Sashe 103
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A kwance ya sameta ta naɗe cikin bargo tana gunjin kuka. Kwanciya yayi ya rungumota ya shiga lallashinta. Dakyar ya mata wayo cewar zasu tafi yau da dare, ai kuwa dan murna harda kiss ta masa saman goshi tana shafa sajansa fuskarshi, tana dariya kamar ba yanzu ta gama kuka ba. Kamal da kanshi ya shiryata cikin ɗoguwar riga ƴar kanti wata blue ya yane mata kanta ya sunkuya yace" Hau baya muje." Cikin mutiƙar farin ciki ta ɗare bayansa tana kyalkyala dariya tace"Yaya Kamal Ina son goyo wayyo daɗi baya." ta faɗi tana saƙalo hannunta wuyansa ta leƙo kanta tana kallon kyakywar fuskarshi, tana mulmula masa dogon hancinsa tace.
"Yaya Kamal an taɓa cema kanada kyau eye mijina...?" ta faɗi cikin wani iirn shaukin sonsa da ƙaunarsa da tayi mata mahaukacin kamu ba tare da ta saniba. Kamal yayi murmushi yace"Sweetie bari mu dawo sai na faɗa maki." ya faɗi yana tafe da ita a bayansa. Kanta ta kwantar gadon bayansa ta zagaye hannayenta saman cikinsa tana shafa ɗan tunbinsa tana lumshe idanunta a shagwaɓe ta ƙirashi.
"Kamal !" A kusan kofar parlon ya sauketa ya gyara mata gyalenta, sun fara tafiya ta janye hannunta, ta ruƙumƙumeshi, tana gunji kuka. Murmushi yay yace. "Sweetie yi haƙuri mu shiga mana, idan mun fito sai ki rungume abinki a ɗaki..." shiru Kamal yayi jin ta duƙa ƙasan sa ta kamo ƙafarsa tana shafawa tana dannawa cikin kuka tace"Kamal ciwo take maka ko? Naga kana ɗingiwa sosai yau, ba kamar daba." ta faɗi tana murza masa ƙafar. murmushi yay yace. "Oh Sweetie ai zaman da mukayi ne a jirgi ta ƙage ne, kin manta mijinki, ɗan gurgune...?" ya faɗi yana sunkuyawa ya ciccibeta sama yana dariya. Kukan sangarta ta saka masa, tana dukan ƙirjinshi. Raɗa ya mata a kunnenta, ya ɗago da kansa ya tsareta da tsumammun idanunsa. Idanunta ta lumshe tana ƴar dariya. A shagwaɓe ta ƙirasa.
" Kamal." Sauketa yayi ya gyara mata fuskarta da
mayafinta ya kama hannunta suka nufo parlon. Bakinta ɗauke da salllama suka shigo parlon. Kawu da Yumnah suka amsa. Ta sunkuya ta gaishesu. Suka masa suna tambayarta ya gajiya? Mubina ganin Umaimah bata gurin yasa ta sauke ajiyar zuciya, Raihana ta zauna kusanta tace"Aunty mai kyau zan biki gidanki." murmushi mubina tayi ta rungume Raihana batayi magana ba. Nan Yumnah tayi serving ɗinsu, Kamal yace."Kawu ina Anwar?" Kawu yayi dariya yace"Kaida kasan mutanan ai shida ƙanwar taka ko sa tashi sai bayan la'asar dakyar fa sukayi salla suka koma baccin su nagado." Kamal yayi murmushi baice kome ba tinda aka sako Umaimah yaga Mubina ta kafeshi da shanyayyun idanunta ko ƙiftawa batayi. Haka suka gama cin abuncin sama-sama sukaci dan ba sa wnai jin yunwa.
Kawu yace" Tom zan da shiga kasuwa dan yau wata insha Allahu an ce an ganinshi bari a ƙaro kayan cima dan yanzu zatafi daɗi zuwa daran wallahi mutum zai iya kai asuba saboda cinkoso." Kamal yace"Kawu bari nazo muje nima zanyo siyayya da munje kawai sai a saka a fridge." Kawu yace.
"Eh ka siyo kome a ajiye ga fridge ce ba kome da kunji ba ruwanku da yawon neme neme tinda can ba kome kake ajiyawa lokacin kai ɗaya muje yanzu sai a siyi kome, Suwaiba ki shirya muje har ke sai ki zabar masu kome a nutse, ɗiyata zakije ko?" ya tambayi Mubina. Cikin kunya tace"Aa dady zamu zauna da Raihana sai kun dawo." Kai ya jinjina da hankalin yarinyar. Kamal ya kalli Mubina yana so ta taso su tafi ta lura sarai taƙiya ta maida hanakalinta kan Raihana. Dole ya fice yaje ya buɗe trolley ɗinsa ya ciro maƙuddan kuɗi ya shirya tsaf cikin shigar larabawa ya fito yana baza ƙamshi. Yumnah ta fito cikin shiri tace da Mubina"Idan kinji bacci ɗiyata kije kiyi kwanciyarki karki bari Raihana ta dameki sai mun dawo." Mubina Addu'ar sauka lafiya ta masu Kamal ba yanda baiba su haɗa idanu taƙi haka suka tafi.
Mubina suna zaune da Raihana tana mata iya yi surutu. Mubina tana son tamabyar Raihana taga rashin dacewar hakan. Nan ta biye mata suka shiga game Mubina ta tsarema Raihana sosai sai kyalkyala dariya take.
Misalin karfe biyu darabi Umpah ne da Mamu suka fito cikin shirin zuwa kasuwa sayiyayar wasu abubuwna na kama azumi. Amrah na kwance tayo matashi da cinyae Ablah tana mata susar kai. Umpah yace"Amrah ya ƙarfin jikin naki?" Amrah tayi murmushi tace"Umpah da sauƙi ga Abalah namin sosar kai naci kanbacin Mubina." murmushi yayi ya zauna kusan Ablah, yana murmushin yace
"Ablah Baby an sauka saudiya lafiya Kamal na gaisheku ɗazu na fita ya ƙirani mun gaisa."Mamu ta zauna tana murmushi." Ablah tace "Oh duniya batada tabbas ban taɓa zaton Mubina zata juyamin baya dan ta sami miji ba, ta manta dani ba saƙon gaisuwarta ma sai wajan miji zanji, ai wallahi shiyasa na kama Amrah yanzu." Kabeer da yake shigowa ya bushe da dariya yace.
"Daga baya kenan." ya faɗi yana zama. Mamu tace"Kabeer ko zakaje kasuwar ne kama amarya siyayya?" Cikin kunya ya zauna kusa da ita yace"Mamu don Allah Umpah yaje gidansu Basma tin kawu Zubairu bai tafi ba..." Umpah yace"Insha Allah bari ya dawo yaje Naimey jiya duba hospital ɗinmu ta can ana mata wani gyara, Nusaiba tashi muje." ya faɗi yana miƙewa, nan sukama Ablah sallama suka fice. Suko sukuma sukaci gaba da hirasu, sai gulmar Mubina suke Ablah da Kabeer Amrah na dariya, daman sunyi hakan ne dan su sakata nishaɗi...
Har akayi sallar la'asar su Kamal basu zoba, Mubina ƙiran sallah ne yasa ta miƙe ta nufi ɓangaransu dan tayi sallah, Raihana kuwa tana zaune tana game. Bayan Mubina ta gama sallar la'asar ta shirya tsaf cikin wata fitinanniyar riga green iya guiwarta me hannun vest ta mata masifar kyau kamar yar tsana ta maidata ta fito mata da shape ɗinta tayi mata matuƙar kyau, ta saki gashin kanta har wucin ƙafaɗarta sai baza ƙamshi take bakinta yasha man laɓɓa, wayarta ta ɗauko tayi zaune a falo ta kunna phone ɗinta tana ƙoƙarin ƙira bayayi ta cika tayi fam haushi goma gomiya 9 sun isheta ga kewar Kamal ga rashin jin muryar ummi da Umpah Mamu Ablah Amrah Kabeer duk missing ɗinsu take. A hankali ta furta. (" *I miss u My Kamal Kan giwa Mai nasara, 3 hours bama tare ka barni da kewa please ka dawo gareni bana iya jure sama da hakan 3 hours yayi yawa bama tare."*) Ta faɗi tana sakin kuka tin karfinta.
Saida tayi ya isheta ta shiga gallery tana kallon pics ɗin Kausar da Basma. A hankali tace" Kausar i miss u Basma i miss u ku ɗin n daban ne kuna raina..." ta faɗi tana kwanciya ta ɗora wayar saman ƙirjinta ta lumshe idanunta. Ko 20 minutes bata rufe ba sai bacci.
Umaiamah ce zaune a parlonsu cup ɗin tea a hannunta tana kurɓa tana yamutsa fuska tace da Rainaha.
"Ke!! Raihana! Wai harda wannan jar ƙosan akaje kasuwar wannan balarabiyar da ganinta zatayi naci." Raihana tace"Ayya batajin hausa fa dan banji tayi hausa ba." Umaimah tace"Yo uban waye zai kashe aikinsa ya koya mata hausa? shegiya busassa." Raihana tace"Wlh sai na faɗa mata barima naje part ɗinsu." Umaimah tace "Kinci ubanki, zan haɗaku na jibgi banzaye wallahi ashe ma tana nan bari naga uwar me take a A canɗin." ta faɗi tana ajiye cup ɗin saman table ta miƙe tana rangwaɗa ta fice Raihana ta bar game ɗin ta bita. Kofar ta murda taji abuɗe kawai ta banko kofar ta shigo idanunta suka sauka kan kyakyawar fuskar Mubina, tana baccinta a cikin nutsuwa. Kusan sumewa tayi ganin zallar kyawun Mubina ɗin da iirn shigar jikinta kusan tsirara take.