← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 124

Sashe 8

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

....Suna shiga direct Umpah ya shigar dasu parlon baƙi, ya nufi cikin gidan domin kiran iyalinsa su gaisa.
Parlon shiru ba kowa sai Tv ita kadai tana yi, umpah ya girgiza kai ya gyara tsayuwarsa ya kwalama mai aiki kira"Laure!" Sai gata daman tana kitchen.
Ta ɗan rankwafa tace"Yallaɓai gani." umpah yace "maza ki shirya abin da kika girka ki kai parlon baƙi , amma ki fara kai ruwa da lemo da abin motsa baki maza." ya faɗa yana haurawa sama.
Cikin girmamawa laure ta masa ta miƙe ta tafi ta fara aiwatar abinda ya sata. Da sallama ya shigo cikin ɗakin, Mamu wacce gama sallar ta kenan, ta saka kaya ta amsa sallamar. Umpah ya ɗan matso kusa da ita har sunajin hucin juna, ta ɗan matsa tana murmushi ta saka rigar tana cewa"Ya dai?" umpah ya mata harara wasa yace"Uhumm bazaki bari naji gumin jikinki ba? Ok ki sauri ki fito munyi baƙi zaku gaisa , ina yarana?" Mamu ta matsu kusansa ta riƙe hannunsa tana dariya tace"Dan balarabe nawan Baby fa fushi take bansa wacece ta mata wasa a school ɗinsu ba shine fa ta riƙe abun a ranta." umpah rungumo Mamu ya manna mata saman goshi da lips ɗinta, yace"Tab to ki barta har baƙin su tafi zamuyi lallashi je kirawo Amrah ɗin." ya faɗa yana janyo hijab ɗin da ta cire ya saka mata sunama juna murmushi, ya kamo hannunta suka sauko ƙasa. Amrah da take zaune cikin shiri riga da zani na shadda green colour kanta babu ɗankwali gashin kanta ta sake shi har gadon bayanta, rabi ya rufe mata fuska tayi kyau sosai, tana waya da Kabeer yayansu taga umpah riƙe da hannun Mamu sun sauko, ta bushe da dariya tace"Brother wlh gidanmu ana zuba love fa , anga Ablah bata nan tana Alge, takusa zauwa ai." ta faɗa tana dariya.
Mamu ta janye hannunta cikin na Umpah, tace"Yarinyar nan ta renani bari kigani" ta faɗa tana nufar wajan Amrah, itaƙo ta miƙe ta tsinke kiran tayi jifa da wayar sama kujera, a guje tayi bayan umpah tana ihu ta ririƙeshi.
Umpah yace" Haba Nusy nah yi hakuri baƙi na jiranmu fa muje, Amrah maza ɗauko mayafi bari na leko Baby."ya faɗa yana hawa steps.
Mamu tace "jeki É—auko mayafi maza ni banson ya jijibo mana yarinyar nan wlh." ta faÉ—a tana zama tana kallon laure mai aiki da take kai komo tana kumshe dariyar ta amma se da ta dan fito.
Mamu ta girgiza kai batace ƙala ba, dan Mubinar ba raga mata take ba, danma tana taka mata burki...
Amrah ta nufi sama tana cewa"Mamu se na faÉ—ama Mubina kina gulmarta." ta karasa maganar tana hayewa saman tana dariya. Kwance take saman bed ta naÉ—e cikin wani irin tattausan bargo se rawar sanyi take hakoranta suna gamuwa waje É—aya.
Umpah ya tura kofar ya shigo da sallama, ganinta a nade cikin bargo, yay saurin! Isa gareta yana faɗi"Baby lfy oya tashi muje ki gaishe da baƙi." ya idar da maganar yana isa bakin gadon.
Yana budeta yaga tana rawar sanyi, da sauri ya haura saman bed ɗin ya kamata yana faɗin"Subahanallahi baby bakida lafiya shine aka barki..." maganr sa ta maƙale ne sakammakon aman da ya kufuce mata ta fara kelaya amai a saman gadon.
Umpah a rikice ya kamata yana buga bayanta ya rungume aman rabi na zuba a jikinsa.
Har ya lafa ya miƙe da ita da sauri tana rungume a jikinsa, ya shiga bathroom ya wanke mata, Mubina cikin galaɓaita tace "Umpah yawune ya bani wlh se na rama umpah yawu ne gurgu ya bani." ta faɗa tana ƙakarin wani aman jikinta na rawa ga wani irin zafi da jikinta ya dauka.
Umpah yace " Baby yawun me? Kiyi hakuri yanzu zamu hospital a kularmin dake." ksro sukaci da Amrah yana fita, ita zata shigo. A rikice tace"Umpah me yasami Baby?" umpah yace"da ta mutu kun tambsyeni mana." yana faÉ—in haka ya sauko. Amara ta biyo su bata shiga É—akinba.
Yana fitowa parlo Mamu ta miƙe ta nufo umpah, tana faɗi."Subahanallahi me ya sameta ne?" umpah yace "ban saniba ai agidan kuke yarinya zata mutu zazzabi take harda amai ba wanda ya dubata , yanzu da ban shigaba Allah kadai yasan me zai sameta , kuje ku gaishe da baƙin ku basu hakuri cewar baby ba lfy." ya faɗa yana nufar kofar.
Mamu tasha gaban sa da gudu ta rikeshi tace "Haba nawan" ta faɗa tana cire hijabin jikinta tace"Nawan kalli fa kayan da suke jikin Mubina bari a samata hijabi gamunan zuwa da zaran mun gaishe da baƙin , Allah baki lfy Autar Mamu da Ablah..." umpah ya katseta cewar"dallah can se yanzu za akulata , bama so." ya faɗa yana hararan Mamu. Tace"kaina bisa wuyana." ta faɗa tana sama Mubina hijabin wacce se ambaton"Yawunsa ya bani se na rama umpah yawu ya bani." Amrah tace" Wane wai? Ko duk zafin ciwone?" Umpah fita yay da ita. Yana fita bai bi ta kan kowa da kansa ya nufi rumfar motoci ya nasata gaba ya shiga yama motar key yaja ya nufi get yana horn, megadi ya buɗe masa ya sulala motar waje.
Mamu kuwa ciki ta koma da sauri ta É—auko hijab tace da Amrah" Maza muje mu gaishe su mu tafi hospital naga Baby tana jin jiki wlh na rasa me aka ma Mubina haka da ta kasa faÉ—amin , nifa na shiga tsoron lamarin nan." ta faÉ—a tana jan hannun Amrah da take kwalla tace" Mamu ni naji tana yawu ya bata inde ba zafin zazzabi bane." Mamu tace" yawun me kuma? bari de zamuji idan ta warwarw zan mata dabara"...

Da sallama suka shigo parlon Kamal da Sageer suka amsa, sakammakon Abbu na waya da Umpah, cewar yayi hakuri yarinyar sa ba lafiya yanzu haka yana hanyar hospital.
Mamu zama sukayi Amrah ta gaishe da su Kamal.
Kamal da sauri ya ɗago kai jin irin muryar cutie angel ɗinsa, cikin rashin sa'a bata kallonsu asalima kanta a ƙasa tana wasa da hannunta. Amsawa sukayi a tare shida Sageer Sageer ya cika da mamakin zallar kamar da yaga tanayi da Bbynsa Mubina, dan sun haɗa idanu lokacin da suka ahigo.
Kamal ya rankwafa ya gaishe da Mamu cikin girmamwa, ta masa tana cewa "ya yan gida fatan kowa lafiya?" Kamal yace"Alhmdllh ummah" Sageer ma ya gaisheta ta amsa cikin fara'a tace" ina yaya ina kanin?" Likacin Abbu ya gama waya yace"Hajiya ina yini ashe yarinya babu lfy to ku tashi muje hospital ɗin ai zama bai ganmu ba." ya faɗa yana miƙewa. Mamu tace" Eh zamuje amman kusha koda lemone ai zaifi Amrah tashi ki zuba masu..." ya katseta yace "A'A insha Allahu zamu dawo baki ɗaya da iyalina yanzu muje aga lafiyar yarinyar." dole Mamu ta miƙe suka fito tare.
Daman Abbu ya kira direba ya fito da mota, suna fitowa Abbu yace suje waje su tafi a motar gidansa.
Mamu bata musa ba suka fito, Kamal ya zauna mazaunin direba Abbu na kusansa Sageer nan sukayi sallama ya shiga motar sa ya nufi gida, sukuma suka nufi hospital.

Umpah suna zuwa hospital aka amshi Mubina ana bata temakon gagawa saboda sambatun da take, sukace zafin zazzabi ne, aka ɗaura mata drip wanda yasha maguguna nan ba jimawa bacci ya dauketa tana riƙe da hannun umpah gam, shiko na shafa kanta cike da tausayin ƴarsa.

Cikin nutsuwa Kamal yake driving hankalinsa a kwance babu wata damuwa dake damunsa asalima tunanun cutie angel É—insa yake tunda yaji muryar Amrah, wani sansanyan murmushi yay ya tura hannunsa cikin lallaunsar sumar kansa yana shafawa yana sakin murmushi da baisan dalilinsa ba...
A nutse ya shigar da kan motar cikin Katsina Huspital hadaddiyar hospita wacce tayi fice a garin maradi, tsarinta kade abin kallo ne shiyasa zakaga anata kawo mutane marasa lafiya daga gurare daban-daban harda ketare.
Parking spece ya shige yay parking suka fito.
Mamu tayi kiran umpah a waye bugo É—aya ya É—aga da sallama, Mamu tace"umpah Mubina gamu kuna wane gefan ne?" umpah yace"muna sama room 11 mu kaÉ—aine guri na masamman Baby najin jiki sai cewa take yawu ya bata na rasa gane wannan lamari , anya ba mayu suka kamata ba?" Mamu tace" Ok ga munan tare dasu Alhaji fa." kitt ta tsinke kiran, tace " Bismillah suna sama." Abbu yace" Ok muje" nan suka rankaya Amrah kuwa duk ta duririce ga kunyar Kamal haka kawai takejin nauyinsa duk bai mata magana ba itama bata masa ba.
Jin ana knocking ɗin kofar yasa umpah jan bargo ya rufeta ruf ya janye hanunsa da ta damƙe gam jin zazzabin ya fara sauka, ya miƙe ya nufi kofar domin ya buɗe masu.... Yasin yau Phone ɗina ƙamewa take ƙam😌😌😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Free Page*

🅿️7️⃣
Chapter 8 · 0% Book details