← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 124

Sashe 116

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai lokacin Mubina hankalinta ya kawo kansu Ummah, cike da jin kunya ta saki Amrah ta nufi gun Ummah ta rungumeta gam tace"Ummana i miss u i love u." Dariya Ummah tayi ta rungume Mubina tana shafa bayanta, tace"Barka da zuwa dota ya gajiya.?" jikinta ta janye cike da kunya ta isa wajan Abbu ta sunkuya har ƙasa tace"Abbu ina yini i miss u." Dariya Abbun yayi ya ɗagota yace"Sannu dota ya gajiya." kanta ta sadda ƙasa tace"Alhmdllh." Iyayan nata sunyi mamakin yanda Mubina ta nutsu haka sosai. Kamal ma cike da kunya da ladabi ya ɗuƙa har ƙasa ya gaishe da Umpah da Mamu, Umpah ya ɗagoshi ya rungimeshi yana masa sannu da zuwa. Samha ta rungime Mubina tana mata sannu da zuwa... To haka suka rankaya motoci kowa ya shiga motar gidansu, duka rankaya gida.

Sageer zaune suke a parlon su Kamal shida Goggo da Hafsat suna jiran isowarsu saboda yana aji lokacin shiya yana fitowa yanzu ya nufo gidan kai tsaye, ya taras basu isoba, sai ya zauna. Da sallama suka shigo parlon. Sageer ya miƙe ya nufi gun Kamal a guje, rungume juna suka sosai suna dariyar murnar ganin juna. Sageer yace"Wow masha Allah haka saudiya tas aka ƙara girma da haske?" Kamal ya sakeshi yana hararsa, ya nufi gun Goggo ya faɗa jikinta yana murmushi yace.
"Goggo na nayi kewarki sosai wlh fatan kina lafiya." Dariya tayi ta kai masa duka, tace"Karya kake a daba kafin ka angwance." dariya sosai Goggo taba Kamal yace"To shikenan tinda haka kikace." ya faɗi yana komawa kusa da Hafsat yace"Uwa mabada mama ina yini i miss u dayawa dayawa." dariya tayi yace"Ai nazata ka manta dani ne." Idanu ya waro yace''taba wane ni." Ummah ta kama hannunsa tace "Aje ayi wanka azo asha girki kala²." ƴar dariya yayi yace"Sageer muje ko ka bani labarin an gwancinka." Hararasa yay ya kama hannunsa suka haura sama. Su Abbu suna murmushi, Ummah da Hafsat suka shiga jera kaloluwan girke² da aka masa shida matarsa. Ummah ta ware na Mubina ta zuba a cikin kwando taba Samha ta kai mata.

Mubina suna shiga ta faɗa jikin Ablah da kame saman kujera a parlo ita adole fushi take da Mubina. Mubina tace"Ablah dare da rana tunaninki nake i miss u Ablah nah." Ablah tace''Mubina mayan ana tunani na ne akayi mikis ƙirama sai mun roƙa, amman fa kin ƙara girma wai ko da yake ance har kinyi ciki ko.?" Mubina ta ɓoye kanta jikin Ablah ɗin tana dariya.
Mamu dai batayi magana sai murmushi take ganin yanda ƴarta tayi mulmul masha Allah ga alamun ciki nan ƙarara.
Umpah yace"Auta jeki kiyi wanka kizo kici duk abinda kike so an girka miki." janye jikinta tayi daga jikin Ablah ta miƙe ta kalli Mamu ta da Kabeer tace"Ina Basma taƙi zuwa tarba ta ko hamm zan kamata wallahi." Mamu tace"Ayya Auta batajin daɗine tana fama da zazzaɓi ne." Mubina tace"Ayyah Bari na huta sai naje na dubata." ta faɗi tana haurawa sama.... Samha lkcn da ta kawoma Mubina girki itako tana sama ta dan jima kaɗan ta tafi. Mubina wanka tayi da ruwan gumi sosai ta gasa jikinta ta shirya lkcn ana ƙiran sallah ta tayar da sallah tana gamawa ta shaiyar ta sauko ƙasa. Girke² iri² aka tsarawa Mubina, nan ta baje tana ciye ciyenta saboda cikin baya hanata cin kome, har girkin gidan su Kamal saida taci, ana tana tsakiya da ciye ciyen ne tace"Allah sarki Kamal ko yaci abunci." Idanu ƴan gidan nasu suka zuba mata. Taji kunya ta fara masu kukan sangarta na borin kunya ta koma jikin Umpah ta rungumeshi tace"Yo ba subutar baki bace nayi Umpah ni ina ruwana ma idan bai ciba." Dariya ta basu sosai. Umpah ya shiga biga bayanta yace"Ai nasani ba da gangan kika faɗiba." to haka yasa ta saki jiki tana lashe lashenta, Mamu dai kallon ƴarta take masha Allah.

Ɓangaran Kamal ma hakane bayan sun dawo daga masallaci da Abbu da Sageer dan Ibrahim ya wuce. Nan tsakuyar parlo suka baje ana sunci sun sha Kamal sai santi yake shima saida bakinsa ya kubce wajan cewa ko Mubina taci wani abun? Allah sa zazzaɓi bai rufe masa itaba.... Sageer dariya kawai yake yana tsokanarsa. Kafin zuwa dare, ƴan sannu dazuwa sai shige da fice ake gidansu Kamal da Mubina. Basma sai dare ta samu tazo tare da iyayanta sun jima sosai, kafin su tafi tama Mubina tsiya wai taci love tayi kyau ta murje, ko dai har ta ɗaukane? Mubina dai bata kulataba har suka rabu... Can dare Kamal ya ƙira Mubina yaji lafiyarta cikin ikon Allah batayi zazzaɓin ba. Haka sukayi ta fira Mubina harda kukan shagwaɓa wai ƙirjinsa takeso ta kwanta, dakyar ya samu yayi ta lallaɓata har tayi bacci. Washegari Kamal da kansa ya kawo kayan Mubina, Harda sarƙa Zinaren da ya siya mata da tsadaɗiyar wayarta da ya siya mata, sarƙa tanada ɗan kunne da zobe da abin hannu wanda kima kuɗinsu 1 million take, kyautace ta musamman da zai bata ya faranta mata, kamar yanda take faranta masa, duk da yasan zinare wajan balarabe bata fi ƙarfinsu ba, tanada ma ita, so amman yaba kyauta tukuici.
Haka Aka shiga rabawa ƴan uwa da makota arziki tsaraba, shima ɓangaran Kamal haka suka shiga rabon tsaraba , Umpah yaji daɗin kyautar da Kamal yay Mubina sosai.

Kwanci tashi babu wuya A wajan Allah! yau satinsu Mubina biyu da dawowa niger, hakan yayi daidai da gobe tarewar Amrah da kuma bikin Kabeer da Basma Mubina da Kamal duk gobe kowa zaije ɗakin mijinsa, masha Allah anko uku sukayi iya family ɗinsu ganin guri ya ƙure, amman Basma su sun jima da fito da tasu, dan da farko Mamu tace su bazasu yiba zauwar Mubina tace sai anyi ta kafa rigima, ita da ba lafiyar kirkiba. Dole akayi, dan haka abubuwa sun kaceme An kawo lefen Sageer akwatina 12 yayi da kaya masu Masifar kyau da tsaɗa, hakama Kabeer ya Yama Basma kaya na gani na faɗa. Ɓangaran Kamal kuwa shi ba'a magana wajan kayan dan har akwatinansa da kome daga saudiya ya sayo abinsa, duk kayan da yama Amrah na baya Umpah yay ta faɗa. Kamal yace Waccan yabarma Amrah Sageer nashine ai. Umpah yace kayan sunyi yawa, saboda ba ƙaramar dukiya Kamal ya zubama Mubina ba... Aure yazo yanzu kam sosai zazzaɓi ke damunta, gashi Ana masu gyaran jiki, ita Mubina ba'a bata maganin mata, saboda cikin jikinta, sai na gyaran fata da tsumin turare wanda take wani irin launin ƙamshi, da kuma koya mata abubuwa daban daban na rayuwar aure.
Mubina basa samun keɓewa, da Kamal sai waya dakyar ya samu ya ɗauketa so ɗaya tin suna baƙin zauwa, ya kaita gidansa sukaci juna sosai. Sageer gidansa ya tsaru masha Allah Umpsh ya zubama Amrah dukiya sosa tindaga kan kayan kitchen da bed da Tv fridge abin ba'a cewa kome. Mubina kuwa daman akwai kayan Amrah wanda aka shirya kafin ƙaddara ta gifta, wanda ba ƙaramar dukiya ba aka kashe, wajan zubasu, sune akaje aka gyara a tamfatsetsan gidan Kamal ɗin aka goge kome tsaf kamar yaune aka zuba kayan saboda ɗakunan suna rufe. Kamal sosai ya maida hankalinsa a company ɗinsa ma'aikatansa sosai sukayi farin cikin dawowarsa, har ƴar walima ta murna babban manager ɗinsa ya haɗa masa.
Wajansu Kamal da Sageer ma sunyi ankon Shadda gzina, fara tas masha Allah sai shirya bikinsu suke, Kabeer ma da abokanansa sun shirya dinner mai ƙayatarwa, bayan ɗaurin aure... Idan kaga yanda Amrah tayi wani irin kyau ita da Mubina abin ba'a cewa kome, kitson su da ƙunshinsu iri ɗaya aka masu tsaf. Ɗangi Abbu na kebbi an cika gida dan babu laifi duk sun zo Muhseen da matarsa yaransa Safiyyah da yaranta, Zakiyya ce kan gaba.

Misalin karfe 11 pm Mubina ce kwance daga ita sai ficikar rigar bacci, ta ɗan rame saboɗa zazzaɓin da ya sha mata kai. Waya manne akunneta se shagwaɓa take zuba masa, ta ɗorama Amrah ƙafafunta.
Amrah ta matsa gefe tace"Kuji yarinya duk kinbi kin bubbugeni da ƙafafu."
Mubina tace"Habibina kaga Aunty taki tamin tausa kuma jikina ciwo yake, barima na koma ɗakin Mamu tamin abuna." ta faɗi a shagwaɓe, tana ɗan hucin zazzaɓin dake neman rufeta. Kamal yace"Wayyo Sweetie sannu babyna baya kyautawa momynsa wollah, bari gobe zaki kwana a ƙirjin Habibinki, kinji Sweetienah."Kukan zallar sangarta ta saka masa tana ƙiransa."Kamal ni kazo kamin tausa."Kamal ya shiga lallaɓata dakyat yasamu kanta tayi shiru.
Sun jima suna hira kafin ya mata sallama, miƙewa tayi ta sauko daga kan gadon ta kalli Amrah da ta ƙumshe cikin bargo suna waya da Sageer banda hira batsa ba abinda yake mata, duk ya taso mata feeling. Mubina tace"Wallahi Aunty daga gani wannan ba hirar arziki kukeba, zallar batsa kuke, inba ha'inciba kiyi magana naji mana, kamar yanda mukayi da Sweety darling."ta faɗi tana ɗaukar hijabi ta saka ta fice ɗaga ɗakin. Amrah dariya tayi tace"Au ashe kajita, barta dai."
Chapter 116 · 0% Book details