← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 124

Sashe 64

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a parlo bayan sun gama lunch, suna tattaunawa kan mgnr da Amrah ta kawo cewar Lameer nason ya turo iyayansa. Umpah yace ma Mamu" Ok babu damuwa har Na dawo daga London sai suzo kinga gobe zamu tafi ai babu mgn se mun dawo" ya faɗa yana kallon Kabeer yace"Wlh Kabeer idan kayi wasa se dai kaji na ɗaura maka aure , tinda bakada niyar fito da mata." Ablah tace"Barni da ƙaton banza se shegen gayun banza, amnan na kamasu fa ranar da yarinyar nan ƙawar Mubina , ai ita yake so ƴar gidan isma'il , ayi a haɗa su su biyu ayi bikin su." ta faɗi tana murmushi. Umpah yace,
"Masha Allah har na dawo Amrah bata shigo bane?" Umpah ya faɗa yana kallon Mamu. Mamu tace" Eh naga yanzu ba jimawa yaron yazo ko." Kabeer yace" Ai yaron yana da nutsuwa sosai Allah ya tabbar da Alkhairi." Umpah ya yace "Ameen yana shafa kan Mubina wacce tayi luf jikin sa, ko 10 minutes bata cike ba da gama yin amanta, sbd ƙamshin abuncin da ya cika mata hanci. Ta kamo hannun Umaph ta riƙe a shagwaɓe tace"Umpah zanci pizza zan sha kunnun gyada." ta faɗa tana rau-rau da ido sun kawo kwalla.
Ablah tace" Ai kuwa yanxu ya samo maki abinda zakici yi hkr baby sannu wannan masifaffan aman da ya saki gaba ai babu dadi , Kamalu anyi shegen yaro wlh..." Umpah yace "Ablah ayi hkr dai don Allah, Baby bari yanzu a samo maki pizza amman ina za'a samu kunnun gyada?" Mamu tace "Akwai markadaɗiyar gyada a fridge bari naje na mata." ta faɗi tana miƙewa.

Ablah tace"Sannu Nusaiba ƴar albarka gwara ki mata baiwar Allah gobe ya warhaka tana ƙasar arna." Umpah dariya yayi ya janye Mubina ya miƙe, yace "Kabeer mu fita sai ka kawo mata pizza ɗin zan ɗan jima waje kaɗan." Kabeer ya miƙe suka fice, Mubina ta koma kusan Ablah tana taɓa fuskarta, tace"Ablah ashe muna kama dake?" Ablah tayi murmushi ta shafi kan Mubee tace,
" Kwarai kuwa Baby." Mubina ta miƙe tana yamutsa fuska tace" Ablah ina zuwa kafin Mamu tamin kunnun." ta faɗa tana rankwafawa tama Ablah kiss goshi, tace"Zanyi missing ɗinki kakata." ta faɗa tana ta tafiya. Ablah tace"Allah yama yaronan abinda ya mana baby Allah na tare dake." Mubina de sama ta haye warta.

Zaune yake cikin haɗdaɗan parlon nasa daga shi sai wando iya cinyarsa, wace take cike da lallausan gashi, se singileti baƙa faffaɗan kirjinsa me cike da yalwa gashi duk a waje, se wani ni'imataccen ƙamshi ke tashi a jikinsa, farin glass ne manne a kyakywar fuskarshi, murmushi ɗauke kan fuskarsa,me kewaye da kyakyawan saje, saboda shirman Mubina da ya gama kallo yanzu bayan ya kunna waya, da hira da Hafsat ta masa ta Mubina harda fitsarin da tayi dan tsoransa, ya sakashi nishaɗi, shiyasa fuskarsa ke ɗauke da murmushi. Tv kunne sai karatun Qura'an me girma ke tashi. Laptop ne gaban sa yana dannawa, jin ƙaran wayarsa yasa ya ɗago da kansa ya ƙurama wayar tsumammun idanunsa, screen ɗin wayar, yaga sunan Umaimah na yawo, fuska ya yamutsa ya ɗan ja tsaki ya ɗauki wayar yay picking ɗin call ɗin ya manna wayar a kunnensa, cikin daddaɗar muryasa yace"Hello Umaimah ykk hope de kina lfy ko?" Daga can Umaimah ta shagwabe murya tace"Yaya Kamal ni banida lfy tinda kaki kirana ni se na faɗama Daddy wollah." guntun murmushi yayi iya kacinsa fatar bakinsa, yace"Sorry mana my Umaiamh ƙanwata." Daidai lkcn Mubina tana kwance saman bed ta shige bargo tayi dailing ɗin number Kamal ta faɗa masa abinda sukayi da Hafsat, ta masa karya wai ita ƴar uwarsa ce. Sai taji yana waya, ta kashe ta sake kira tana zumburi baki gaba. Kamal jin shigowar kira na biyu yasa ya ciro wayar a kunnesa yaga Mubuna ce da sauri ya kashe kiran Umaimah ya picking ɗun call ɗin yana danne dariya vidoe ɗin da ya kalla na shirman da ta tafka wanda Hafsat ta tura masa. Manna wayar yayi a kunnensa, ya sakar mata kyakyawan murmushi haɗe da kiss.
Mubina ta sauke ajiyar zuciya ta narakar da murya tace"My Deen Aboki É—an kurma, ina yini shine baka nema na ma ko?" ta faÉ—a tana shirin sanya masa kuka. Murmushin ya sake sakar mata mai taushi haÉ—i da kiss É—in yana hura mata iskar bakinsa ta wayar.
Numfashi ta sauke ta saki murmushi A shagwaɓe tace" My Deen bari kaji wani rainin hankali gun wancan shegen gurgun kwarton banza da na hofi, ya turo min ƴar gidan su wai a matsayin ƴar uwarka , tazo ta yaudare ni ta rabani da cikina su mugaye, bata san na santa ba, ai kuwa na mata rashin kunya na bata sako ta faɗima shi mugun maras imani se naga bayan sa, ni de Allah ya isana ban yafe masa ba wlh se yaga ƙarshensa." ta idar da mgnr tana sakin kuka.

Kamal ya lumshe lumsassun idanunsa yana fitar da numfashi me zafin gaske yana jin zafin abinda ya aikatawa Mubee duk da ba da gangan ba yayi, ga kukanta dake taɓa zuciyarsa. Kiran ya tsinke kitt.
Ya shiga whatsapp ya tura mata sako kamar haka,

```" Sorry my Mubee mmn Babyana yi hkr bari kukan, nasan akwai rana na zuwa, wacce zaki yafema Kamal duk da ya cuceki ni ɗe yanzu na a tuba bari kukan bana son kukan ki zai taɓa lafiayrki da kuma lafiyar babyna so share hawayenki, wato ita ta ɗauka bakida wayo har zata juyaki a zaman ƴar uwata lau a cutar min da cikina ko, ai ji nake kamar ni nayi cikin ina son cikin sosai wlh ya tsayamin a zuciya ki haifamin yaro mai kamarki My Mubee ƙawar ɗan kurma, maza share hawayenki na baki lbr me daɗi, da kuma shawara wacce zamu sama ɗan kurma ciwon zuciya, kuma se mun haife masa ɗansa ehe Oya yi shirunki yanzu bani lbrn zamu haɗu a London naga lafiyar babyna Oya Amsa yanzu Mubee nah.😘 ```

Haka ya tura mata. Lkcn kuwa har tayi fushi ta kashe wayar, jin ya jima bai turo sako ba! zatonta baya ra'ayin mata mgn ne, tinda yaƙi lallashinta ya bata shawara. Kamal jin shiru bata kiraba bata buɗe sakon ba! Kuma datar ta a rufe ya gane tayi fushi, murmushi yay ya dafe kansa a hankali ya furta, "Babyna kana saka momy saurin fushi fa yanzu wannan idan ba sa'a ba bazata buɗe ba ayau gobe kuwa bata ƙasar. Ya fada yana tura hannuwansa cikin sumar kansa yana shafawa, kiran Umaimah ya sake shigowa, a dole ya ɗauka yana amsa mata mgnr...

Mubina kuwa bayan ta kashe wayar tana hawaye ta shige bargo, sai kuma ta kunna tana turo baki, amman bata kunna data ba! Se ga kiran Sageer ya shigo, shanyayyun idanunta ta buɗe ta ƙurama wayar idanu ganin Sageer ne yasa ta ɗauki kiran ta manna wayar a kunneta. Sageer yace"Babyna ykk?" Mubina tace"My one ni banida wata lfy Allah kuwa" Sageer yace na sani kiyi hkr zaki warke da safe ina tafe muyi sallama tare zamu har Airport ɗin ok" Mubina ta shagwaɓe masa tace"My one kaga ɗan kurma ya taɓani ko." Sageer yace"Waye hakan Baby?" shiru tayi sanin babu amsar tambayar dan sam bata san me zata ce masa ba.! Se kawai ta shiga zuba masa shagwaɓa yana lallaɓata.

Suna cikin haka se ga Basma kamar an jefota, ta fado kan Mubina tace" Makaryaciya nayi ta jiranki kika ƙi zuwa kika sa na biyo dare anan zan kwana sai gobe dani za'aje Airport rakiya." Mubina ta zumburo baki tace"My one kaga Basma ko duk ta taushe ni." Sageer yace" Zan ko rama maki ta hanyr mata Allura, Ok bari na barki ku gaisa zan kira can dare musha love ki kularmin da kanki ki shafamin babyna dadynsa na gaishesa." ya faɗa yana tsinke kiran. Mubuna ta kama Basma da kokowa tana cewa"Tab yarinya se na rama wlh..." Mamu ce ta shigo da katon kwalin pizza Amrah na riƙe da cup ɗin kunnun gyadar.
Mamu tace" Ke!! Baby bakuda hankali kina haka kuke kokowa, ke!! Kuma Basma me hankalin sai ki biye mata." Basma tace"Mamu wlh itace ta kamani." Mubina ta saki Basma tana murna ta sauko daga saman bed É—in, tana lasar baki yawunta sai gudawa yake.

Ta amsahe kwalin pizza ɗin a hannun Mamu ta zauna saman carpet tace"Wow nice wlh zatayi dadi Allah ya barmin Babana Umpah." ta faɗi tana buɗe kwalin da hannu take cira abinta tana kaiwa baki da bismillah ta fara ci. Amrah ta bata kunnun gyadar tana haɗawa. Mamu tace"Mubina bazaki ma ƙawarki tayi ba?" Basma tayi dariya ta sauko ta zauna zata ɗauka Mubina fur taki harada kwalla tace "Wlh se na ƙoshi salon ki cinye mani tab." Mamu tace "Zo muje akwai kwali ɗaya a ƙasa sai ki debo." Basma ta miƙe tabi Mamu, Mubina bata kulasu ba ci kawai take. Amrah se dariya take mata wai yau Mubina ce ke rowar abunci tab. Se da ta ƙoshi dam ta miƙe ta shiga bathroom tayi sabon wanka ta fito ta saka rigar bacci ta haye bed ko ta kan wayarta bata tinda Sageer ya kashe kiran ta kasheta, bata biba ta kanta, bare Basma da take zaune itama sama carpet tana cin pizza ɗin. Mubina na kwanciya sai bacci cikin ikon Allah batayi amai ba. Amrah taji daɗin hakan. Sun jima suna hira da Basma kafin suke kwanciya. Mamu ta leko ta tambaya Mubina batayi amai ba? Amrah tace bata yi ba.! tsakiya suka sata suna hirasu har barawon bacci ya ɗauke Amrah. Basma kuwa suna hira da Kabeer ta waya, ta ɗauki wayar Mubina ta kunna tana game tana hira da Kabeer.
Chapter 64 · 0% Book details