← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 124

Sashe 91

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mubina tana gama sallah ta kwanta nan saman darduma ɗin, yin duniya sun mata taci wani abun taƙiya. Nabeel da Majeed sun tafi sai ummi kawai tana famar lallashi, Mubee taƙi sai kuka. Ummi ta zauna ƙasa ta ɗora kan Mubina a cinyarta, cikin lallami tace" Baby ba fa da Sageer aka ɗaura miki aure ba da Kamal aka ɗaura."Mubina ta ɗan ɗago ta kalli ummi da shanyayyun idanunta da suka rine, ta zumburo ɗan ƙaramin bakinta gaba tace.
"Ummi ni bana sonshi ai kuma tsokanata kike, ni ina ruwana dashi."ta faɗi tana lumshe idanunta. Murmushi ummi tayi tace"Hummm bakya so kika ki cin kome? Bari ma na ƙira Mamu na faɗa mata."
Ummi ta faɗi tana daukar waya kamar zata ƙira Mamu. Mubina ta miƙe ta rike hannun ummi ta marerece tace. "Ummi bana jin yunwa ni ƙirawo Dr ya sallame mu mu tafi gida zanci agida."ummi tace "No sai kinci tukun..."knocking ɗin kofar da akayi ce tasa ummi katse maganar tace.
"Bismillah" Ganin ba abuɗe ba an shigo yasa ummi janye kan Mubina, ta miƙe ta nufi kofar, ta buɗe. Kamal da Makel ta gani tsaye. Cikin girmamawa suka gaisheta.
Ummi ta amsa tace "Bismillarku."Biyota sukayi a baya, har ciki ta nuna masu ɗayan gadon mai face da na Mubina suka zauna. Kamal tinda ya shigo idanunsa kan Mubina. Makel ne yace"Madam ya jiki?" Mubina jin murya Makel yasa ta ɗago da sauri, ta waigo sharan da yake, karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna ita da Kamal. Manyan Idanuwanta ta waro waje, cike da tsoro ta miƙe ta faɗa jikin ummi tana cewa"Ummi kin ganshi ko me yasa kika barshi ya shigo? ai ni inada aure."
Ummi tayi dariya ta buga bayanta tace"Eh shima yanada mata gaki kusansa gunki yazo."Mubina ta girgiza kai ta kasa magana. Kamal yace"Mubina sannu ya jikin naki kinci abunci kuwa?" Ummi ta janyeta tace"Wallahi shine nake fama da ita taki cin kome tin jiya, zo don Allah ko tea kasata tasha, ni bata tsorona." ummi ta faɗa tana miƙewa.
Mubina ta ruƙumƙumeta gam ta saki kukan sangarta tace"Wlh ummi bazaki fita ba zanci abunci yanzu."Ummi ta ƙwace jikinta tana dariya tace"ƙarya kike tin safe nake fama dake nida yayunki, kika ƙiya, har gashi ana dab da ƙiran magarib." ta faɗi tana buɗe kofar zata fice. Mubina ta biyota da gudu. Kamal yay saurin tare kofar ya tsare hanyar ya rufe kofar. Ƙasa ta duƙe tana zumburo baki gaba, tace"Ni dai ba ruwana dakai fita a sabgata."ta ƙarasa maganar tana sakin kuka. Kamal cikin tsantsar sonta da kaunarta haɗi da tausayinta ya zuba mata kyawawan tsumammun idanunsa, wanda kallo ɗaya zaka masu ka gane zallar ƙaunar Mubina da suka baiyya a cikin idanun nasa, ya zuba mata su tamkar zai cinyeta kukanta na taɓa masa zuciya ya sunkuyo dab da ita, still idanunsa a kanta yana kallonta, cikin wata kasalalliyar murya mai cike da mayen sonta yace.
"Ya Salam me na miki kika fita sabgata? Bakya murna da kasancewarmu miji da mata ne? Haba sweetie na, nafa san kin mutu akaina, kamar yanda na mace nima, akanki.
"Oya muje kici abunci." ya faɗi yana kama kafaɗunta zai miƙar da ita. Buge hannunsa tayi, ta ɗago ɗa kanta, cikin rashin kunya, idanunsu suka sarƙe da na juna, gabanta ya yayi wani irin faɗuwa idanunta da suke cike da mayen sonsa suka fallasa sirrin kansu, ta kawar da kanta tana turo baki. Kamal bai jira kome ba yay sama da ita ya dauketa caɗak, ya manneata saman faffaɗan ƙirjinshi, kamar ƴar baby.
Ihu ta saki tana dukansa da wuntsila ƙafafu da ɗan guntin karfinta da ya raga tana cewa.
"Sakeni ni bari taɓani bana so." Ta ƙarasa maganar tana dukan ƙirjinshi tana gunjin kuka tana kallon kyakyawar fuskarsa, mai ɗauke murmushi. Saman gadon ya ɗorata, ya zauna dab da ita ya riƙeta gam, yace da Makel"friend zo haɗamin tea mai kauri ka zuba min abunci kuma."Makel ya miƙe yana dariya ya iso gun kayan abuncin ya shiga haɗawa. Mubina kuwa fasa kukan tayi ta haɗe gira sama da ƙasa taki ko kallonsa. Makel ya beko masa cup ɗin tea ɗin, ya matso masa da plate ɗin jalof ɗin taliyar yace"Bari na baku waje." ya faɗa yana ficewa ya rufo kofar. Kamal ya janyota jikinsa ya tallabo kanta, yace"Haaaa bakinki kinji Sweetei." Cikin tsiwa tace"Bazan shaba ko ana dole? Ni sakeni." ta faɗi tana ƙoƙarin ƙwace jikinta. Kamal ya kurɓi tea ɗin a bakinsa ya ajiye cup ɗin ya kamo ƙugunta da hannunsa ɗaya, ya ɗago kanta, da ɗayan hannun nasa, ta ɗago a tsorace idanu suka haɗa, ya watsa mata wani shu'umin kallo mai saka mutum cikin shauki batare da ya shiryaba nan take ta gigice ta rasa abun yi ga ƙamshinsa da yagama gigitata, ga wani sinadari da suke fitowa daga cikin ƙwayar idanunsa suna shiga nata idon.
Lumshe shanyayyun idanunta tayi, ta xumburo baki gaba, hawaye suka fara zirya kan fuskarta. Kamal ya matsu fuskarsa dab da tata, jin hucin numfashinsa, dab da ita, yasa ta buɗe idanunta, shiko yayi azamar ɗora bakinsa saman nata, ta buɗe da niyar ihu ya juye mata tea ɗin bakinsa. Ta waro idanunta tana girgiza kai. Idanunsa ya sake zuba mata, take ta haɗiye tea ɗin, abin ya xare bakinsa sai ya shiga lasar harshenta yana ɗan yawo dashi tsakiyar bakinta. Kuka ta saka masa tana ririƙeshi, ya zare bakinsa anata ya ɗauki cup ya sake kurba, kukan ta haɗiye cikin mayar da numfashi ta fara magana tana hawaye tace"Kamal zansha tea ɗin da kaina." ta faɗi tana kwantar da kanta kafaɗarsa. Wani irin magaɗisun kaunarta ne ya sake kawo masa marfaki yana bin kowane lungu da sako na jikinsa, baiya magana ba ya haɗiye tea ɗin bakinsa ya janyota jikinsa sosai ya ɗago da kanta ya kafama cup ɗin a bakinta, yace"Oya sweetheart." ba musu ta fara kurbar tea ɗin da sauri sauri. Kamal yana shafa bayanta da yake cikin hijab yana bata tea ɗin tana sha, sosai tasha kanta bisa kafaɗarsa, sai da ya kusa qarewa ta kawar da kanta gefe, ta janye daga jikinsa. Plate ɗin jalof ɗin taliyar ya ɗauka ya gyara zamansa ya saka hannunsa ya ƙara matsowa kusanta ya tsakuro taliyar ya kai bakinta. Kai ta kauda tana turo baki gaba, baiyi magana ba ya saka taliyar bakinsa ya fara taunawa. Tana satar kallonsa ganin haka tayi saurin juyowa gareshi baki ɗaya, cike da rauni ta riƙe hannunsa ta shagwaɓe fuska, cikin zazzaƙar muryata da tasake yin ƙasa da ita, ta riƙe hannunsa gam cikin nata, wanin irin sukaji shock, sukaji atare bata yarda ta kalli idanunsa ba tace.
"Kamal zanci da kaina kaji."ta faɗi cikin wata irin siga tana ƙara yin ƙasa da kanta, tana gunguni, still hannunta damƙe da nashi. Kallonta yake cike da tsantsar ƙaunarta.
Cikin cool voice ɗinsa yace"Sanyin idaniyata please kalleni kaɗan kinji Sweetiena."Taushin muryasa da daɗin mgnr da ya mata yasa taji wani iri acikin jikinta. Hucin numfashinsa taji dab da hancinta, yana hura mata iskar bakinsa, yana murza lallausan tafin hamnunta cikin nashi, wani dumi sukeji atare, da sauri ta rumtse idanunta, zuciyarta na bugawa, ga fitinannan ƙamshinsa ya cika mata hanci. Cikin aro jarumta ta fizge hannunta ta matsa gefe, tana cewa"Ni Kamal yunwa nakeji."Ta faɗi tana ɗago da kanta ta kalleshi ƙasa² da runannun idanunta, tab suke da hawaye. Plate ya riƙe ya kamo hannunta ya nasa a cikin abunci A hankali cikin taushin murya yace.
"Sorry Sanyin idaniyata Oya ci abunci na dubaki Dr yaxo ya bamu saki zakije guna muyi fira?" ya faɗa yana tsareta da shegun idanunsa. Taliyar ta ta tsakura takai bakinta tare da bismillah, ta fara ci ko kallonsa batayi ba, bare yasa ran zata amsa masa. Barinta yayi dan taci abuncin a nutsu amman yasan wayon da zai mata ya ɗauke abarsa, yau saman ƙirjinsa zata kwana. Murmushi ya sake ya shafi gefen fuskarta, sauka yayi daga saman gadon yana ƙarema room ɗin kallo ya sunkuya ya dauki cup ya tsiyaya mata ruwa a cup ya kai mata dab da ita ya ajiye. Kallon tsadaddiya agogon hannunsa yayi yaga, lkcn magarib yay bazai wuce 5 minutes ba ayi ƙiran sallah, da sauri ya nufi toilet. Mubina ta bisa da kallo, kamar ya sani ya juyo ido hudu sukayi, ya sakar mata lallausan murmushi mai kashe jiki. Ta murguda masa baki ta kawar da kanta gefe, tana cin taliyarta. Ya kama handle ɗin kofar yana shafa sumar kansa, still yana murmushi yace.
Am Matata bakijiba." Da sauri ta waigo ta kalleshi tana turo baki cikin tsiwa tace"Ni ka fita sabgata." ta faɗi tana kauda kanta gefe, sai tura taliyar take cikin bakinta, kamar dole. Kamal ya girgiza kai yace "Ok bari nazo na wuce gun Umaimah ta ma." Da sauri takalleshi tace"Uwar yarinya zan Allah kuwa, ni bana ɗaukan renin karuwsi fa, karkaje kabari har mu rabu." ta faɗi idanunta na kawo ƙwalla, tana kallonsa. Idanunsa ya waro yace.
"Am sorry Sweetiena na saki kuka bari na fito na lallashi abata. Baki ta murguda ta kawar da kanta. Kai ya girgiza ya shige toilet É—in.

Yana shiga Mubina sauko daga saman gadon ta ajiye plate ɗin taliyar ta ɗauki ruwan tasha, ta saka takalmi tayi dam ta buɗe kofar ta fice a guje. Ummi da take zaune saman kujerun gurin ta miƙe tana cewa"Baby lafiya?" Mubina ta rungume ummi tana maida numfashi tace"Yo ni kawai sai haɗani da ƙato ɗaki ɗaya, niko na gudu wlh yafiye abin haushi ne." Ummi tace"Yanzu dai bazakiyi hankali mijin naki ne kato mijinki ne fa, shine me abin haushin ma, bakeba? yanzu muje dai a ƙira Dr ya sallamemu lokacin sallah yayi." ta ja hannunta suka nufi cikin room ɗin.
Chapter 91 · 0% Book details