Sashe 69
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna zuwa hospital ɗin aka amsheta cikin gaggawa aka fara bata temakon gaggawa, domin tsayar da jinin da yake zuba. Umpah hankalinsa yayi masifar tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye ƴarsa tinda abin nan ya faru kullum cikin ƙalubalen rayuwa take. Sai kai komo yake ya kasa zama. Abbu ya rasa meke masa daɗi yanajin haushin Kamal duk shine yasa su cikin wannan musiba da suke ciki a yanzu. Abbu ya riƙe Umpah yace.
Please kayi hkr ka zauna insha Allahu ita da abun da ke cikinta suna lafiya babu abinda zai samesu." Umpah ya jinjina kai yabi Abbu suka zauna saman kyawawan kujerun da suke jere a gun. Ummi tace"Allah yasa ma cikin ya zube kowa ya huta yarinya sai wahalar duniya take sha ina dalili, duk hakurinka sai ka tanka..."Abbu yace.
"Sabeela ayi hakuri don Allah, amman bari fatan zubewar cikin tinda bamu san abinda irin ɗan ko ƴar zasu zama ba a duniya , idan Allah ya rayasu. "Majeed baki ya taɓe, shi Abbu ɗinma haushi yake bashi, sai yaga kamar yana sane ɗansa yayi fyaden har son cikin shege suke. Umpah yace" Tau Allah ya mana mai kyau." Suka Amsa da "Ameen" Umpah na ganin kiran Mamu yaƙi ɗagawa dan tin ɗazu tasha masa kai ya bata Mubina, message kawai ya aika mata cewar ta bugu ne da table ta faɗi suna hospital...
Sai bayan 2 hours Dr ɗin ta fito baturiya ce tana goge zufa dan ba ƙaramar wuya taci ba. Tana fitowa, su Umpah suka mata caaaaa, suna tambayarta. Da harshen turanci tace" Ku gode ma Allah S.W.T ƴarku tanada rai anyi aiki cikin nasara yanzu haka tana lafiya sai de bata haiyacinta sbd tasha wuya, an sanya mata drip tana bacci amman kuyi hkr cikin ya zuɓe, wlh yarinyar taci wuya har wanki ciki muka mata sbd sauran gudajin jinin da suka laƙe a marata sam basuda niyar fita hakan ba ƙaramin illa bane ga rayuwarta, zai iya jamata matsala, babba amman yanzu Alhmdllh kome norma da zaran ta dawo haiyacinta..." ta faɗi tana kallonsu. Umpah da Abbu suka haɗa baki wajan cewa"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! "To Allah shi kadai yasan meke nufi da hakan, sai da muka zo nan ya zube." duk atare suka faɗi hakan kamar haɗin baki. Ummi tace" Alhamdulillahi, Allah kasa haka yafi alkhairi." Umpah zama yayi dabas ya rasa farin ciki yake ko baƙin ciki, a hankali yace" haƙiƙa Allah shine mai yin yadda yaso akuma lokcin da yaso." Ummi tace" Dr ko zamu iya ganinta yanzu?" Dr tace "No ba yanzu ba tana ɗakin hutu sai an fito da ita bata haiyacinta a yanzu, zaku ganta zuwa dare karku damu yarinyar yanzu babu wata matsala da zata fuskanta mun mata aiki mai kyau , ku mata Addu'a samun wani nan kusa." ta faɗi tana nuna Majeed tace" Kaine mijinta ko?" Kai ya ɗaga mata. Tace "Ok Allah ya baku wani muje ka amshi magugunan da za'a bata da zaran ta tashi." shida Abbu suka bita, Umpah da Ummi na zaune, ummi dai murna fal ranta zubewar cikin, tasan yanzu zata dawo normal ta nutsu tayi karatunta a nan, fatan ta ta warke kawai....
Misalin karfe shida na yamma Kamal ya gama karatunsa cikin masallaci, game da ƴan Addu'o'insa, ya miƙe ya fito a nutsu yake tafiya cikin izzar da haɗe da kamala, yana sanye ne da jallabiya ruwan toka, daman gidan kusa da masallaci yake, bai wuce gida biyar ba zaka wuce. Ya shigo da sallama, ya nufi parlon su kawu Jafar.
Umaimah ce zaune da Nafissa Raihana na famar game a Tv. Nafissa ta amsa sallamar tace"Oyoyo yaya Kamal yau ina ka ɓuya?" Fuska ya ɗan yamutsa ya zauna yace"Ina masallaci ne, ina yumnah da kawu ne, da Anwar?" Nafissa tace" sunje hospital ganin matar Abokin Daddy batada lafiya tahaihu ɗan baizo da raiba." Kamal yaji gabansa ya faɗi ya lumshe idanunsa A hankali ya furta "Ya Salam Allah yasa me cetone..." jin cup cikin bakunsa abu me sanyi a cikin bakinsa ya wuce masa maƙoshi, yasa ya buɗe tsumammun idanunsa, ya sauke su tar kan fuskar Umaimah, tana dab dashi a zaune ta kafa masa cup a baki. Haɗiye na bakinsa yay ya kauda kansa, ya haɗe face, yace.
"Bana so kina fa ganina kika shareni sai yanzu zaki wani bani zobo ni me kwaÉ—ai ko?"
Nafissa tayi dariya tana cewa "Na gansu a rana." Raihana ma dariya take tana cewa"Yaya Anwar kazo anga uncle Kamal da Aunty a rana."
Umaimah ta matso kusan Kamal ta marerece fuska kamar zata shige cikin jikinsa, har suna jiyo hucin junansu, idanunta ya tara kwalla, tace"Yaya Kamal kaji daɗi ana min dariya dan naga kazo kamar akwai gajiya a tare dakai , shine naje na ɗaukoma lemon zobo a fridge nice kuma na haɗa maka amman ka kwaleni ko?" ta faɗi tana shasheƙar kuka ta faɗa saman faffaɗan kirjinsa ta zagaye hannunta bayansa tana kuka tana shaƙar sansanyan ɗadɗaɗan turaren jikinsa, mai neman zautar mata da tunani.
Kamal yace"Ya Salam daga wasan oh ni sakeni ba na hanaki rungumata ba?! To mun ɓata." ya faɗi yana ɓanɓareta daga jikinsa. Ganin Nafissa na mata dariya yasa ya kama hannayanta duka biyu ya riƙe yana goge mata hawaye yace"Ok naji Sorry bari naba ƴan sa ido kunya ƙanwata ni dake bata ɓaci shiru bani lemon nasha." ya faɗi ya beƙa mata ƙaramin bakinsa. Tako saki murmushin farin ciki ta bashi lemon a baki ya kurɓa sau uku ya kauda kansa, yace.
"Alhmdllh" cikin jin daɗi Umaimah tace"Yaya baka ci abincin rana ba na kawo maka ko?" Kamal ya miƙe yana zuba hannunsa cikin aljihu yace.
"No Umaimah wallahi banajin daɗi banida nutsuwar cin abinci , bari naje na ɗan huta kafin a kira magarib , ina godiya da kulawarki gareni ." ya faɗi yana wucewa. A dole Umaimah ta hkr tabi Kamal da kallo kome nashi na burgewa ne ga ɗiya mace. Idanunta ta lumshe tanajin inama a goben ɗaura auransu tabi Kamal cikin garin Makkah suyi zamansu susha love, ɗinsu dan tasan dole zai iya love irin na ƴan india, zai kuma barta sai ta gama secondary school ɗin acan cikin garin Makkah, kafin su wuce Niger. Ihu ta saki tace"Yes Qalbina zanma biyayya a zaman aure, ina sonka wollah kai ɗin zaka zama gwarzon maza, fiye da maza uku wanda babu kamar su, na cikin book ɗin Aunty Ladingo *Abdallah na Hatsabibiya Ramlat ko Abdallah na Aunty Rumaisa, ko Dr Sardauna na Zeey baby!* Nasan soyayyarmu zatafi tasu ma insha Allah, yasin yaya Kamaluna ka hadu ingarma namiji, zanyi yaƙi da duk macan da ta raɓeka wlh sai inda ƙarfina ya ƙare, Qalbina MuAhhhhhhh." ta karasa kiss ɗin tana lumshe idanunta
Nafissa wacce ta cika da mamakin ƙanwar tata, bata san har abun ya girma haka ba! Tace.
"Oh Umaumah ni karki cinye min ɗan uwa yasin kuji kallon ƙurulla da irin wannan kalamai haka tab, haba yo danke ɗaya aka yishi ne?" ta faɗi cikin dariyar mugunta. Umaimah ta zumburo baki gaba, tace"Wlh ƴan baƙin ciki sai dai su mutu yayana sai ya aureni tinda Daddy ya gama bashi ni." ta faɗi tanama Nafissa gwalo. Raihana ƴar auta ita dai dariya take, tana kallon yayun nata. Nafissa tace"Tom Allah yasa muje Nigar kai Amarya."Da gudu Umaimah ta nufi bedroom tana rufe fuska tace "Amin inma baika zcy ba.!! Nafissa ta bita da kallo tana dariya.
Kamal yana zuwa ɓangaransa ya cire jallabiyar jikinsa, daga shi sai gajeran wando da singlet ya faɗa saman bed ya lumshe idanunsa ya rasa meke damunsa zuciyarsa babu daɗi sam. Wayarsa ya ɗauka ya shiga gun messages yana duba irin hira da suke da Mubina, sai ya tsinci kansa da murmushi ya ɗora wayar saman kirjinsa ya lumshe tsumammun idanunsa yana shafa kwantaccen gashin kirjinsa, A hankali yace" My Mubeen ɗan kurma fatan kina lafiya keda Babyna pls ki kirani naji lafiyarki, ke da babyna , una son ɗana please ki temakeni ki haifemin abuna" ya faɗa yana buɗe idanunsa yay saurin yin dailing ɗin numbert. Amman switch off. Tsaki yaja ya kira Hafsat. Bugu biyu ta ɗauka da sallama. Kamal yace.
"Momy ina yini ya gidan? Please momy kinada labarin tafiyar Mubina ne?" Hafsat tace"Lah my son ai sun isa lafiya tin jiya da dare yauma da safe wlh yayan ya kirani yana kiran Ummah da Samha bai same su ba yace naje naga lafiya wai sun isa lafiya London , to shine fa naje, na iske ashe wai Samha gidan gaggo ta kwana tabar wayar a gida can É—akinta Ummah kuwa lkcn bata kunna tata ba safiya ce, ina faÉ—i mata kuwa sakon Yaya ta kunna ina gidan ma ya kira suka gaisa harda Mubina É—in, sai ka ajiye hankalinka É—anka ko Æ´arka na lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske, yace.
"Alhmdllh Momy Ngd nasan ma zata nemi ɗan kurmanta." ya faɗi yana murmushi. Hafsat tace" Kamal kana son ƴarinyar nan fa dayawa wallahi ba ɗan cikin kadai kske so ba! Har ita ɗin sonta kake..." Kamal ya katseta ta hanyar cewa"No No No Momy bari faɗin haka ina son Babyna dai ina jin tsoron ta zubar min da cikina , duk da naji irin wayon da iyayanta suka mata zaiyi wuya ta zubar wai dan ta ƙuntata min." ya faɗi yana murmushi ya shafi sumar kansa yana lumshe idanunsa. Hafsat tace.
"Ƙarya kake wlh kana mugu mugun sonta..." Kamal tsinke kiran yayi bai bari ta gama faɗin abinda zata faɗi ba, ya yamutsa fuska yana taɓe baki ya ajiye wayar yana lumshe idanunsa a hankali ya ambaci " *Mubeena...* Tsaki yaja ya miƙe ya shuga bathroom sbd lkcn sallah magarib ya ƙarato...