← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 124

Sashe 24

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama suka shigo parlon baƙin, Mubina tana riƙe da hannun umpah. Kamal ya ɗago karaf suka haɗa ido da Mubina tayi saurin komawa bayan umpah tana cewa"Umpah nah ai ga ɓarawon da ya sace ni wlh shine me yazo yi gidanmu?" ta faɗa ta na murguda masa baki ta ƙamƙame umpah ta baya. Kamal kuwa abin dariya ma ya bashi wai barawo, idanu ya ƙura mata tayi masa mugun kyau atamfar ta amsheta ɗas a jikinta duk da bata da ƙiba akwai diri. Idanunsa ya janye daga kallonta yana taɓe baki. Umpah yace"Eh Auta shine ajiye hankalin ki bazai kuma sace kiba." ya faɗa yana ɓanɓare ta daga jikinsa. Mamu kai ta girgiza ta isa kusan ummah suka gaisa cikin raha ta gaishe da Abbu ya amsa cikin sakin fuska. Mubina ta isa kusan Abbu ta zauna tace"Dady ina yini." Abbu ya dafa kanta yana murmushi yace"lfy lau doter ƴar albarka." murmushi tayi ta gaishe da Ummah da hafsat suka amsa cikin sakin fuska, se dai Hafsat tana mamakin katuwar budurwa se sangarta. Samha ta gaishe da umpah da Mamu suka amsa cikin sakin fuska. Amrah ce ta shigo da sallama ta kara so ta zauna kusan Mubina ta gaishe da Abbu da Kamal da su Ummah cikin girmamawa, suka amsa suna yabon hankalinta. Mamu ce ta miƙe ta tsiyaya ma kowa ruwa da lemo tabi kowa ta bashi suna godiya, se lokacin Kamal ya rankwafa ya gaishe da umpah da Mamu, suka amsa cikin mutunci. Mubina ko da wasa bata sake kallan sharan Kamal ba... Bayan son sha ruwa da lemo an kara gaisawa, Abbu yayi gyaran murya ko da Abbu yayi gyaran murya Mamu ta kira Mubina ta taso ta dawo gunta ta zauna kusanta. Abbu yace ba kome ya tara mu anan ba se ina son Abdulrahim in roƙi alfarama wajanka kaba Kamal auran ɗaya daga cikin ƴaƴanka masu albarka , da farko Wannan na zaɓa masa" ya nuna Amrah yace "so sai na lura kamar wannan yake so" ya nuna Mubina Kamal ya zaro idanu waje! zaiyi maga Abbu ya watsa masa mugun kallo. Kansa ya maida ƙasa. Abbu yace dan haka ina nema ma Kamal auran Mubina a bamu..." Mubina tayi wata irin zabura zata bude baki tayi magana tana kallon umpah Mamu ta danne mata cinya ta rufe mata baki... Abbu ya zayyanewa Ummah da hafsat da Samha kome tinda safe irin diramar da ke kaftawa... Umpah ya kalli Mubina yaga yanda hankalinta ya tashi... Take ya gano ƴarsa bata son Kamal. Gyaran murya yayi yace" Masha Allah naji dadin wannan lamarin insha Allahu bazan hana ɗana Kamalu gudan jinina ba se dai Mubina karatu take , tana da burin karatu kaga misali da anyi auran Allah ya kawo rabo da wuri idan cikin mai laulayi ne zai ɗatse mata karatunta , ko kuma ma daga baya mijinta ya hanata dan shike da ikonta , so sai nake ganin a bashi Amrah tinda ita ta gama ko gobe ma ashirye nake haɗa zuri'a dakai! Abubakar na ba Kamal auran Amrah idan yaso zata ci gaba da karatu ko aiki a gidanta." ya faɗa yana murmushi. Mubina ajiyar zuciya ta sauke ta kalli sharan Kamal ta cinno baki baki gaba ta lumshe idanunta ta tura kanta cinyar Mamu taji dadin jin ba ita bace ba!! Mamu kuwa haushin umpah ya cikata se hararasa take a ɓoye ga yarinya me buƙatar aure ya kasa ganewa ya bada watanta... Abbu cikin farin ciki ya isa gun umpah ya rungume shi yana godiya sosai da fatan Allah ya sanya alkhairi. Ummah ma da Hafsat da Samha sunji dadin samun Amrah a matsayin matar Kamal, dan sun fahimci tana da nutsuwa gashi abin kai tsaye taji amman taki nuna ɓacin rai sai kanta da ta sadda ƙasa. Kamal dauriya yake kurum sai yau yayi nadamar kin faɗa cewar ya sami wacce yake so, gashi za'a masa auran dole. Abbu ya zaro daurin ƴan dubu-dubu na dubu hamsin ya beƙama umpah yace"ga kuɗin tambaya mun gani muna so insha Allahu zamu zauna cikin satin nan a saka rana da kome wlh abun yamin dadi ban taɓa zaton kai tsaye zan samu karbuwa haka ba , Allah yabar zumunci."Umpah yace "Amin ni ke da godiya ni da ake son haɗa iri dani..." Haka suka kasance cikin farin ciki sosai kiran sallah ne ya tashi taron su Abbu suka tafi gida suma suka koma ciki...

Bayan sallah isha suka hallara gurin cin abunci, Amrah idanunta sunyi jajur taci kuka ta koshi a ɓoye. Yanzu ma sai juya spoon take ta kasa ci, Mamu tace"kici abuncin ki ni banga aibun yaron ba wlh ga hankali kiyi hkr..." Mubina ta ajiye robar ice cream ɗin ta bushe da dariya ta rungume Mamu tace"Kai Mamu nah gurgu ne fa yana ɗan ɗingisawa amman ai dole zata ma umpah biyayya.." Mamu ta buge mata baki, ta saki ƙara ta saketa ta koma wajan Umpah. Umpah ya kalli Mamu yace"Nusaiba wlh na fahimci kina nuna banbanci tsanin yaranan duka dai ke kika haifa kuma Amana Allah ya baki , ke Amrah kuka kikayi saboda na zaɓa miki miji na gari?" kinada tsayayye ne da zaki fitar? kuma inama zaki sami kyakyawan yaro mai nutsuwa irin Kamalu ga nera gashi yakai a so shi ki riƙe abinki da kyau." Amrah tace"A'A umpah bana kuka insha Allahu zanyi maka biyayya ina sonshi mana." ta faɗa tana danne kuka nata ta miƙe ta nufi sama. Umpah yace" yauwa Allah ya miki albarka."Mamu tace "Amin itako ta gaban ka se ka mata Addu'a Allah ya shiryata." umpah murmushi yayi ya shiga ba Mubina abunci a baki yace"Adawa bata yi ba wlh." Mubina tayi dariya. Ta miƙe ta haura sama.

Can gidansu Kamal haka suka kasance cikin farin ciki da walwala, amman banda Kamal. Misalin 12:pm na dare kwance yake a makeken gadansa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare idanunsa lumshe ya dafe kansa shi kaɗai yasan meke damunsa ya rasa me yake ji, yana jin zafin yadda ɗazu ya roki Abbu cewar ya masa alfarama yanada wacce yake so ya haɗa su su biyu ya aura, amman Abbu yaki yarda yace ko kusa da duk zamn sa bai ce yana da wada zai aura ba se da ya samo masa matar aure... Juyi yayi ya ɓeka hannuns na gefan gado ya janyo wayarsa ya sake kiran Amrah amman a kashe sakonta ya sake karantawa na cewar su hakura da juna an mata miji zatayi biyayya wa mahaifinta anman tana sonsa har karshen rayuwarta... Cillar da wayar yayi ya dafe kansa yace" Kina mace ma kin hakura bare ni namiji zan amshi kaddarata insha Allahu." ya faɗa yana buɗe idanunsa ya miƙe zaune ya sauke ya shiga toilet ya dauro alwalla ya fito ya dora jalabiyya kan kayan baccin sa ya hau saman darduma ya tayar da sallah nafina ta neman zaɓin Allah...

Amrah na kwance Mubina na manne jikinta se kwasar barci take a nuntse tana sanye da yar guntuwar riga ta bacci. Amrah ta rushe da kuka tace" Wlh ni KAK nake so amman dole zan amshi kaddarata zan mantaka insha Allahi." ta faɗa tana shasheƙar kuka ta rungume Mubina gam. Mubina kukan ya tayar da ita bude ido ta zabura ta riƙe Amrah tace "Anty lfy kuwa?" Amrah tace "Baby bari kiji abinda ke faruwa inada wani saura yi bayan Lameer daman kinsa shi ba sonsa nake ba , amman shi bamu taɓa haduwa ba ina sonsa yana sona yana nan maradi amman na masa karyar ina dosso , gashi za'a rabamu se dai fa ban taɓa ganin sa ba." Mubina taja tsaki ta sake shigewa jikin Amrah ta lumshe idanunta tace"Anty kiyi manage ki auri gurgu kawai kibar kukan idan bakya so zansan hanyar da zabin a fasa ta ruwan sanyi sai kima haduwar fecebook ɗin mgn ya fito." Amrah cikin murna tace"Ngd kanwata amman mubi kome a sannu se dai har na tura masa sakon mu rabu fa." Mubina tace"Hum ki bari zan san abin yi mu kwanta dare yayi." Nan Amrah ta rungumeta tsam suka kwanta ba jimawa Mubina ta koma bacci, Amrah ce ta ɗan jima kan tayi bacci...

*************** ******* ***************

*Bayan wata É—aya*

Zuwa lokacin an gama mgnr auran Amrah da Kamal an sanya wata biyu masu zuwa yanzu saura 38 cif auran su Ablah ta dawo tafi kowa murna, Mubina taɓara se abinda yayi gaba, se iskanci take ma Amrah wai an badata sadaka, amman tinda bata so zasu san abinyi, Amrah bata kulata dan tasan Kamal ya kai namiji, zuwa yanzu ta fara sabawa dashi tana jinsa a ranta sosai, sbd yana bata kulawa duk da baya kiranta ya kan zo ya saka megadi ya kirata su gaisa ya fice warsa dan Kamal da Amrah ba laifi yana ƙoƙarin zuwa zance babu yabo babu falasa suna ɗan gaisawa tana bashi girmansa.
Ɓangaran cutie angel shikam tin ranar da ta tura masa sako su hkr ya fasa kiranta, ya goge numbert duk da yana sonta bazai so ya zugata ta kasa ma iyanyata biyayya ba, idan ta kirasa ya kan ɗauka su gaisa amman baya kiranta ya tsaya inda mahaifinsa ya ajiye sa, duk da baya kiran Amrah ko numbert har yanzu baya da tinda se yafi sati bai zoba in yazo megadi yake sawa ya kirata. Mubina da Sageer sun shaƙu sosai ba laifi ko a makaranta sukun ɗan zanta ta saki jiki dashi sbd yadda yake bata kulawa da hira masu dadi, yanzu ta fita harkar Kamal sbd Jarabawar da suka fara ta rage iskanci sosai ta maida hankali a karatunta, ita da Basma kuma ko ba haka Kamal ya fasa ko kallan inda take baya kulata duk abinda zatayi baya kulata sabgar gaban sa yake, kasancewar ta zama kanwar matar da zai aura... Yau ta kama weekend ne babu aiki, kuma yau ne Kabeer zai sauka a garin maradi, da misalin 9: pm na dare idan kaga yadda Mubina ake shirye-shirye harda kitso da kunshi, kasancewar bata kitso sai wannan gamin ya mata wani irin kyau, haɗe da kunshi yarinyar ta hadu sosai, tin safe bata zauna kome siya masa take, ta matsu dare yayi, haka Amrah ma...
Chapter 24 · 0% Book details