Sashe 95
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta juyowa tayi ta fuskacin Kausar tace"Ke kuma saboda tsabar rashin kamun kai, ki kalli tsakiyar idanun mijin wata kice ya haɗu, ba ko jin nauyina ina tsaye ki yabar min mijina, ke halan macijiyace bakya gina ramin kanki sai wani ya gina ki shiga...? " To Kamal mijina ne da gaske, kuma ba'a sonsa ɗin, amman wallahi babu ƴar iskar da ta isa taso min mijina, saidai bayan idanuna, ke kam kinci darajar ƙaunar da kike nunamin , da abotar da take tsakanina dake, wlh ba dan haka ba ko hummm kinsan banida kyau..." Ta faɗi tana juyowa wajan Kamal wanda ya harɗe hannayensa saman ƙirjinsa, ya zuba mata tsumammun idanunsa yana sakin sansanyan murmushi, tsananin sonta da ƙaunarta na yawo a kowane lungu da sako na jikinsa, yana masifar so da ƙaunar Mubina. Makel baki da hanci ya saki yana kallon dramar wannan matar ta friend ɗinsa, duk da baisan me take. Kausar ce tayi sauri shan gabanta tana dariya, ta rungume Mubina ɗin tacewa. "Am sorry sahiba wallahi wasa nake maki lallai da farko bansan mijinki bane, amman koda naji kin ambaci mijinki wlh na A jiyeshi gefe, haba sahiba kin manta inada Suhal ɗina yana jirana? Sha ruwan sanyi, baxan so abinda kike soba..." Mubina ta kai mata duka tace. "Allah ya isana nice nace maki ina sonsa? Ai dole mace tayi kishi akan mijinta ko bataso, ba wai se tana soba, ai kishi halitane, kuma naji daɗi da kika ce wasane." Ta faɗi tana janye jikinta daga na Kausar, ta mata raɗa, tace"Bari na masa barazana." ta faɗi tana nufar gun Kamal ɗin. Wanda har yanzu kallon abar sonsa yake. Mubina tana isowa gaban Kamal ta zumburo baki gaba tana hararasa ƙasa² dan bata jure kallonsa, ta riƙe ƙugunta tana girgiza tace. "Malam sai ka ƙara gaba wannan ƙawata bazataci amanata ba, ehe wai harda cewa itama ta haɗu kuma anan gidan take, to dame tafi idan ba jikiba da zaka cima matarka fuska a gaban ƙawarta." Ta faɗi tana matsar ƙwalla. Kamal ya waro idanu, ya janyota da sauri ya sake matsawa can gaba ya shigar da ita cikin jikinsa sosai luf tayi a ƙirjinshi, ta fashe masa da kuka. A rikice ya tallafo kanta, ya kamo fuskarta ya ƙura mata idanunsa masu masifar saka shaukinsa, ba tare da ta shirya ba. Jijigata ya fara yana shafa bayanta, cikin sigar lallashi yace. "Oh Sweetie please natuba, wallahi babu wata ƴa da nakeso a duk duniya saike, wlh zuciyata kekadai take muradi, temaka kibar kukan to meye abin kukan? Kinsan bazan so ƙawarki ba, nifa daga ke na rufe kofa..." Bori ta fara masa tana tirjewa, sai kokowar kwatar jikinta take. Dab da fuskarta ya kawo fuskarsa, cike da tsantsar ƙaunarta ya fara magana, cike da rauni murya can ƙasa cikin cool voice ɗinsa, yace. Sweetienah please kibar zubarmin da hawayenki, akan wata da bazan taɓa sonta ba, haka itama so meye na damuwa Sanyin idaniyata? Wlh ina masifar son ayi kishina irin yadda kike ɗinan, i love u my sweetie sanyin idaniyata." ya faɗi yana ƙara rungumeta tsam², yana bubbuga bayanta. Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Mubina, idanunta ta lumshe ta zagaye ƙugunsa da hannayenta, tana shaƙar daddaɗan ƙamshin Kamal. Ɗan Ƙaramin bakinta ta zumburo tanajin wani irin abu na mata yawo adukan gaboɓin jikinta. Kamar an tsikareta ta sakeshi ta fizge jikinta tace. "Ni a daina taɓani ehe." Kamal ya kamo hannunta yace"Ok yi haƙuri muje ciki na gaishe dasu ummi." Hannunta ta janye tace"Ai ni rakiyar ƙawata zanyi ka shiga mana, ko sai dani?" ta faɗi tana murguɗa masa baki, ta nufi gun Kausar wacce suke hira da Makel kamar sunsa juna. Mubina tana isowa tace"Muje karki rasa texi." Kausar tace"Ok muje." Kamal yace"Sweetie muje mana a kaita gidan ko sai mu maidoki ko?" Mubina tace"Bama so wa zai shiga motarka? tab, anan kofa zata shiga taxi." tana faɗin haka taja Kausar suka tafi. Kamal ya lura ba waya a hamnunta, yace da Makel"Bisu kaga tafiyar ƙawar tata, sai ka tsare min ita da hira a gun mota har na fito na wuce da abuna da safe na maidota, nasan wayon da zanyi, bari na shiga na gaisheda ƴan gidansu."Makel yace"Ok sir friend." Kamal murmushi yay ya nufi kofar falon. Sallama Kamal yayi a kofar parlon. Ummi ce tazo ta buɗe kofar, tace"Kamal bismillah mana."ta faɗi tana matsawa. Cikin girmamawa Kamal ya shiga falon, yana sake sallama. Papa ya amsa. Ƙasa Kamal ya zauna yana gaishesu, suka amsa cikin fara'a ummi ta ƙira Natalee ta kawo masa ruwa. Kamal yace"Ah ummi saman hanya muke ga maganin nata amman tace gidansu Kausar zata kwana, suna mota, zamu ajiyesu nida abokina, wai tace ko phone ɗinta ina, a bata zata ƙira yayanta Majeed yaje gidansu Kausar ya ɗaukota gobe." ya idasa maganar kansa a sadde. Ummi tace"Kamal karfa ka yarda tana yawo sakaka amman ni bazan hantaba tinda ka yarda kaine ma zaka kaisu shikenan, bari na ɗauko mata wayar." ta faɗi tana miƙewa ta nufi bedroom. Papa yace"Gobe insha Allah zan amsa takardunta na makaranta Abdul yace a baka ashe jibi zaku wuce ko gobe?" Kamal cike da kunya, yace. "Sai jibi Abba." Papa yace"Allah ya kaimu" Kamal yace "Amin" Aleem dake zaune kusan Kamal yace "Uncle inzo ka kaimu muma gidansu Aunty Kausar?" Kamal yace"Ai ni gida zan wuce daga can ko gun antynka zaka kwana?" Papa yace. "Rabu dashi idan ta ƙira Majeed zaije ɗaukarta gobe sai kuje tare." Azeema tace"Yeeee nima zan bisu" Kamal yay murmushi. Ummi ce ta fito da wayar Mubina taba Kamal tace. "Ka bata maganin tinda can zata kwana kar aje cikin dare zazzaɓin ya dawo mata." Kamal ya amsa cikin girmamawa, ya ɗauki ledar maganin ya masu sallama ya fito. Ummi tace"Yanada hankali idan wani ne wlh bazai barta ba." Papa yace"Ai kuwa hamm an maidaki gara ko wallahi matarsa zai ƙwamashe babu gidansu Kausar ɗin da zai kaisu, ni kallonsu kawai nake." Ummi tace"Ah wlh can zai kaisu Mubina tacika taurin kai bazata bishi ba." Papa yayi murmushi ya miƙe a doguwar kujera, bai sake magana, ya shiga kallon labarai. Ummi ta shiga nazarin maganar papa Saleem... Mubina suna tsaye nan duk motar da tazo a cike, wata kuma ba hanyar da Kausar zatayi bane, zasubi basa ɗauka. Ganin haka Makel ya isa wajansu, yace da Kausar ta yarda su ajiyeta ma agida. Mubina tace"Bata so abarmu idan bata samu sai mu koma ciki ta kwana." Makel yace"Haba Mrs Kamal yi haƙuri mana, ai idan baki yarda ba, muje harke a ajiyeta sai mu maidoki gida, yafi kuna tsaye anan."Kausar ta kama hannun Mubina tace. "Sahiba kinga Aunty sai ƙirana take please ki bari su kaini gida, kinga dare nayi sosai muje tare kiga shigata gida sai su maidoki, wlh bazan kalli ko mijinki ba."Mubina ganin yanda Kausar ɗin ta matsu yasa tayi sanyi tace da Makel. Ok muje a kaita amman banda Kangiwa ya jira idan ka dawo dani sai ku wuce."Makel yace"Ayya madam ai shima rage masa hanya zanyi ina ajiyeta zan ajiyesa, sai na kawoki dan yafiki nisa." Ɗan jim tayi sai tace"Ok amman kar ya shiga sabgata." Makel yace"angama madam." Kamal dake ɗan nesa dasu yana jin kome ya iso yana danne dariyasa ya fara cin magani bai ko kalli inda suke ba, ya buɗe motar ya shige gidan gaba yay zamansa. Mubina tana ganin haka ta taɓe baki ta kama hannun Kausar tace "Muje ƙawata, shima ai ba motarsa bace, arziki ne yakeci, amman ji wani jiji dakai da yakema mutane."Kausar murmushi tayi, batace kome ba. Makel ya buɗe masu seat ɗin baya suka shiga ya rufe. Ya zaga ya shiga gun zaman driver yaja motar. Kamal yace"my friend fara ajiyeni a gidana tukun inada baƙuwa..."Mubina ta zabura ta waro idanunta waje, amman batayi magana. Makel yace"sir friend bari mu ajiye Kausar tikun." "Ok." kadai Kamal yace bai sake magana ba. Mubina ranta duk babu daɗi takeji amman ta daure tayi shiru. Kausar ta ɗinga masa kwatance gidan har sukazo, Suna zuwa kofar gate, Kausar ta buɗe motar ta fito bayan sunyi sallama da Mubina wacce duk yayi wani iri abin tausayi. Haka Kausar ta nufi ciki, bata yarda tama Kamal mgn ba saboda gudun jarabar Mubina. Makel yaja motar yabar gun. Kamal yana lure da ita, tausayi ta bashi, ganin ta haɗa kai da guiwa, duk se yaji hankalinsa ya tashi amman bai mata mgn ba. Sosai Makel yake gudu, bai ɗauki lokaci ba ya iso hotel ɗin. Yana gama parking ya buɗe ya fice. Se lokacin Mubina ta ɗago da kanta, da sauri taga Kamal ya buɗe motar ya fice. Bata wani sa kome a kanta ba jin daman sai an kawoshi za'a kaita gidansu. Kamal seat ɗin bayan ya buɗe inda Mubina take zaune, ya shiga ya zauna. Idanunta ta zaro cikin masifa tace"Lafiya zaka dawo nan, ba an kawoka masau kinka ba? gun da kuke baɗala ɗin..."Tafin hannunsa ya ɗora mata kan bakinta, ya rankwafo, kamar zai shiga jikinta, cikin wata irin murya yakai bakinsa, dab da kunnenta yace. "Sweetienah zo muje ku gaisa da my lovely na wacce nake masifar sonta da ƙaunarta."Dukansa tayi da karfi ta matsa gefe, idanunta sun fara ƙanƙancewa, ta buɗe baki zatayi magana ta kasa ta kifa kanta saman cinyarta tana sauke wani irin numfashi. Kamal ya ɗagota ya rungumeta ƙirjinsa, wani irin rikitaccen kuka ta sakar masa, tana ƙoƙarin haɗa sunansa. "Ka...ma...l..." Ya manneta sosai yana buga bayanta yace" Na'am Mubina wasa nake miki karki ilatamin kanki wallahi wasa nake miki babu kowa a wajena, muje ciki ki gani sai muje na ajiyeki a gida, shiru Sweetienah."ya faɗi yana fitowa da ita rungume a ƙirjinsa, tana kuka. Yatsarsa ƙarama ya saka mata cikin bakinta, a hankali yay mata raɗa a cikin kunnenta yace. "Oya cijeni sai ki huce ki daina kukan kar ace satoki nayi, in dai ba so kike ba police ya kama miki mijinki ba."ya faɗi yana sakar mata zazzafan kiss a kunnenta, ya ɗago da kansan ya zuba mata kyawawan tsumammun idanunsa. Mubina kuwa jin yace ta cijeshi, ta tsagaita kukan, jin kuma ya ambaci police zasu kamashi, yasa tayi tsit ta shiga cizon yatsar tashi a hankali. Murmushi ya saki ya sake