasa yana gaishesu, Ummah ta amsa cikin fara'a tace"Yasu Nini?" Sageer yace"Suna lafiya Umnah Abbu barka da ganin wata Allah ya nuna mana ƙarshensa lafiya." suka amsa da "Ameen" a tare.
Samha tace"Yaya Sageer ango." Murmushi yayi yace"Samha ya karatu an shiga hutu ko?" dariya tayi tace"Eh ni wallahi dama Abbu ya zubamin kujerar umara se na iske su yaya Kamal muyi ibadarmu cikin nutsuwa acan." dariya ta basu su duka suka dara.
Abbu yace"Allah sarki inda kinyi haƙuri ai ƴar gidan Jafar zaki zama ma baki ɗaya." cikin jin kunya ta miƙe da gudu tayi bedroom. Sageer sun ɗan jima suna hira ya masu sallama ya tafi, kai tsaye gidansu Amrah ya shiga.

Ablah an baje saman kujera tana kallon tashar Al'jazeera, tana kallon labarin ganin wata da al'ummar duniya sukeyi.
Mamu kuwa se kai komo take kitchen, Umpah na zaune suna magana da Zabairu wanda ya iso yanzu ba jimawa daga Naimey, magana suke kan auran Basma da Kabeer, dan yanaso ya wuce Algerie jibi, sun gama magana da Isma'il mahaifin Basma gobe zaje neman auranta.
Sageer ne yay sallama daga kofar parlo. Su Umpah suka Amsa, ya shigo ya duƙa har ƙasa, cikin ladabi yace.
"Umpah ina yininku barka da ganin wata Allah yasa muga ƙarshensa lafiya."Zabairu da Umpah suka amsa da "Ameen" Mamu tace"ya wajan tsafin?" Sageer yace"suna lafiya Ablah ina yini."Ablah ta amsa tana tsokarsa. Murmushi yayi Mamu ta miƙe ta nufi sama.
Amrah tana kwance tana chart da ƙawayenta, wanda sukayi makaranta tare. Mamu ta shigo tace"Amrah shirya ki fito mijinki yazo ku gaisa, sauran ki masa shan ƙamshi." Amrah ta ajiye wayar, tana turo baki tace"Mamu dan Allah shan ƙamshin me nayi?" Mamu tace"Na uwaki." ta faɗi tana ficewa. Saukowa tayi daga saman bed ɗin ta ɗauki hijab ta saka ko turare bata saba ta nufi ƙasa. Kusan Ablah ta zauna tace da Sageer "Ina yini." Sageer ya amsa yana miƙewa. Yama su Umpah sallama. Umpah yace bazaki rakashi ba." miƙewa Amrah tayi ta biyo bayan Sageer. Tafiyarsa yake a nutse, har yaje tsakiyar compound ɗin gidan, yanajin takun Amrah na biye dashi tana gunguni tace.
"Wai bazaka tsayaba muyi sallamar da aka turoni muyi gaskiya ni zan koma." ta faɗi tana jan burki, cak ta tsaya. Sageer murmushi ya saki yaƙi tsayawa yayi kamar bai jita ba, dan so yake ta iso har gun motarsa.
Amrah tsaye tayi tana kallonsa har ya isa wajan motarsa kusa da gate. Cikin jin haushinsa ta ƙaraso lokacin yana shiga motar, tsaye tayi tana turo baki.
"Bakin ya ƙarema kallo a ransa yace"Bari na koya maki ladabin bin miji." kofar ya buɗe yace"Am Amrah shigo kiji mana zan baki sako gobe fa azumi zamu tashi dashi, amman bakya neman gafara wajan mijinki?" yafaɗi yana kallonta. A hankali tace"To meyasa ka rabani da masoyina Lameer ka aureni...?" ta tambayeshi tana matsar ƙwalla.
Sageer yace"Yauwa zo ma kiji yanda abin ya faru." ya faɗi yana beƙa mata hannunsa. Kin kamawa tayi tace"Aa faɗamin a haka." Ganin bazata shigoba ya waiga yaga megadi da sauran ƴan aikin gidan ba kowa kusa yayi kamar zai rufe motar kawai sai ya fizgo hannunta ya jayota cikin motar, ta faɗo samasa ya rufe motar .
Ihu ta saki tana shirin sanya kuka, yayi saurin matseta jikin kujera yayi wufff da bakinta ya tura bakinsa aciki, bai jira komeba ya shiga kissing É—inta da zafi zafi yake shan bakinta.
Idanunwa ta zaro waje jikinta ya shiga rawa tana kallon yanda ya kanainayeta yana tsotsar bakinta, ga wani ƙamshi da bakinsa yake fitarawa. Haƙoranta ta saka iya karfinta ta gantsara masa cizo, a harshensa ba shiri ya zare bakinsa a nata yana cewa.
"Woshhhh zafi wlh." ya faɗi yana ruƙumƙumeta. Kuka ta sakar masa tana cewa"Daman saboda haka ka rabani da Lameer ko?" Sageer yace"No Amrah ki daina faɗin haka mana wlh yanda aka miki haka akamin ƙanwarki fa ce zan aura ya zanyi kuma na dawo nace ke idan ba ƙaddara ba bari kije to yanda abin ya faru, nasan kuma kinsan soyayyar da take tsakanina da Mubina kafin ta juya ta koma tsakanin Kamal da Mubina, wacce suka ƙulla a london..." Nan Sageer ya bata labarin yanda sukayi da Umpah da kuma Lameer kan cewa shine ya haƙura da ita wai ƴar uwasa ze aura da su biyu zai haɗa, dan yana sonta, to yaji daɗin dattakun Umpah shiyasa yace ya barmin ke ba sai an bashi wata ba..." to kinji fa Amrah dan Allah me laifina?" ya faɗi yana ɗago da fuskarta yana mata wani sihirtaccan kallo.
Idanunta ta lumshe ta ɓoye kanta a ƙirjinsa. Murmushi yayi ya shafi kanta ya ɗagota yace"To shiga ciki sai da safe."ya faɗi yana bata kiss a goshinta, ya manna mata ɗaurin kuɗi yan jaka. Jikinta ta janye ta fito a mota tayi wufff ta ajiye masa kuɗinsa saman cinyarsa, ta juya ta fara tafiya. Fitowa yayi ya biyota da sassarfa, ya kamo hannunta ya rungumota saka mata kuɗin cikin rigarta har ya tabo albakatun ƙirjinta, yace"Ke matatace kuma Azumine yazo dan haka ki biya buƙatarki ba sai kin takurama su Mamu ba." ya faɗi yana sakinta ya juya ya tafi ya barta atsaye. Da kallo ta bishi tana turo baki. Juyowa yayi suka haɗa ido kunya taji ta turo masa baki ta juya cikin sauri ta nufi ciki. Murmushi yayi ya ƙarasa ya shiga mota ya mata key yaja ya nufi gate ransa fari tas. Haladu direba akwai gulma ashe duk yana kallon, ya iso wajan baba megadi wanda zai zauna kan benci ya gama kulle gate kenan bayan tafiyar Sageer, Haladu yace"Baba kaga masoya ko? Allah me iko mijin ƙanwa ya zama na yaya wai kaga yanda ya wani kanainayeta zai bata kuɗi, cikin riga fa ya saka mata kuɗin, wlh daman kamar itace yakeso, a motama naga sun jima Allah kadai yasan me sukayi..."Baba megadi yace"Kai subahanallahi Haladu ka lalace ina ruwanka matarsa ce fa ni bana son gulma, ko tsoron Allah bakaji watan Ramadan guda." ya faɗi yana juya masa baya. Haladu ya miƙe yace"Ai ba gulma bace to na barka lafiya baba." ya faɗi yana shiga kewayansa. Baba megadi ya bishi da kallo. Amrah kuɗin ta ciro daga rigarta tana mamkin daman Sageer kwartone, tana shiga ta fara ciccira idanu cikin kunya ta ba Mamu kuɗin ta gudu sama. Da dariya suka bita.

Saudiya bayan sun Kammala lunch, suka baje aka fara hira duk akan dai azumin ne.
Umaimah ko lunch kin fitowa tayi sabida tsabar haushin Mubina da takeji, ɗaki ta ƙulle tana chart ɗinta, se Raihana ta kaimata abuncinta can, taci dan tace bazata fitoba, tana ci suna video call da ƙawarta Amisha tayi ta zugata akan meyasa zata yarda mace mai ɗaura zane a hannun hagum ta azabtar da ita saboda namiji, nan fa tayi ta zugata karta bar mata Kamal ɗin ai yayantane.....
Chapter 107 · 0% Book details