← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 124

Sashe 40

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamu ce tsaye tsakiyar parlon kusan wasu dirka dirkan akwatina, idanunta jajur tana kai koma waya a hannunta Amrah tace"Mamu wlh bata jeba gun telanba nakirashi yace yana kiranta wayarta na ringing ba'a ɗauka kamar yanda kika kira yanzu ba'a ɗauka ba..." Sabeelah tace"Mun shiga uku mun lalace..." Wani kyakyawan matashi saurayi yace"Ummi yo ina babyn ta shiga ne wai? wlh nayi kewarta ƴar kanwata ina kira ba'a ɗauka" Sabeelah tace"Wlh shine fa matsalar." Ablah tace" Ke!! Basma da ina da ina kuke zuwa da ita? Wayyo ni na shiga uku ina ta tsaya har anyi magarib ka ubanta ya shigo" Basma zatayi mgn, Umpah ne suka shigo da sallama shida Abbu, Abbu ɗa Kabeer Kabeer ya nufi part ɗinsa yay wanka kafin a kura isha zafi yake ji. Abbu ya karasa ya sunkuya yana gaishe da Ablah ta amsa. Amrah ta sunkuya har ƙasa ta gaishe da Abbu cikin girmamawa, ya amasa yana sa mata albarka. Umpah yace"Ina Auta yau rabona da ita tin safe fa , kenan bayan ta dawo daga makaranta da yamma ta tafi amsar ɗinkin? amman ai nace abar bari in yamma tayi kwarai tana fita ko?" Mamu ta rasa abin faɗa ta gishe da Abbu idanunta na fitar da kwalla. Ablah tace"Abdul maganar gaskiya jeka ne momin Baby wlh tin fitar safe bata dawoba ta kira dai da azuhur tace zata gun tela ta dawo makaranta hallo idan an tashi ta koma can, yau komin dare sai ya bata ɗinkin ta..." Umpah ya zaro idanu yana ma Mamu wani mugun kallo yace"Shine bazaki kirani ki faɗamin ba ƴarinyar bata gida? Ok yanzu badan Abubakar ba yace muzo ya gaishe da Ablah yama baƙi sannu.da zuwa, kafin a kira sallah isha, tinda ta zo sau daya ya shigo ashe da baza a faɗin ba ɗiyata bata gida Ngd Nusaiba." ya faɗa yana kama hannun Abbu suka nufi kofa, Majeed yabi bayansu yace "Umpah ina zuwa.. Umpah yace"muje mana kanwar ka bata gida ina zama" yace da Ablah"Ablah ni da yazama dole na abar sona na tafi neman bari naje gurin telan." ya faɗa suna fita daga parlon. Amrah zata yi magana Mamu ta rufe mata baki... Sabeelah tace"Baby bby ina ta shiga ne...?" Abbu yace "ai bamuga ta zama ba muje a dubata". Mota suka nufa Abbu zai zauna gun zaman direba Majeed yace"Abbu bari nayi driving ɗin sai kuna nuna min inda zamubi." Nan Majeed ya shiga suka zauna gaba, yaja motar ya nufi get, megadi ya bude get suka fice. Ganin mota Kamal a kofar gida Abbu yayi mamaki yaaan baya ajiye mita a kofar get, Yace"baƙo tsaya yauwa ga malamin nasu a bari na shiga inji karfe nawa suka tashi dan wataran suna kaiwa har magarib ma."Umpah yace muje kawai tare Allah yasa ma wani laifi tayi ya hukuntata zafin jin dadi nasan tana hannu nagari." Abbu ya jijina kai Majeed yay parking suka fito suka nufi cikin gidan su ukun.

Kamal kuwa yana shiga ya cire kayansa ya saka jallabiya baƙa me kyau ya ɗauro alwalla yana fitowa yaga Ummah zauye da sauri ya hau darduma ya tayar da sallah magarib. Yana gamawa ya ɗaga hannunsa sama yana kwararo Addu'a yana kuka. Ummah ta miƙe arikice jin abinda yake faɗi, jikinta na rawa tace"Kamal zina kayi? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Mu ka tozarata? irin tarbiyar da muka baka kenan?" Kamal ya miƙe ya rungume ummah yace"Nasan kinsan halina Kinsan me zan aikata me kyau da maras kyau , amman wannan ba lallai ki yarda dani ba..! Ba lallai ki fahimceni ba... ummah kaddara ta hau kaina nama ƙanwar Amrah fyade na lalata mata rayuwa na sata cikin kunci Mubina na ɓata maki rayuwa, ummah ku yafeni na ɓata maku suna ban san da idanun da zan kalli umpah ba
wlh sharrin magautane..." Wani lafiyayyan mari aka sauke masa kumatunsa guda biyu. Ummah a tsorace!! Ta É—ago da kanta taga waye taga Abbu na zubar da hawaye jikinsa na kyarrrma yana nuna Kamal da yatsa...

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan*
*lambobin👉🏻+22792589446/* *+22796515805*[26/07, 1:29 pm] +234 806 949 3599: *KAMAL NE*

*Book 1*

*SHAFIN DUKA NAKUNE ƳAN AMANA🤝🏻😻SADAKARWA GAREKU ƳAN AMANA MASU FITARMIN DA BOOK WAJE ALLAH DAI YABAR KAUNA ƳAƳAN AMANA🤝🏻🤩🤩🤩*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣3️⃣

Abbu cikin rikita da kuma tashin hankali marar musaltuwa yake nuna Kamal, hawaye ya gama wanke masa fuska yace"Nine ka tozarta ka wulaƙanta a idanun duniya,? Kamal ka rasa wacce zaka lalata ma rayuwa se kanwar matar da zaka aura? kuma ɗiyar aminin da ba mujima da haduwa ba , amman ya ɗauki dukanin yarda shi da yabani , kai ko ka cutar dani ka zalumce ni kayi zina da ita ka lalata masu gobenta...?" Abbu ya karasa mgnr yana sakin kuka ya duƙe ƙasa nan saman carpet. Kamal kuka yake sosai ya saki ummah ya zube gaban Abbu zai dafashi Abbu ya masa wata irin tsawa! Wacce ta saka Kamal ɗin sarewa, yace"Karka taɓani kana fama da najasa zaka raɓi jikina, ni ban taɓa lalata ƴar kowa ba, amman kai ka tozar tani kayi babban laifin da bazan yafe maka ba! ka kunyata ni a idanun duniya..."ya faɗa yana kuka. Zakiyya wacce take tsaye shigowarta kenan, dan se ta shiga ɗakin Samha tai fitsari kafin ta shigo, duƙewa tayi itama ta saki kuka duk bata san me suke ma kuka ba.! Kamal yana kuka yace"Ummah ki saka baki Abbu ya fahimceni wlh bansa ya a kayiba hakan ta faru ba bansan ta yaya nai mata fyade ba..."Ummah da take kuka tace"Kamal shaye-shaye ne ka fara har kaje kayi zina sabon Allah? Me yasa idan ita yarinyar kake so ba yayarta ba, ka mana mgn mujira ta gama karatunta a aura ma ita? Amman se ka aikata zina ka cuce mu ka cuci ɗiyar mutane ka zubar mana da mutunci, kasa munji kunya amman kai da yake bakada kunya gashi ka tsaya gaban mu kana faɗa mana..."Kamal ya miƙe ya faɗa jikin ummah yana cewa"Ummah ku yarda dani dan Allah..."Abbu ya katse shi yace"Wuce muje gun mahaifinta ka kaimu inda take, se ka masa bayani amman ka sani ni na yafe ka zaka barni kayi nesa dani don Allah na roƙeka" ya faɗa yana gama hamnunsa yana kuka. Zakiyya a guje tayi waje. Ummah a rikice ta kalli Abbu tabbas a halin da yake bazai amshi roko ba a yanzu. Rungume Kamal tayi ta kece da kuka tace"Kamal nima zan barka kayi nesa damu ko zamu samu nutsuwa ka cutar damu ka wulaƙanta mu a idanun duniya." Kamal yama cije ya kasa kukan sbd girman lamarin. Zakiyya ce da goggo da Samha suka shigo. Samha kuka take sosai tana cewa"Wlh Abbu sharrin shedan ne..."Goggo tace"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! A gaskiya akwai wani babban alamari wannan ba halin Kamalu bane! Abubakar Fatima kuna da hankali zaku ce yabar gari? Bama haka wace yarinya ce wai?" Abbu ya miƙe yace"goggo ɗiyar de wanda muka shigo ya gaishe ki wanda suke nan parlo suna jiran mu, ƙanwar matar da zai aura." Goggo duƙewa ƙasa tayi a rikice tace"Allah mun tuba ka yafemu ka bamu ikon cin wannan jarabawar , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Abbu yace"muje ka kaimu gun yarinyar se ka kalli idanunsa ka faɗa masa abinda kama ƴarsa mafi soyuwa a zuciyar sa..." Kamal ya saki ummah, ya kama hanyar waje yana cewa"goggo kisa su fahimceni zan faɗa maki iya abinda na sani." ya faɗa yana fita. Abbu ya goge fuskarsa yace"Fatima karma kisa damuwa a ranki bazamu zauna dashi ba, dan zaima iya ma Samha haka tinda yama ƙanwar matar da zai aura..."

goggo tace"Wlh bazai yi ba"ummah kasa mgn tayi. Kowa goge fuskarsa yayi suka biyo bayan Kamal. Kamal kuwa yana saukowa yaga umpah zaune suna hira da wani matashin saurayi baƙon gidan su Mubina. Duƙawa yayi gaban Umpah, ya kama guiwowinsa ya fashe da kuka yace"umpah ina neman gafarar ka na maka mummunna laifi nasan ba lallai ka yafe min ba..."Umpah ya rufe masa baki yace"Subahanallahi haba ɗan albarka wane irin laifi zan kasa yafema haba dai babu shi gaskiya kuma karma Allah ya kawo shi, ina mutuniyar nace ko dai tayi laifi ne kake hukantata ai da naji dadi baby fitina wlh..."Kamal ya sake riƙe umpah yana kuka yace"Umpah tana hospital kuma nine sana ɗi wlh naji kunya na aikata babban laifi bansan ya akayi ba na mata fyade..." Ai bai gama ba umpah ya rufe masa baki da sauri, yace"No karya ne haba dai Kamal ya zaka tozartani ka ɓatama ɗiyata gobenta ka hargitsa mana kan zuri'a..." Kamal yace"Wlh umpah iya gaskiyata na faɗa." ya karasa mgnr yana kuka. Umpah jikinsa mazari ya ɗauka ya ƙame ƙam a tsaye waje ɗaya, ya kasa kwakwaran motsi, ya zubama Kamal idanu ya ɗago ya kalli Abbu da ke famar zubar hawaye ya duƙe gabansa ya riƙe guiwarsa. Da sauri ya kauda kansa yana faɗin"Allahumma ajirni'fi musibatin wa'akilli khairan!! Tashi muje kaini inda take ko ta mutu ne?" Umpah ya faɗa yana ciro handkchierf yana goge zufar da take keto masa. Abbu ya riƙe masa ƙafa ya kasa mgn. Kamal ya miƙe ya nufi kofar fita. Goggo tace"Abdulrahim ka yafe mana hakiƙa yaron mu be kyauta ba sam ya samu jin kunya babba..." Umpah jikinsa na rawa ya girgiza kai ya sunkuya ya kama Abbu ya miƙar dashi yace"Abubakar kabar kuka muje muga abinda Allah yayi , ba me ja da hukuncin Allah shike kome a lkcn da yaso ko ta mutu ma dole zan daure..." Majeed yace"Kai haba dai wlh se inda karfina ya kare baby za'a ma fyade mu kyale..."Umpah ya daka masa tsawa! yace"wuce jeka gida Majeed karka sa na harzuƙa adai-dai wannan lkcn shiga gida kawai." ya faɗa yana kama hannun Abbu suka fito, ummah ta biyo bayan su. Kamal yana bakin mota a tsaye suka fito Umpah ya kira Mamu a waya yace ta fito cikin shiri da sauri. Bata jima ba ta fito.

Motar Kamal Umpah ya shiga shida Mamu da Abbu da goggo da ummah Majeed ya maida motar cikin gida. Suko suka tafi Umpah ya hana kowa binsu ya jama Majeed kunne.
Chapter 40 · 0% Book details