← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 124

Sashe 62

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat tace" goggo inada mgn dake zanzo zuwa jibi yanzu na fito gobe bazan fito ba." Safiyya ta share kwalla tace"Koma meye ake ɓuye min Allah ya baiya na mana shi kawai." Ummah tace" Kai Safiyya wlh bansan inda yake ba taya zan ɓuye maku wlh ban saniba , sai de ko Abbu dan wlh nafi zargin shi ya tura sa wani wajan, kuma ai bazaki ce an ɓuye maki ba ina ce kinsan kome yarinyar yanzu haka cikine da ita ko, ai ko wannan ya isa yasa yabar gari da ƙafar sa..." Hafsat tace"wace yarinya kuma?" Safiyya tace" Mubina wacce ƙaddara ta afka masu mana..." Goggo tace"No Safiyya abar mgnr Hafsat bata san kome ba." Hafsat tace" Tom goggo gaskiya dai a barta kar ta ɓatamin ma rai kowa ya riƙe sirrin sa." Goggo tace"wane sirri?" Hafsat tayi murmushi tace"Ni kam zan wuce yanzu ma wani aiki ya kawoni, Aunty ki gaishe min da Abbu Suhailat gobe sai Kebbi ko, Aunty Safiyya sai kin shigo ko , Samha tana makaranta ko?" Safiyya tace" Wai anya Hafsat ba kina tare da Kamal ba kuwa...?" Hafsat ta miƙe tace"A'A ni kuma, ni dai kunga tafiyata." ta faɗi tana barin parlon. Ummah tabiyota rakiya tana cewa". Hafsat ki gaishe min dasu Ameer da Abban su." Hafsat tace"Tom Aunty." haka ta rakota har harabar gidan, ta shiga ƴar ƙaramar motar ta mai kyau taja ta nufi get, Ummah ta koma ciki tana tunanin anya ba Hafsat nada lbrn Kamal ba kuwa...?

Kwance *Kamal* yake saman royal bed ɗinsa, yana sanye da jallabiya fara sul, wani ni'imataccan ƙamshi ne ke tashi jikinsa, haɗe da ɗakin baki ɗaya, ga sanyi Ac me daɗin gaske. kyakyawar fuskarsa na ɗauke da alamun damuwa, dan se sauke katuwar ajiyar zuciya yake, akai akai lumsassun idanunsa sunyi ɗan Ja kadan se lumshesu yake yana buɗewa yana feso iskar bakinsa waje. Hannunsa ya dora saman kwantacciyar sumar kansa, yana cacakuɗa sumar, a hanakali kamar baya son mgn yace"Mmn Babyna pls ki buɗe wayarki pls *Mubee* ina kika shiga ne tin jiya ne? Oh my god." ya faɗi da dan karfi yana jan sumar kansa. Miƙewa zaune yay ya sauko daga saman bed ɗin, ya nufi saman darduma ya hau ya zauna, ya buɗe Alqura'ani me girma, kenan zai fara karatu yaji wayarsa ta ɗauki ringing, da sauri ya ajiye Qura'an ɗin yaji daɗin bai rigada ya fara karatun ba.!! Ya miƙe ya nufi gun wayar, bakinsa ɗauke da Addu'a Allah yasa Mubina ce. Yana isa bakin gadon ya ƙurama wayar idanu, ai kuwa yaga sunan *Mmn Babyna* yana yawo saman screen ɗin wayar, cikin kuzarin sa yay saurin ɗaukar wayar tana dab da yankewa, yay picking ɗin call ɗin cikin farin ciki maras musaltuwa, ya manna wayar a kunnensa, yana zama bakin gado, ya watsa mata sansanyan murmushin da yasan tana muradi, haɗe da kiss, "MuAhhhhhhhh." yay mata.

Mubina wacce take naɗe cikin blanket, ta lumshe idanunta haɗe da miƙa, ta sakar masa kuka tin karfinta, tana cewa"My Deen kana jini?" Kamal rumtse idanunsa yayi da karfi zuciyarsa na bugawa da karfin gaske tamkar zata fasa kirjinsa ta fito, haka yakejin zafin kukan nata, gashi babu halin yayi mgn, se ya tsinke kiran. Yay saurin tura mata sako kamar haka *Sorry Mubee don Allah kibar kukan haka yana taɓamin cuciyata yi hkr faɗamin damuwar ki bari na kiraki yanzu.😫*

Mubina tana ƙoƙarin sake kiransa taga sakon, tana gama karantawa kiransa ya shigo, take ta ɗauki kiran ta maida wayar kunneta, ta sake ajiyar zuciyar. Kamal ya hura mata iskar bakinsa ta wayar yana sauke ajiyar zuciya. Mubina ta gama gano ita yake jira ta share hawayen fuskarta ta shagwaɓe murya tace"My Abokina wlh na yarda dakai zan faɗa maka sirrina amana ka bani shawara pls kaji abokina?" Kamal ya sakar mata murmushi mai cike da mugun tausayinta tare da mata kiss. Mubina ta shiga ƙamƙame jikinta ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya tace"Deen bazaka dawo Niger ba ni kazo kaji." ta faɗa a shagwaɓe. Murmushin ya kuma mata. Mubina ta gyara kwanciyarta idanunta a lumshe fara ba Kamal labarinta da Kamal fyaden da ya mata, ta irin rashin lafiyar da take, har zuwa jiya da taji tanada ciki, da irin hukuncin da suka dauka sbd baya son cikin ita kuma tace se ta haife sa gobe ma zasu wuce London dan ya dawo gari yana nemanta ruwa a jallo ya zubar mata da ciki.

Har Mubina ta gama ba Kamal lbr kuka yake a ɓuye cike da tausayinta da tausayin kansa, da kuma murnar ta hkr zata haihu wai dan kuntata masa bata san cewar wayo iyayanta suka mata ba yaji daɗin cewar Abbu nada lbrn cikin kuma adukan alamu suna sonsa ɗan, tace tare da Baban kwarto za'aje London a ɓoyeta, gun ya basa dariya sosai amman babu damar yin dariyar.
Muryata ya tsinto tana cewa"Abokina se anjima zan dan fita gidan su ƙawata tinda bazaka bani shawara me kyau ba." ta faɗa a sangarce muryata na rawa tana shirin masa kuka.

Kamal ya tsinƙe kiran ya tura mata sako kamar haka, ```Sorry Baby Mubee nah ta ni kadai da Babynmu insha Allahu, ina cikin rudune wlh ina mugu mugun tausaya maki kuka nake sosai bansan me zance ba! amman yanzu kince zaki fita to kije idan kin dawo zan kiraki na baki shawara me kyau, amman da sharaɗin zaki yafe ma Abban Abubakar Sadeeq ko Fatimazahra, so zan faɗa maki yanda zamu gasa dan kurma se baƙin ciki ya kashe sa ma baki ɗaya,kuma don Allah kibar yawon motsa jiki ki kula da yaron cikinan ɗan kurma na mugun son cikin sosai Wallahi, bye se kin dawo nima na kashe wayata dan karki dameni da tambaya karatu zanyi bye me ciki Nide ina son babyn nan sosai.😜😜😜 ``` Haka ya tura mata yana murmushi me haɗe da kuka hawaye na zubowa kan fuskarsa, ya kashe wayar baki ɗaya, ya miƙe ya shiga toilet.

Mubina kuwa tana ga sakon ta saki kukan sangarta tana cewa"Allah ɗan kurma bazan yadda ba karka kara cemin me ciki kuma se ka faɗamin ina kasan baban babyn ne harda wani saka ma yara suna ni de bana son cikin Kamal sam , kuma kaima ka dena son cikin ko mu ɓata." ta faɗi tana dailing ɗin number Kamal, amman switch off. Lips ɗinta ta ciza ta miƙe ta sauko daga saman gadon ta ahiga bathroom.

After 30 minutes

Mubina ce ta fito cikin shiri tana sanye da Abaya red da mayafinta, sai takalmunta mara tudu, sai wayarta a hannunta, tayi kyau matuƙa sai de bata sanya turare ba.! Mamu zaune a parlo Amrah tayi matashi da cinyarta, suna mgn akan Lameer naso ya turo iyayansa tambaya. Mubina ta ƙaraso ta zauna kusan Mamu ta dora kanta saman kafaɗarta. Mamu ta shafi fuskarta tace"Autana ina zuwa akayi kwalliya keda kika gama amai ba jimawa.?" Mubina ta shige jikin Mamu tayi lamo can kamar bazatayi mgn ba! A hankali tace"Zan je gidan su Basma ne a ƙafa na motsa jikina inajin kasala sosai, ai naji dama ɗazu mukayi waya da Sageer yace a gaishe ku." ta faɗi tana rungume Mamu tana ture Amrah. Amrah zatayi mgn wayarta ta ɗauki ringing, ganin Lameer yasa ta miƙe tana murmushi tai picking ɗin call ɗin ta manna wayar a kunnenta, tabar parlon. Mubina ta bita da kallo tana taɓe baki. Mamu tace"Ok muna amsawa, amman karki dade kinji baby." Mubina ta ɗaga kai ta mannawa Mamu kiss a kumatu ta miƙe tace"Bye Mamu Ablah na barci ko?" Mamu tace"Eh baby bye ki gaishe min da Lubah."Mubina bata sake mgn ba ta fice a parlon tana tafiya cikin sanyin jiki.Tinda ga nesa Haladu ya hango Mubina yana washe baki, yace"Baba megadi gafa sarauniyar marasa kunya an fito, amman naga duk tayi sanyi makarantar ma bata zuwa." Baba megadi yace"Bana ciki da gulma Haladu." dariya Haladu yayi ya miƙe yace"Bari na tashi maybe gari zan kaita." dede lokacin Mubina ta isa kusan su, tace da baba megadi," Baba ina yini." bata jira amsar saba ta wuce.
Baba megadi ya amsa yace"Mubina fita za'ayi a ƙafa ko?" Kai ta ɗaga bata juyo ba. Haladu yaci"Hajja Mubina ina yini." Murmushi tayi ta buɗe kofar ƙaramar get ta fice bata kulashi ba. Dry Haladu yayi yace"Yau ba marasa kunyar bane ba wlh." baba megadi baice kome ba dai, ya jinjina kai.

Hafast kuwa tinda ta fito take shawarar ta shiga gidan su Mubina ta kasa dan sun santa amman Mubina bata santa ba.!! Shawara ta yanke ta shiga kawai, get É—in ta nufo da motar, tana dab da isa get É—in se taga Mubina ta buÉ—e get ta fito
Tsayawa tayi tana kallon yarinyar kyakyawa fara siririya, " masha Allah ni se yau na ƙare mata kallo ƴar balarabiya." Hafsat tace.
Mubina kuwa tana fitowa ta fara tafiya a nutsu ita ko motar ma bata lura da ita ba! Tana É—ago kanta da ta kalli get É—in gidan su Kamal sai taj

i muguwar faɗuwar gaba, da karfin gaske, ta tuna ance yazo gari dan ya kamata ya zubar mata da cikinta. Wani irin mugun tsorone!! ya kama Mubina take jikinta ya ɗauki ɓari ta juya a mugun tsorace!! da gudu ta nufi get ɗin gidan su jkinta na ɓari, ganin mota dab da get ɗinsu ta kara shiga tashin hankali, bakinta na rawa tace"Ka...mal... ne... Wan...nan... Zai... saceni...." ta faɗi tana fashewa da kuka ta ƙara gudu amman bata lura ba sai ji tayi ta faɗa jikin mutum, ai take futsarin da take riƙewa ya kufce ya fara bin cinyoyinta....
Real Ladingo ce😜

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣6️⃣
Chapter 62 · 0% Book details