← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 124

Sashe 115

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Da sallama suka shigo parlon, kawu Jafar ya amsa yana masu sannu da zuwa. Kamal ya gaishe da kawu da Yumna, haka Mubina ma.
Yumna tace"Mubina kamar bakida lfy ma ko?" Kamal yace zazzaɓi take."Kawu yace.
"Subahanallahi! Kamalu kamata kuje can ɓangaranku ta kwanta ta huta, Anwar muje masallaci kar a tayar da sallah."Kamal yace"Muje dai mu dawo sai muje tayi sallah sai ta kwanta." kawu yace"Ɗiyata kwanta ki huta to kafin muke dawowa daga masallacin." cikin girmamawa tace"To Dady." Kamal toilet ɗin falon ya shiga ya ɗauro alwala suka wuce masallaci. Mubina ta miƙe ta ɗauro alwala Yumna tace.
"shiga can ɗakinsu Umaimah kiyi sallah."Mubina ta amsa da "To" ta nufi ɗakin. Umaimah ta baje tana bacci itada Raihana. Mubina ta taɓe baki ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah.
Tana idarwa ta miƙe ta iso bakin gadon ta fatke Umaimah a duwawu, da karfi zabura tayi ta buɗe idanunta, ta saukesu kan Mubina. Fuska ta haɗe tace"lfy me haɗinki dani?" Mubina tace"To uwar jaraba saura ki shigewa mijina wlh yau zan sauke zafin zazzaɓina a kanki kibi a sannu azabar da zan miki se tafi ta baya, ban hanaki magana da ɗan uwanki ba ba ruwana, amman wlh ki kiyaye." ta faɗi tana hararata.
Umaimah tace"Aikin banza ai na fasa auran saura nima aleda zan buɗeshi dal yanzu Allah ya bani Hamraz dan haka can ku ƙarata." ta faɗi tana sauka daga saman gadon. Mubina tace"ba wani bazaki dai samuba, shi wanccan ɗin kinada tabbacin bai taɓa ɗana wata ba...?" ta faɗi tana yamutsa fuska saboda zazzaɓin dake taunar ƙashinta. Tace"To dan haka dai Kamal kwalelen biri da hantar kura." tama Umaimah gwalo ta fice. Umaimah baki ta taɓe ta shiga toilet.
Mubina tana zaune su Kamal suka dawo, Kawu yace"Kamal kaita ta huta, bari Anwar xai kai maku abuncinku, an gyara maku ɗakin."Kamal yace"Tom Kawu." ya faɗi yana Kama hannun Mubina ta miƙe, Yumna tace"bari yanzu da na gama girkin a kai maku ku samu ku huta." Kamal ya amsa da "To" suka fita.
Masha Allah ɗakin tsaf a gyara, Kamal nufi toilet da Mubina. Ta rungumeshi ta baya tace"Habibina nayi sallah fa." ɗan murmushi yayi yace"Wow sweetie sannu to bari nai maki wanka ko?" a shagwaɓe tace"Ni banaso yunwa nakeji kuma kamin tausa." Kamal ya juyota suna fuskantar juna yace"Ok Sweetie muje ki zauna na kawo maki abunda zakici, me kikeso"Ƙara shigewa jikinsa tayi a cikin sanyin murya tace" Habibina pizza zanci nasha juice shikenan ni." murmushi yay ya kama hannunta jikinta zafi rau, tausayinta ya mamaye masa zuciya bedroom ya kaita ya kwantar da ita ya shafi fuskarta yace"Ok mmn baby yi haƙuri bari yanzu naje na siyo maki pizza mai zafi kinji." ya faɗi yana shafa lallausan gashin kanta. Kai ta ɗaga masa tace"Habibina rufeni sanyi nakeji." rufeta yayi ya kamo hannunta ya saka mata wayarta yace"ki riƙe zan ƙiraki muna hira har na dawo, bazan iya barinki haka bansan halin da kike ciki ba." kai ta ɗaga masa." kiss ya manna mata a goshinta ya miƙe ya fice. Kamal yana fita ya shiga mota yay mata key yabar kofar gidan, ya ƙira Mubina, ta ɗaga ya fara mata hira tana lumshe idanu tana zuba masa zallar shagwaɓa, a haka har yaje ya nemo mata pizza ɗin ya biyo da juice masu sanyi da laban, harda ice cream. Kwance take da wayarr manne kunneta suna magana. Tsaye yayi bakin kofar ya tsinke ƙiran ya ƙaraso bedroom ɗin yana murmushi.
Miƙewa tayi tace"Habibina sannu."amsawa yayi yana murmushi. Ya ajiye ledojin ya zauna ya buɗe ledar ya ciro da kwalin pizzar yace"Oya aci." jikinsa ta kwanto ta narke tace"Sweety darling kai zaka bani." yace"Ai fa daman." ya faɗi yana ƙara tarairayota jikinsa yasa hannusa yana cirowa yana bata a baki ta amsa tana ci. Sosai taci pizzar ya bata juice tasha ya ɓallo maganinta ya bata tasha yaje ya wanko hannunsa yazo ya kwanta ya ɗorata ƙirjinshi, ya jamasu blanket, yana matsa mata jikinta gaɓa gaɓa, tana masa zallar shagwaɓa. Ya jima sosai yana mata tausar har zazzaɓin ya sauka, idanunta biyu, salon Kamal ya fara canzawa ya shiga lagudata da tsotsarta, Mubina tanajinsa tayi mukis ta ƙyale tana amsar sakon nasa, ta sakar masa jiki yana murzata da tsotsarta sai shagwaɓa take masa, wacce ta ƙara susutashi. A hakan har bacci ya ɗauketa, ganin tayi bacci ya cire bakinsa daga saman nonuwanta ya ja mata rigarta ya rungumeta tsam a jikinsa, yanajin tausayinta da ƙaunarta fiye da kome.... A haka yaji ƙaran buga kofa. Idanu ya buɗe a hankali yace"Oh my god nifa bana majin yunwar Anwar!" ya faɗi yana zame jikinsa a hankali daga jikinta, ya lulluɓeta ya sauka daga kan katifar ya gyara rigarsa da nutsuwarsa ya nufi parlon. Yana buɗewa yaga Anwar da babban tray an shaƙe shi da kayan abunci. Kamal ya amsa yace"Ai tayi bacci pizza na sayo nata bari na zubi iya cina mu koma can naci, zata jima bata tashi ba. Parlon ya koma yay xuba abinda zai iya ci a plate Anwar na tsokanarsa Kamal yace"A yanzu fa ni surukinka ne ko kana so na fasa bada Samhar ne...?" Anwar yace"Haba babban yaya na tuba Samha itace farin cikin rayuwata wlh na matsu fa aje a ɗauro mu dawo." Kamal ya waro idanu yayi gaba yana cewa.
"Tab Allah ya shirya to." Anwar yace"Ameen Brother amman nasan duk abinda kuke da ƴar balaraba bazamu kamo koda rabinku ba." Kamal kofar ya janyo baiyi magana ya saki murmushi. Parlon su kawun suka dawo har sun fara cin abuncin. Kamal ya zauna kusan kawunsa. Jafar yace"Ina Mubina ɗin?" Kamal yace"tayi bacci kawu, taci pizza." ya faɗi yana kallon Umaimah yace"Oh duniya ƙanwata ba oyoyo yayan ma?"Umaimah ya ajiye spoon ɗin hannunta ta turo baki tace"To matarka fa ta iskeni har ɗaki ina bacci ta tasheni wai karna ma mijinta magana, niko nace ta raba jinin dake gudana naka ajikina idan zata iya, kuma ni yanzu Wlh Hamraz ne a zuciyata, yaya Kamal sannu ya hanya...?" ta faɗi tana kallonsa tana dariya. Kamal yace.
"Wai ashe an kasani yanzu da har inacewa kawu ya bani ke nayi manage dake a ta biyu."dariya kawu da Yumna sukayi. Umaimah tace"Dady kaji yaya ko?" Kawu yace"Kamal ai mutuniyar an kusa aure fa."Kamal yace"Allah ya sanya alheri, wlh naji daɗi, wai ina Raihana ne?" Umaimah tace"Hummm ai dole kace kaji daɗi tinda daman ba sona kake ba." ta faɗi a shagwaɓe. Dariya Kamal yay yace"Haba dai kefa jini nace."Kawu yace biye mata zakayi ko..."Murmushi Kamal yay yana hamdala ya rabu da Qaya. Haka suka kasance cikin farin ciki da anushuwa, har dare, dan Mubina ma bayan ta tashi tayi wanka Kamal ya sake ciyar da ita Anan suka lalace wajan taɓe taɓe, sai yamma likis, suka koma parlon su kawu, har dare, Raihana tana liƙe da Mubina, Umaimah kuwa bata isheta kallo ba.... Sai karfe tara suka fara shirin tafiya. 10 pm suna Airport, du dukansu selfie Mubina ta ɗaukesu su dukansu. Sai karfe goma shabiyu aka fara sanarwar matafiya. Mubina Kamal da sukama su kawu sallama cike da kewarsu, suka nufi jirgi, Umaimah se lokacin tama Mubina magana.
Suna zama a kujera Kamal ya ɗaurama Mubina blet, shima ya ɗaura. Mubina tana rungume jikin Kamal cikin murna ta saƙalo hannunta wuyansa, fuskarta dab da tashi, tace"Habibina yau zanga Mamu da Umpah da Anty yaya Kabeer Ablah Abbunmu Ummah Samha." ta faɗi tana haɗe face ɗinsu tana murmushi.
Iskar bakinsa ya fesa mata kan fuskarta ya bata kyakyawan kiss saman lips ɗinta, ya zura hannunsa cikin rigarta ya shafo marata, a hankali yace"yes Sweetiena." lamo tayi jikinsa tana murmushi. Fuskarsa ya janye ya ɗauki ledar towel na rufar jirgi ya buɗe ya luluɓeta ya zura hannunsa yana shafa cikinta, can ƙasan maƙoshi yace"Sweetie" Mubina ta ƙara narkewa jikinsa tace"Na'am Sweety darling." murmushi yay yana shafa cikinta, yace"Oya yi baccin ki."Kai ta ɗaga masa..... Haka suka kasance abin sha'awa a cikin jirgin har ya lulu ya shiga hazo, kallo ɗaya zaka masu kasan so da ƙauna ya samu gurin zama a tattare dasu. Se da jirgin ya tashi su kawu suka koma gida.
Karfe 12 am na rana jirginsu Kamal ya sauka a Airport ɗin maradi. Kasancewar jirgin ya biya ƙasarsa Ethoipia kafin ya juyesu a sake ɗaukar fasinja na zallar ƴan niger.
Umpah da Abbu da Ibrahim Kabeer, Mamu Ummah Samha Amrah nagani tsaye cikin shiga mai kyau bakinsu ya kasa rufuwa sai raba idanu suke suga ta inda Mubina da Kamal zasu bllo.
A hankali a nutso suke saukowa daga jirgin, hannunsu riƙe da na juna, kaida kanka idan ka jina baka gansu ba to fa tabbas zaka ga yanda suka ƙara mhaukacin kyau kallo ɗaya zaka masu kasan a hankalinsu kwance yake, dan Mubina cikinta bai sata ramaba. Suna saukowa Mubina ta riƙe hannunwan Kamal tace"Habibina banga su Mamu ba?" Hannunta ya damƙe sosai a cikin nasa yace"Sweetie muje mu gama sauran abubuwa kafin nan ko." Kai ta ɗaga yajata suka bar wajan.
Bayan sun gama rubuce rubucan su suka nufi gun kayansu ya ɗora saman abin tura kaya saida ya ciki abu biyu, nan yace wani masu kula da abin tura kayan ya temaka masu har gurin da ake tarbar baƙi. Haka suka nufi wajan. Tin daga nesa Mubina ta hango Umpah da gudu ta nufi wajan tana ƙiransa. "Umpah!" tana gudu tana dariya. Hannuwa ya ware mata yana dariya shima. Jikisa ta faɗa ta rungumeshi gam tace"I miss u ilove u Umpah nah." Umaph yace"Me too Baby masha Allah kinyi kyau, abinki ɗiyar albarka." dariya tayi ta saki Umpah ta faɗa jikin Mamu tana dariya tace"Mamuna nayi kewarki sosai." ta faɗi tana son saka kuka. Mamu tace"Nima nayi kewarki Autata i love u ya gajiya." Mubina tayi luf a jikin Mamu tana murmushi. Kabeer yace"Auta muda Amrah ba'a yinmu ne?" Mubina ta saki Mamu ta rungume Kabeer tace" Tuba nake yayana i miss u i love u." Kabeer ya buga bayanta yace"Me too." Mubina ta sakeshi ta rungume Amrah tana dariya tace" i miss uI love u Auntyna." Amrah tace" nima haka Baby kinyi kyau masha Allah fa." Kamal ma da saurinsa ya ƙarasa ya rungume Abbunsa yana kissing nasa, yana dariya. Abbu yace "Kai karka cinyemin kumatuna haba kai me kaci ka ƙara zama ƙato haka..?" Kamal ya saki Abbu ya rungume Ummah yace" I miss u Momyna ina sonki nayi kewarki sosai wollah." ƴar dariya tayi tace sakeni karka karyani." Kamal ya saketa ya rungume ibrahim yace"I love u Ƙaramin babana nagode matuƙa da temakonka gareni." Ibrahim ya masa dukan wasa yace"Bana son wata godiyarka." Samha ce ta rungumeshi ta baya tace" Ni ka tsaneni baka sona." Kamal ya juyo da ita ta gaba ya rungumeta yace"Sorry sweetheart niɗin banza zan tsani rabin raina." dariya tayi tana maƙalƙaleshi.
Chapter 115 · 0% Book details