← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 124

Sashe 15

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mubina ko sallama ba tayi ba ta fado parlon. Basma ce tayi sallama. Amrah na zaune ta dora kanta jikin Mamu suna hira su ta uwa da É—iya.
Mamu ta amsa sallamar tace"Oyoyo ƴan matana sannun ku." Mubina ta fado jikin Mamu ta ruƙunƙumeta gam ta saki kukan shagwaɓa. Mamu da Amrah suka riƙeta suna tamyarta" Baby yau kuma keda wa har ta saka mana ke kuka?" Mubina ta shige jikin Mamu tana shasheƙar kuka taki magana. Amrah ta rungumota tace" Ki faɗa mana ke dawa?" Basma ta zauna tace Aunty Amrah ba maca bace ita da Sir Kangiwa ne tai masa laifi shine ya haɗamu ya mana hukunci amma ita harda mari..." Amrah tace"Kan uba saboda me zai mareta horanta aka bashi? Waye kangiwar?" Mamu tace" Baby kin masa ɓarna ne ko ko kuwa rashin kunya?" Mubina ta janye jikinta daga na Mamu tana kuka tace"Ni ban masa kome ba kawai ya kware wajan iya zalumci ne , har fa ruwan toilet ya dura mani..." Mamu ta kalleta da sauri tana zare idanu dan yanzu kuma ta gama gano ƴarta harda karya ta feso. Mubina sama ta haye tana rere kukanta. Amrah ta miƙe ta bita a baya, Mamu tace" karki je ta haukace ma mutane har uban yaji barta zan lallaɓata , zo zauna ." Amrah ta dawo ta zauna tace" Basma ki faɗa mana abinda kika sani idan ya kamata umpah yaji yaje ya masa magana tinda ba horo ba aka bashi ba." Basma tace"Aunty gaskiya umpah ya sani fa ta faɗa masa kome har Ablah ma taji kuma mune bamuda gaskiya..." Nan ta zaiyane masu kome da Mubina take ma Kamal a cikin class.
Mamu ta zaro idanu ta rabka salati ta fara tafa hannuwa, tace" abinda kuke kenan a makarantar ko? Ai kuwa wlh kadan ya mata da yaci ƙaniyarta ne Baby bata ji." ta faɗa tana tagumi. Amrah tace" Baby bataji gashi umpah yaji harda Ablah nasan kuwa zugashi zatayi tace a kwato mata hakkinta..." Mamu tace "No zan faɗa masa gaskiya abinda Basma ta faɗa , se dai marin da ya mata yayi yawa gaskiya naji abun har raina , bana son na nuna mata ne ta kara narkewa ." ta faɗa tana miƙewa ta nufi kitchen. Basma miƙewa tayi ta nufi saman bene gun Mubina. Mubina tana hawa sama ta cire kayan jikinta tin a kofa tayi zigidir ta shiga bathroom.
Tana zuwa ta cika bath ta zuba sabulu me kamshi na ruwa ta shige ciki ta lumshe idanunta ruwan na ratsata, tana ciza lips ɗinta nippels ɗinta ya buɗe yayi wani irin tsine se tagwayen ajiyar zuciya take saukewa, tana mimmiƙewa a cikin ruwan hawaye na sintiri saman fuskarta, ta tura hannunta ɗaya cikin lallaunsa gashinta wanda ya jiƙe da ruwa tana cakuɗawa, tana ciza lips ɗinta, cikin sanyin murya me haɗe da ƴar shasheƙar kuka tace" Allah ya isana ya Allah kabi min hakkina insha Allahu bazan sake kula gurgu ba tinda shi bayada imani da tausayin mace , na tsaneka zanyi ta Addu'a Allah ya maka abinda ka min mugu ɗan iska kwarton banza... Wlh ka guji ramuwar gaiyya zaka shiga kunci ɗan gurgu kawai , wlh na tsaneka fiye da mutuwata..." bugun kofar da Basma tayi ma kofar toilet, yasa Mubina yin shiru ta bude shanyayyun idanunta wanda suka rune sukayi jajur saboda jaraba, ta miƙe da sauri ta fito daga cikin ruwan ta tsaya gaban shower ta kunna madanin shower ɗin ruwan na zuba tsakiyar kanta, kunsa 5 munites ta kashe tayi alwalla ta janyo towel ta daura a jikinta ta dauki karamin towel ta daure kanta ta bude kofar ta fito.
Basma na zaune bakin gado, ido suka haɗa da Mubina wacce tayi kicin-kicin da fuska tana zumburo baki. Basma ta miƙe tana danne dariyarta tace"sannu Mubee ya naga kinyi kuka? Bari nayi alwalla nazo na wuce gida." ta faɗa tana shiga bathroom. Mubina ta goge jikinta ta busar da gashinta ta shafa masa mai me kamshi ta ɗaure shi da ribbon amma taki yarda ta kalli madubu ta murje jikinta da maiyuka masu sanyin dadi da taushi, ta nufi wardrobe ɗinta ta buɗe ta kurama uban tulin kayan idanu, ta yamutsa fuska ta beƙa hannunta ta janyo wata Abaya red me masifar kyau tasha adon duwatsu, saman a matse ƙasan ya dan buɗe kadan ta zaro mayafinta ɗan guntune bayada girma ta cire towel ɗin ta yada shi ƙasa, har zata saka rigar taji breast ɗinta na masifar ƙaiƙayi se motsi yake, tsaki tayi ta ciro bra ta saka se lumshe idanu take ta saka Abayar, wow nace Sbd tayi mata masifar kyau ta kamata daga sama sosai kirjinta kamar ya fasa rigar ya fito ƙasan ya dan buɗe amma kuma daga ƙugunta ya ɗan kamata hips ɗinta ya fito, tayi masifar kyau ta nufi kan Dreesing mirorr ta dauki turarenta mai sanyin dadi ta fesa ta yane kanta da ɗankwalin. Basma ce ta fito ta isko Mubina saman dadduma zaune da Alqura'ani a hannunta tana karatu cikin zazzaƙar muryata tana karanta suratul Yasin. Basma gun jakarta ta nufa ta buɗe ta zaro wayarta ta duba taga lokacin sallah yayi an taso juma'ah, ta ɗauki ɗayar dardumar ta shimfiɗa ta tayar da sallah.
Umpah ana tashi daga masallaci nan suka hadu da Abbu yake bashi labarin abinda wani malamin su Mubina ya mata har da ruwan toilet ya bata, karan sa zai kai. Abbu ya jajanta yace su wuce Company gurin Kamal yasan yana can yanzu, Kamal ya sami malamin yaji dalili akan me zai mari karamar yarinya har mari 13 da bata ruwan toilet daga can idan sun faɗama Kamal ɗin, kila ya san malamin daganan suje kawai police sitetion ɗin, suyi karansa, shine fa direct sukayi Company, daga can suyi police sitetio a basu yan sanda a tafi da Mubina ta faɗi abinda malamin ya mata a hukuntashi...🤔
Mubina tana gama sallah tace da Basma " Tashi muje gidan ku daga can zan shiga a dedeta na tafi gidan Baffa Inusa a can zan kwana yau." ta faɗa tana lumshe idanu. Basma ta ɗauki jakarta tace"muje kalli mom se kirana take wlh." ta faɗa tana tafiya. Mubina bata sake magana ba ta ɗauki wayarta ta kashe ta kaita ƙasan pillow ta ajiye. Amrah da sauri ta sallame tace"Baby ina zaki a haka kalli yanda idanunki suka yi Ja ki kwanta mana." ta faɗa tana miƙewa ta rungume Mubina ɗin. Mubina tace" eh yanzu zan dawo ai rakiya zanyi in dai baki ji me nace ba." ta faɗa tana janye jikinta daga na Amrah ta mata kiss a goshi tace" se na dawo." ta kama hannun Basma suka fito. Parlon ba kowa se wayar umpah na ta ringing, Mubina tayi saurin ɗauka tai piciking ɗin call ɗin ta kama hannun Basma tana cewa"Mamu idan kin fito na raka Basma gida a ƙafa zamu fita tinda ba nisa." ta faɗa tana manna wayar a kunneta suka fice daga cikin parlon.
Kamal ko lokacin da aka gama sallar, hospital suka nufa shida Sageer yaga wata mata wacce take fama da ciwon zuciya ga
basuda kudin aikin da za'a mata nan yasa hannu akan zai biya kome, duk da Sageer yace zai mata, daga nan sukayi sallama cewar zasu haÉ—u 5 pm akwai hira ta musamman.

Mubina suna fitowa ma'aikatan gidan suna gaisheta da jiki da mamakin maras lfy ce taci kwalliya haka? Mubina banza ta musu suka fice a ƙafa, tinda gidan babu nisa sosai titi kawai za'a tsallaka, suyi ƴar tafiya.
Tafe suke cikin nutsuwa Mubina jikinta sai motsawa yake masha Allah, tamkar tarwada hips ɗinta ya fito, ɗuk da ta rufe dede kirjinta da ɗan gyalan amma hakan bai hana tudun nonuwanta fitoowa ba kallo ɗaya zaka mata kasan Allah ya mata manyan nonuwa masu lafiya. A cikin nutsuwa yake driving waya manne kunnansa yana sakin ƙayattacen murmushi, cikin amo murya sa me daɗin sauraro yace "goggo nah wlh bacci ne cike da idanuna gani nan na kusa isowa fa bazai wuce tafiyar 3 munites ba , a kunna min daddɗan turaren wutar nan fura kada a sa min ƙanƙara wlh mura nake ji tin jiya , bye se na iso." ya faɗa yana tsinke kiran. Ya karya kwanar titin ya tsinkayo su Mubina, suna tahowa kallo ɗaya ya mata ya ganeta saboda face ɗin motar sa suke tahowa, yanda take takunta cike da jiji da kai se dai fuskarta ba walwala waya manne a kunneta tana mgn, ga takalmin ƙafarta da tsini, kirjinta se kaɗawa yake, hips ɗinta ya fito, se kallan baiwar kyanta jama'a suke, wani matashi na biye dasu a mota. Kamal ya zaro fitinanun idanunsa, yace"Ikon Allah wannan yarinyar ashe har yawon banza take haka wai ina iyayanta ne? Suka barta ta lalace gata jarababbiya , basa tsoron ta ɗauko masu abin kunya , kai Allah ka shiryemu amma nan babu tarbiyya bari kiga na hargitsa miki lisafi tinda baki san waye ba bare ki ɗauki fansa , masifafiya zakiyi zawo yanzu , muga karya tafiyar iskanci bari na fanshe ɓarnar da kika min." ya faɗa ya sakin murmushin mugunta ya saki hanya yay kanta a guje. Basma ta fasa ihu tace"Mubina kauce mota..." Mubina ganin mota tayi kansu ta fasa uban ihu! tace"Ablah hatsari..."ta saki wayar umpah ta faɗi ƙasa jikinta na rawa........

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*
*💖😭KAMAL NE😭💖*

_*Book 1*_

_NA_

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

_Ƴar Mutan Niger_🤙🏻
Chapter 15 · 0% Book details