← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 124

Sashe 104

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Umaimah tace"Kan uba haka ya kwaso karuwar balarabiya zama tsirara? salon ki sacemin zuciyar masoyi." ta faɗi tana isowa dab da Mubina ɗin ta tsaya. Raihana ce ta shigo tana cewa"Wow Aunty balaraba tayi kyau..." Umaimah ta lailayo zagi tama Raihana, ta beƙa hannun ta kama gashin Mubina taja da ƙarfi Mubina ta buɗe idanunta cike da bacci tana riƙe gashin ta ɗago kanta sukayi idanu huɗu da Umaimah, manyan idonta ta waro tana kallonta. Umaimah da hausa tace"Ke!! Mayya ki rabu da Kamal ba sa'anki bane, me zaiyi dake mace a bushe ba tsoka sai shegen nonuwa da kyau da wani hips ɗin banza, to wlh ki kama kanki Kamal nawane..." Mubina fizge gashinta ranta na masifar suya ta danne ta saki murmushi da harshn larabaci tace"Me kika ce yimun yarena, ta faɗi tana miƙewa tsaye ta kalli Raihana tace" je ki ɗaukomin ruwa a can part ɗinku." Raihana da gudu ta fice Mubina ta cira kenan Umaiamah ta fizgota tana huci tace "Ke!! Mayya me yasa kika nacewa Kamal dan jaraba baya sonki ya aureki bayan ni yake mutuwar so nima ina sonsa kamar raina zan iya kome kan Kamal..." Mubina rumtse idanunta tayi da karfin gaske tanajin zuciyarta kamar zatayi bindiga, jikinta ya ɗauki rawa wani irin mugun ɓacin rai ya ziyarceta wanda ita da kanta tasan idan bata aikata ƙuɗirinta ba zata iya rasa ranta...... Cikin fizgo numfashinta wanda yake ƙoƙarin barin gangara jikinta ta jefa idanunta cikin na Umaimah, wacce kallo ɗaya tama Mubina, gabanta ya faɗi ta ɗauke kanta saboda bata taɓa ganin idanun mutum suna jajawur hakaba, kamar garwashin wuta. Wani irin sihirtaccen murmushi Mubina ta saki, ta baza maroon gashinta ya sauka har kusan gadon bayanta ta gyara tsayuwarta ta harɗe hannayenta, a saman ƙirshinta, tana kallon Umaimah. Wacce take shawara da ƙoƙarin zambatar Mubina ɗin ta tisge gashin kanta taci ubanta, kafin mijinta ya dawo ta nakasata. Mubina ta gama gano ƙudirin, Umaimah na son kawo mata hari, Mubina ta ƙara ɓoye hannayenta, a ƙirjinta da sake ba Umaimah damat ƙudirinta, tace Ma Umaimah " Ƴan mata mai cikar halita, ke A ganinki kamar Haɗaddɗan Namiji mai cikar halita, kyakyawa ajin ƙarshe wanda ya haɗa duk wani abinda mace mai lafiya zata buƙata, a tattare dashi kamar My bugun zuciyata Kamal! Ya yarda yayi tattaki yabi macan da baya so , har uwa duniya ya iskota London ya aurota, ya ɗauko abarsa yana riritata yana tattalint, ko ƙuda bayason ya rabar masa Sweetie ɗinsa, amman kuma kice baya sonta...? Kuma Kamal ɗin ne yace maki baya son Sanyin idaniyarsa Mubina ke yake so...? Oya Answer me...?"
🥺 Yacin yau nagaji sosai, read more yayi yawa ba lallai ba gobe ku samu, maybe se jibi ko ma....🥱🥱

*~Sweet Real Ladingo ce~😘*

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikiin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*https://www.facebook.com/groups/3339190372800311/permalink/3361752087210806/*KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣

Umaimah cikin dakiya da nuna jarumtarta, tace"Eh shine ya faɗi kuma ai ba ƙarya yayi, abinda kowama ya sani ba shi bane ya miki cikin shege, kin saba bin maza daman, amman kika liƙe masa, wai cikin shine da yace baya so kika zubar da cikin dan ki janyo hankalinsa, gareki, bayan ɗiyan turawa sun gama ƙwaƙwaleki..." Wani irin gigitattun maruka ta sauke ma Umaimah guda hudu a jere tana huci tayi kukan kura ta damƙe wuyanta, iya ƙarfinta ta sakama Umaimah ƙafa ta jata sai ƙasa timm tabi bayanta ta danneta ta maƙore mata wuya iya ƙarfinta.
Mubina ilahirin jikinta ɓari yake ta shaƙe Umaimah iya ƙarfin cikin ƙaraji tace" Kamal ne yace maki saura ya sameni? kuma nayi cikin shege? ƴaƴan turawa suke nemana...?" Wallahi idan baki faɗamin gaskiya zan iya kasheki, faɗamin gaskiya..." ta faɗi cikin ƙaraji. Tana ƙara maƙore mata wuya ta zauna saman ruwan cikinta.
Umaimah cikin tsoro da ganin Mubina na ƙoƙarin kasheta dan idanunta sun firfito numfashinta na dab da tsayawa, tanaga lahira kusa yasa ta buɗe baki dakyar tace"Ki sakeni zan faɗa maki gaskiya wlh." Mubina ta ƙara matse mata wuyan tace"Wlh a haka zaki faɗa ko ki mutu a yau dan zan iya kasheki wlh saidai nima a yanke min hukuncin kiss tinda a saudiya nake." ta faɗi tana sake matse wuyan nata.
Umaimah tana zubar da hawaye numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta, can ƙasa ba'a jin maganarta ma sosai tace"Wlh bashi ya faɗamin ba, asalima ance tugu aka kulla maku dan Allah karki kasheni." ta faɗi tana tari idanunta sun fara lumshe. Mubina ta sake wanka mata mari tace.
"Ok so kike ki haɗani da mijina shiyasa kikace nice na nace masa ko? To inaso ki faɗa da bakinki bakya son Kamal kuma sharri kika ƙullamin banyi cikin shegeba, sannan kice nayi haƙuri." Umaimah cikin rawar murya tace" Wlh sharri na ƙulla miki bazan ƙaraba, Wallahi ina sonsa har ciwon zuciya nake saboda shi..." Mubina ta ƙara kwasheta da mari ta ƙara matse mata wuya tace.
"Wlh sai kince baki son Kamal kin barmin mijina zan rabu dake, idan ba hakaba na kashe ƴar iska kwartuwa me son mazan mutane..." Kamal ne ya katse mata magana yana faɗin"Kai subahanallahi Mubina me zan gani?" ya faɗi yana isowa wajan. Mubina cikin ƙaraji tace"Kamal na rantse da Allah idan ka kuskura ka ɗaukeni a kanta ba tare da tace bata son mijina ba a bakin auranka karka ɗauka wasa nake zan shayar dakai matuƙar mamaki." ta faɗi tana ƙara shaƙe Umaimah. Kamal ya iso cikin lallami yace"Haba Sweetie don Allah kiyi haƙuri bata son mijinki fa." ya faɗi ya rankwafowa. Zai taɓata tace"Wlh zan baka mamaki kana taɓani kasan na barka har abadan se dai ka auri Wannan jakar matan, ke zaki faɗamin kin barmin mijina kokuwa?" Umaimah tana fitar da numfashi sama sama tace"Wlh nabar miki Yaya Kamal ki sakeni." sakinta Mubina tayi, Kamal ya ɗauketa cak ya nufi bedroom da ita. Kuka ta sakar masa tana dukansa a ƙirjinsa. Yana kwantar da ita saman katifa da gudu ya bar ɗakin ya rufo kofar ya murza key, ya nufo gun Umaimah wacce yaga bata ko numfashi, hankalinsa a mugun tashe ya nufo wajanta, taɓata yayi yaga bata numfashi, miƙewa yayi ya nufi kofar fita da sauri yana faɗin"wai Allah Mubina ya zanyi da kayan kunya?" yana buɗe kofar sukayi karo da Raihana, da robar ruwa a hannunta, ya riƙeta ya amshi ruwan yace"Raihana maza jeki kiyi game gamuna zuwa bari naba Aunty balaraba ruwa tasha."Raihana tace"Uncle ai Aunty Umaima tana ciki fa, Daddy yace tazo tasha magani." Kamal yace.
"Ok jeki gamunan zuwa yanzu." juyawa tayi tana dariya ta tafi, kofar ya murzama key ya dawo wajan Umaimah Mubina kuwa sai dukan kofa take tana kuka tana ƙiran"Kamal wlh karka taɓata."
Ruwan ya buɗe ya zuba a hannunsa ya shafa mata a fuska ya shiga zuba mata aƙirjinta. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana tari, Kamal ya kamata ya tasheta riƙeta yayi ya nufi saman kujera da ita suka zauna ya bata ruwan tasha sosai tana hawaye. Kamal ya kama hannunta cikin sigar lallashi yace"Ƙanwata dan Allah kiyi haƙuri da abinda Sweetie ta miki kishine ke damunta, please karki bari a gane a gida zanji kunya, amman me yasa kika zo kika cemata kina sona?" kuka Umaimah ta saki ta janye hannunta daga riƙon da ya mata, tace"Yaya Kamal wlh ta kusa kasheni ban shirya mutuwaba duk da ina sonka zan haƙura wlh wannan kasheni zatayi kalli fuskata irin marin da tamin kalli wuyana ta kusa kasheni..." daga can Mubina tace"Zakici ubanki idan nafito fa wlh." Kamal ya kama Umaimah suka nufi kofar fita, kofar ya buɗe yana riƙe da ita ana kofar suka tsaya ya zuba mata ruwa ta wanke fuskarata ya shiga lallashinta har ya samu ta dawo nutsuwarta, ya kama hannunta suka shiga part ɗinsu Kawun.
Chapter 104 · 0% Book details