Sashe 53
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamal ya lumshe tsumammun idanunsa, ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, yace"Momy wlh kema ba lallai bane ki fahimceni amman insha Allahu zan faɗa maki, zuwa gaba yanzu zan tafi gun karatu se karfe 12 pm na dare zan dawo." tace "Ok kaci gaba da bautar Allah kana kai kukan ka wajan Allah insha Allahu kome zai zo da sauƙi."
Kamal yace
"Ok Momy se munyi waya gobe idan ko ban kira ba se zuwa jibi bye." ya faÉ—a yana tsinke kiran, ya ajiye wayar ya sake É—aukar É—ayar wayar.
Kiran Sageer ya shigo, da sauri Kamal yay picking É—in call É—in, ya kata a kunnensa amman bai yi mgn ba. Sageer yace"Wai don girman Allah waye ne? Se akira ba mgn?" Kamal baice kome se. Sageer yace"Baza ayi mgn ba?" shiru ba'ayi mgn yasa ya tsinke kiran yana jan tsaki.
Murmushi Kamal yay ya fara tura masa sako kamar haka, ```Dr Sageer kana kula kuwa da masoyiyar ka Mubina? Ya kamata yanzu ba anjima ba, kaje ka dubata sbd bata jin daÉ—in jikinta... ``` yana turawa ya kashe wayar baki É—aya ya ajiye ya nufi wajan darduma ya É—auki Alqura'ani me girma ya fice daga bedroom É—in.
Sageer zai ajiye wayar yaga sako ya shigo, ya buɗe ya karanta ya zaro idanu yace"Wai waye wannan ne? Taya mutumin dake Saudiya naga number Saudiya, har yasan Babyna ba lfy ne ni ban sani ba?" ya faɗa yana kiran number amman a kashe. Number Mubina yay dailing. Mubina kuwa lkcn ta gama sallah kenan ta magarib tana kwance saman Sallaya, dan bata jima da tashi daga bacci ba. Jin ringing ɗin wayarta yasa ta buɗe shanyayyun idanunta ta kalli gefen da taji ƙaran wayar, ta kalli jakar dan rabonta da jakar tinda ta zo daga school bata sake kallon ta ba.
Zaune ta miƙe tana yamutsa fuska, ta kasa tashi ta ɗauko wayar, baki ta zumburo gaba can ƙasan makoshi tace"Allah ni bazan tashi ba yo kai kurma baka mgn nice zan tama zuba zubar surutu, to ni banida lfy." ta faɗa tana kwanciyarta ta ƙudundune cikin hijab, ta lumshe idanunta, tana jin wayar har aka mata kira 5 bata tashi ba.
Sageer ganin ya kira Mubina har sau 5 bata ɗauka ba, yace"Oh my god ko dai Baby bata da lfy da gaske ne? Bari naje nayi sallah isha naje na dubata baiwar Allah." ya faɗa yana fitowa parlo, yana kiran Nini ba kowa sai Najwa ƙanwar su Sageer autar su ƴar buduwar, zata kai 14 year. Miƙewa tayi tana murmushi tace"Yaya Sageer wai ina Yayana Kamal ne? gaskiya nayi missing ɗinsa sosai?" ta faɗa a shagwaɓe. Sageer yace"Ke ina Nini ne?" Najwa tace"tana ciki ai se tayi isha take fitowa, ya naga ka dawo kabar Abba a masallaci ne?"Sageer yace"Ban saniba ki ce mata daga masallaci zan ɗan jima ban dawo ba hospital zan wuce." ya faɗa yana ficewa a parlon. Tace" Ka gaishe min yaya Kamal pls." Sageer bai saurareta ba ya fice zuwa masallaci. Najwa ta zauna tana kallon Tv...
```Yauwa don Allah kumin Afuwa ranar da Kamal yazo gidan su Sageer, nace Sakina nayi mistcke ne ba Sakina ba ne Najwa ce ƙanwar Sageer Sakinan ƙanwar Basma ce...```
Mamu tana gama sallah isha ta fito parlo ba kowa, ta zauna tana danna wayarta, se ga Amrah ta fito daga kitchen tana waya, zata zauna Mamu tace"Ke kira min Baby naji jikin nata É—azu naji akwai zafi da muka dawo." Amrah ta nufi saman bene tana waya. Mamu ta bita da kallo tana girgiza kai.
Kabeer ne suka shigo da umpah bakinsu dauke da sallama. Mamu ta amsa. Kabeer ya zauna kusanta yana kwantowa jikinta. Umpah yace"Ina Babyna ya jikin nata? Wai me ke damunta ne?" Mamu ta bugi Kabeer a kafaɗa tace"ɗagani katon banza se kace Mubina." dariya Kabeer yayi yana sosa kansa. Mamu tace"Wlh ɗazu naji jikin nata da gumi fa na tura Amrah ta kirata naji..." Umpah yace"Bari naje naji da kaina idan da zafi mu tafi hospital." ya faɗa yana nufar saman benin. Mamu tabi Umpah da kallo tana cewa"Baban Mubina ba..."Kabeer yayi dariya yace" Baby fa shagwaɓa ce kawai." Mamu tace"Auta ba wasa ba ai."
Mubina tana kwance Amrah ta shigo, tana waya se murmushi take saki ta zauna gefen gado, ta kalli Mubina tace"Baby Mamu na kiran ki taji jikin naki." ta faÉ—a tana kallon Mubina. Mubina
ta buɗe idanunta tana turo baki tace"Ni lfy ta lau kawai a sayo min agwalima yanzu nasha shi kaɗe nake so." ta faɗa tana miƙewa ta tayar da sallah isha'i.
Amrah zatayi magana umpah ya shigo da sallama, ganin Mubina tana sallah yace"Alhmdllh Baby, Amrah jikin ta ba zazzaɓi ko?" Amrah ta tsinke wayar tana dariya ta mike ta nufo gun Umpah tana cewa"Umpah lfyr ta lau wai agwaluma take so..." Umpah yace"meye haka nan ɗin? Ana samin sane nan kusa?" Amrah tace"Eh nan kusan mashin masara ma ana samu." Umpah yace"to muje a siya mata soyene ko me miyane?" Amrah ta bushe da dariya ta kama hannun Umpah tace"Ba abunci bane ba Umpah wani abune kamar gwaba se tsamin tsiya fa..."Umpah yace"Bari de ta idar da sallah se muje ta zaɓi abinda take so." ya faɗa yana isa bakin gadon yana riƙe da hannun. Amrah suka zauna. Mubina tana gamawa ta miƙe tana lumshe idanunta, ta nufi gun Umpah, ta faɗa jikinsa ta lafe luf. Umpah ya taɓa wuyanta yace"Baby sannu naji jikin da zafi tashi muje hospital..."Kukan sangarta ta saka masa tace"Umpah bajin zazzaɓi ni a sayo min agwalima nasha yanzu bana jin yunwa naci taliya kusan magarib." ta faɗa cikin shasheƙar kuka. Umpah yace,
"Ok Baby yi shiru tashi muje ki zaɓo da kanki ko." Mubina ta janye jikinta tana hamma tace"Ni Umpah kuje da Aunty tasa gurin ai, kwanciya zanyi." ta faɗa tana faɗawa saman bed tana ma Umpah murmushi. Umpah yace"yauwa ƴar albarka kwanta abinki kinji." kai Mubina ta ɗaga tana kallon su suka fice, da Amrah. Suna fita ta miƙe zaune ta sauko ƙasa ta cire abayar jikinta cillar ta shiga bathroom ta sakar ma kansa shower.
Mamu suna suna zaune ita da Ablah da Kabeer, su Umpah suka sauko. Mamu tace"Ina Mubina ɗin?"Umpah yace"da sauƙi ta kwanta ne, bari zamu sayo mata abu muzo."ya faɗa yana kallon Ablah.
Ablah tace"Ai bata jin yunwa ɗazu taci taliya da yaji ba kadan ba, Nusaiba je ki fito da ita." Amrah tace"Ai ba abunci bane, Umpah muje."ta faɗa tana kama hannunsa suka fita, Kabeer ya miƙe ya bisu yana cewa"Umpah bari nayi rakiya, daga can zan sauka gun wani abokina zamuyi hira kadan , Mamu kar ku jirani kuƴi lunch fa." ya faɗa yana ficewa ya bisu suka fita.
Mamu tace"Ablah taliya Mubina taci da yaji kuma?" Ablah tace"Eh kome ai marmari ne, tashi ki janyota ku fito." Mamu tace"Nayi mamaki ne Baby bata son yaji, bari na lekota."ta faɗa tana miƙewa, haka kawai taji gabanta yana faɗuwa, ta nufi saman benen.
Ibrahim kuwa bayan sunyi sallah, direct gidan Hafsat ya nufa. Yana zuwa ya kirata yana bakin get, da kanta ta fito ta sayo sa ciki. Bayan sun gama gaisawa yace"Ina Maheer ɗin kuwa?" Hafsat tace"Kai yaya Ibrahim jiya ko nace ma yayi tafiya fa se sun kwana biyar, dagani se yara..."Ibrahim yace"Ok anyi haka, Hafsat don Allah temako zaki min, domin ceto ɗanmu daga wata mummunar kaddara da ta fada masa, wacce nasan tabbas makirci ne aka shirya masa, dole amman mu ɗin iyayansa ne, sbd ƙannin mahaifinsa ne, don Allah kinsan inda Kamal yake? Ko kuma ya faɗa maki komai?" ya faɗa yana kallanta. Hafsat tace"Yaya ni babu abinda ya faɗamin amman tabbas nasan inda yake ko ɗazu munyi waya, amman yace kar na faɗawa kowa amana ce, se dai zanma alkawalin lallaɓashi ya faɗamin me ya faru haka har yaya Abubakar ya kore shi daga gida."" Ibrahim yace"Good yayata ta kaina Ngd sosai ki lallaɓashi ki samo mana lbr yanda zan tarwatsa mikiyan ɗana."Su Ameer sukayi dariya suna cewa"Uncle waye makiya?" Ibrahim ya miƙe yana murmushi yace"Hafsat zan wuce, kai Ameer kuzo muje Haulat na neman abokin wasa."dariya sukayi suka riƙe shi suna dry. Hafsat tace" ku sake shi maza, iyayan son yawo." sakin sa sukayi suna ɗry, Hafsat ta ja yaranta suka raka shi har kofar get, seda ya shiga mota ya tafi suka dawo ciki.
Mubina bayan ta gama wankan ta fito ɗaure da guntun towel a jikinta, yawu na taruwar mata ga tashin zuciya ta rasa ya zatayi, ta goge jikinta taje gaban dreesing mirror ta murje jikinta da maiyuka masu laushi da daɗi ta nufi wardrobe ta buɗe ta ciro rigar bacci doguwa me santsi ta saki towel ɗin ta saka riger, ta mata das gwanin kyau, ta ciri rigarta me ƙamshin da tafi so ta nufi toilet ta zubar da yawu ta dawo, saman bed ta fada taja blanket ta lulluɓe jikinta ta rufe fuskarta da rigar tana sunsunawa tana lumshe idanunta. wayarta ta ɗauki ruri, ido ta buɗe cike da kasala ta janye blanket ɗin ta beƙa hannunta ta janyo jakar ta zuge zip ɗin ta ciro wayar, taga sunan Sageer na yawo, fuska ta yamutsa tai picking ta kara a kunnenta a shagwaɓe tace"My one" Sageer yace"Baby fito maza na ganki me yake damunki ne?" Mubina ta turo baki tace"My one to waye yace bani da lfy? Ni ba abinda ke damuna fa."ta faɗa a shagwaɓe, tana diddira ƙafafunta. Sageer yay murmushi yace" Uhm Babyna, oya fito yanzu, harda abin dadi na kawo maki fa..." Mubina tace"Ni ba wani wayone kake min fa" ta faɗa tana ɗaukan hijab kato har ƙasa ta zura. Sageer yace" Wlh kuwa ba wayo bane Babyna." ya faɗa yana murmushi. Mubina zatayi mgn Mamu ta shgo da sallama taga Mubina da katon hijab har ƙasa, tana tsaye waya manne a kunnenta. tace"Mubina ya jikin naki? Zo muji." ta faɗa tana isa gun Mubina. Mubina ta ciro wayar daga kunnenta ta tsinke kiran, ta faɗa jikin Mamu ta rungumeta gam tana murmushi tace"Mamu nah Sageer ne fa yazo bari naje nazo." ta faɗa tana ɗago da kanta tana kallon Mamu tana murmushi.