← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 124

Sashe 93

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamu suna zaune a parlo ta kalli Umpah tace"Wai meyasa kace ya tafi da ita ne?" Umpah yay murmushi yace.
Nusaiba kina bani dariya to mutum da matarsa, tinda kikaga ya cire kunya ya tambaya, kawai abarshi ya tafi da ita, ba fa xai barta tayi karatunan ba, kawai barsu lokacin da yaso suka dawo ƙasar zata ƙarasa, nikam inata asara zuba maƙuddan kudina a bazan, ya hanata ta nutsu tayi karatu, so yanzu dai ai kome yaƙare, shine zaiji da matarsa, ruwansu suyi ruwansu karsuyi, badai ta kore jahilciba, babu ƙasar da bazatajeba, iliminta ya wadaceta na boko da mahammadiya." ya faɗi yana murmushi yana kallon Mamu.
Mamu tace"Ikon Allah! Tom Allah yabasu zaman lafiya, ai nikm na fita bayan Mubina ƙiri² Baby ta kunyatani wai Kamal take so mu yafe masa amasu aure."Ablah tayi dariya tace"Ai fa kam baby ba dama, amman ni kam yanzu wallahi inason Kamal daman rashin sani ne yasa na tsaneshi, suku ma sunga ƙarshensu ko." Umpah yace"Wai ina Amrah ne?" Mamu tace.
"Tana ɗaki fa." Ablah tace"Yarinya me haƙuri da biyayya." Umpah ya miƙe yace "bari naje na dubata" ya faɗi yana nufar sama. Mamu tace"Ablah Mubina yau ko ƙira fa batayi ba oh ni Nusaiba..." Bata idasa rufe baki kuwa sai ga ƙiranta ya shigo wayar Mamu. Ganin number ummi ce yasa ta ɗaga, da sallama. Mubina da take xaune tsakiyar bedroom sun baje da Kausar suna cin indomie, tace.
"Mamu i miss u kuma Mamu shine baku nema na?" Mamu tace"Ikon Allah Baby Æ´ar love sannunki fa ya soyayya É—in, ashe karatun zaki bari kibi miji saudiya ko?" Mubina daga can ta waro manyan idanunta kamar zasu faÉ—o tace"Wayyo ni Allah na!! Mamuna inji wa?" Mamu tace.
"Kinci gidanku inji mijinki mana ɗazu ya ƙiramu nan ya gaishemu yana faɗama Umpah." Mubina ta saki kukan shagwaɓa tace.
"Wollah Mamuna ban saniba ma ni bana zuwa karatuna zanyi..."Mamu tace "Hummm ni dai ba ruwa kibi mijinki." Ablah tace"Nusaiba ki bani mana nima mu gaisa." Mamu tace"Baby ga Ablah" ta faɗi tanaba Ablah ɗin wayar. Ablah ta amsa ta manna a kunnenta, tace"Baby sannu ya jikin naki? Ashe zazzaɓi kikayi?" Mubina tace"Eh Ablah nah i miss u wayana ce bansan inda take ba tin jiya ashe Ummi ta ɓoyeta, shine na ƙira da wanan yanzu, ina yaya Kabeer da Amrah?" Ablah tace suna lafiya lau?" diff ƙiran ya ɗauke daga can ashe kuɗine ya ƙare.
Mamu tace kuɗine ya ƙare ko?" Umpah ne suka fito da Amrah yana riƙe da hannunta yana waya yana cewa"Eh Sageer zazzaɓine kazo ka dubata jikin akwai zafi sosai." yana faɗin haka ya tsinke ƙiran. Suka iso parlon ya zaunar da ita saman kujera yana mata sannu ya zauna kusanta. Mamu ta taɓa jikin nata taji zazzaɓi, tace"Sannu Amrah kiyi haƙuri kinji." Jikin Mamu ta kwanto ta ɗaga kai. Umpah yace"Bari a zubo maki abunci kici kaɗan ko?" Amrah ta ɗaga kai. Da kansa ya zubo mata abincin ya kawo mata ta ɗanci kadan ya zubo mata lemo ta ɗan kurba, tana gamawa Sageer yay sallama kofar parlon. Ablah ta amsa tana cewa"me gida shigo mana."
Sageer ya shigo da leda a hannunsa ya sunkuya ya gaishe dasu Umpah da Mamu, suka amsa cikin sakin fuska.
Umpah yace"Yauwa Amrah kuje parlon baƙi sai ya dubaki." Cikin ɗauriya ta miƙe tana ciza baki ta fice. Sageer ya miƙe yama su Umpah sallama. Amrah tana zuwa ta zauna saman kujera ta haɗa kai da guiwa tana kuka. Haka Sageer ya iskota, yauninta yakeji matuƙa baisan ta ina zai fara ba. Zama yayi kusanta cikin dakiya yace"Amrah kiyi haƙuri nasan bakya sona dole aka miki, amman yanzu kiyi haƙuri mu amshi ƙaddara please, bari muji jikin naki." ya faɗa yana kai hannunsa wuyanta, zafi yaji sosai ya ɗago da kanta yana kallonta ya shiga goge mata hawayen, yana mata magana amman ko gezau tama ki yarda ta buɗe idanunta.
Sageer ya janyota jikinsa baki ɗaya ya rungumeta tsam, ya buɗe ledar maganin ya haɗa alluran da zai mata ya janye siket ɗin jikinta fara cinyarta ta baiyana a hankali ya ƙara ƙasa da siket ɗin ya tsira mata alluran, ɗan zabura tayi kaɗan, ta ƙamƙameshi tana zubar da hawaye. Haka ya samu ya gama alluran, yakai bakinsa saman kunnenta, yay magana a hankali"Sannu Amrah akwai zafi ko?" ya tambayeta yana lailaya mata wajan yana bubbuga bayanta. Amrah ko ci kanka bata cemasa ba. Siket ɗin ya mayar mata, ya gyara mata kwanciya a ƙirjinsa, ya ciro magugunan ya buɗe ya ɗago kanta yace"Please Amritana buɗe idanunki na nuna maki maganin naga harda ciwon kai kike."
Dakyart ta buɗe idanunta sai kumburo² take. Murmushi yay ya nuna mata yanda zatasha maganin. Jikinta ta janye anasa ta koma gefe. Sageer ya miƙe ya kamata ta miƙe tsaye yana riƙe da ledar ya kama hannunta suka fito. A kofar parlo ya saki hannunta. Yace"Ki bani number wayarki please kinji." Baki ta turo tayi wuff ta shige parlo. Dariya yayi yabi bayanta. Sallama yamasu Umpah ya bata ledar maganin ya tafi. Mamu tace.
"Halan rashin arziki kika masa?" Amrah tace"Aa wlh."ta faɗi tana ɗaukar ledar maganin ta nufi sama. Ablah tace"Aa ai batada rashin kunya indama tawajenace zata aika."Umpah yayi dariya ya miƙe yana cewa"Kuma yau aikuwa sai na gamaki da Mubina Ablah." Ya faɗi yana ƙiran number papa Saleem yana sheda masa ya amso takardun makarantar Mubina yaba mijinta. Ya fita daga parlon yana faɗa masa duk yanda sukayi. Mamu da Ablah sukaci gaba da hirasu...

Umpah kuwa yana gama waya da papa, yana fitowa ya ƙira Abbu bayan sun gaisa yace"Abubakar muje mana policestetion gurin yaranan muga wane irin horo suka samu." Abbu daga can yace"Wai ban faɗama ba ai ɗazu da yamma bayan na fito daga company na biya. Wallahi sun jigata sai roƙona suke, bari gobe muje da safe rabu dasu." Umpah yace.
"Ok Allah ya kaimu, ɗazu muka gaisa da yarona, fa ashe saudiya zasu wuce gobe yace ko jibi." Abbu dake zaune kusan Ummah sai da ya dafeta yana zaro idanu. Umpah yayi dariya yace"Au shiru kayima to wlh kull ka hanamin yaro tafiya da ƴarka sam wlh bazanji ɗaɗi ba, sonta da yake yajayo hakan, kuma kasan ba kowa zaibar matarsa tana wata ƙasa karatuba shi yana wata ƙasa." Umpah ya faɗi yana sakin murmushi.

Abbu yace"Wallahi Abdulrahim samu nagartaccan mutum irinka a duniya sai an tona, ni kam banida bakin maka godiya, ai ni ko faÉ—amin baiba fa, nasan sai ya gama shirin ko ya hau jirgi sannan ya sanar dani ko." Umpah yayi dariya yace.
"A to ai gaskiya dan kasamu muna son ƴarka sai kana mana iko sanin bazaka barmu bane yasa yaƙi faɗa maka, to zan ɗan fita Abbu sai anjima." Nan suka sallama ya tsinke ƙiran ya nufi compound ɗin gidansa ya ƙira Haladu yaja shi a mota suka fita.
Ummah ta kalli Abbu tace" Ya dai Kamal ne ko?" Abbu yace"Aff shine mana, yana can yana shirin tafiya saudiya da matarsa, shine bazai barta tayi karatunta ba, yaron nan yafiye son kansa wlh." Ya faɗi yana dialing ɗin number Kamal. Lokacin kuwa sun kama hanyar gidansu Mubina dare ya fara sosai, yaga ƙiran Abbaunsa, Bugu biyu ya ɗaga tare da sallama. Abbun yace"Kaci gidanku, akan me zaka raba yarinya da karatunta, yanzu ka kyauta kenan saboda Allah Kamalu?" Kamal ya marerece murya daga can yace.
"Wayyo ni Kamal Abbu kayi haƙuri, wallahi ba haka bane naga watan ramadan ne ke shirin kamawa nan da kwana 2 ko 3 days so kaga sai muje muyi ta ibada muna maku Addu'a Allah ya ƙara maku lafiya da nisan kwana." Abbu yace"Hamm ƙarya kake to wlh da zaran an kammala Azumi ka ɗauko yar mutana ku dawo gida tinda ka rabota da karatunta, na london dole zaka barta ta karasa ana maradi kaji na gaya maka, kuma maza ka ƙira Kawunka ka sanar dashi kana london ka faɗa masa kome, sam baka kyautaba ƙanwarka ma Umaimah ba lafiya ka masa ya maijiki." Kamal yace"Yauwa Babana shiyasa nake sonka wallahi, ayya kawuna yayi haƙuri yanzu kuwa zan saka kati na ƙirasa na bashi haƙuri insha Allah! Umaimaha me ke damunta? Zan ƙirata,Abbu ina Ummah nah da rabin raina Samha.?" Abbu yace.
"Ga Ummanka Samha kuwa gobe ba school tabi Goggo can gidanta." ya faɗi yana ba Ummah wayar. Ta amsa ta kara a kunnenta. Kamal yace"Hello Mummynah ina yini"Ummah tace"Hamm lafiya lau ɗan albarka ya ɗiyata?" Kanshi ya shafa ya saki ƴar dariya yace"To Ummah ni ina zan ganta tana gidansu fa." Ummah tace"Ƙarya kake yaron kirki faɗamin gaskiya bani mu gaisa jiya da yau bata ƙirani ba."Kamal yace"Ummah to ni dai bana tare da ita gaskiya ina zan ganta sai zamu tafi zani gidansu ai." Ummah tace"Hummm yayi kyau zanko haɗaka da ita, wai kaji labarin duk abinda ya faru kuwa?" Kamal ya jinjina kai yace"Eh mana nida nakeda Momy Hafsy." Ummah tace "ai kuwa dai." Parking ɗin da Makel yay a kofar gidansu Mubina ne yaska Kamal yace"Ummah zan shiga bayi bari ajima zan ƙira ku bye." Ummah tayi dariya tace"Ai ƙaran mota naji ko toilet ɗin ma a mota ake zuwa?" Kamal yayi dariya ya tsinke ƙiran. Ummah ta meƙawa Abbu wayarsa tana murmushi. Abbu yace.
"Ya sheƙa maki ƙarya ko?" Dariya tayi ta rungumeshi tace"Yarona fa Kangiwa ya biyo a soyayya." Abbu ya rungumeta yana dariya. Nan suka shiga hirasu suna manne da juna...
Chapter 93 · 0% Book details