Sashe 20
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kamal Amrah na tsinke kiran ya saki lallausan murmushi, ya shiga danna horn tin karfi, se ga megadi ya bude masa tamƙameman get ɗin gidan, ya shige ciki.
Nan farfajiyar gidan yay parking ya juya ya kalli Mubina wacce take sheme a sume, kayan jikinta a jiƙe jagab sun dameta, tsaki yaja ya ɗauke idanunsa daga kallonta ya fito ya kulle motar ya nufi cikin gidan.
Parlon ya shigo shiru ba kowa se Tv, saman bene ya haura cikin saurinsa, yana hawa ya zaro key daga aljihun sa ya saka jikin kofar ya murza ya buɗe kofar yasa kai ciki, wani daddaɗan kamshi ne yake tashi cikin ɗakin kome fes a gyara, kome na ɗakin adon Maroon coulor ne, wani lumtsumeman carpet ne malale a tsakiyar katon filin ɗakin se wani makeken gado da tafkekiyar wardrobe da ta kusa cin rabin bangon ɗakin, da wasu manyan kujeru. Cikin sauri ya rage kayan jikinsa, daga shi se boxer ya shiga bathroom. Shower ya kunna kome agagguce yake, yayi wanka ya ɗaura alwalla faffaɗan kirjinsa mai yalwar ni'imar gashi se ɗigar da ruwa yake, ya daura towel ya fito. Wajan shirin ma a gaggau ce ya shirya ya murza maiyukan sa masu sanyin daɗin kamshi, ya gyara kwantacciyar sumar kansa baƙa lut, se sheki take tana walkiya sansanyan kamshi ke tashi daga cikin jikinsa. Wardrobe ɗinsa ya nufa ya buɗe wace take shaƙe da launin kaya iri iri, wata Jallabiya ruwan toka ya ciro sabuwa dalla a leda ya saka.
Ya dawo gaban dreesing mirror ya fesa sansanyan turansa, ya fice da gaggawa dan an fara sallah. Nan parlo yaga hijab saman kujera a ajiye, ya ɗauka ya fice, nan motar ya bude ya nasa hijab ɗin ya fice Masallacin. Bayan ya fito daga masallaci ya tsinkayo umpah da Abbu sabida gaggawar da yake bai masu magana ba, kuma suma basu ganshi ba, yay wuff ya shige ciki. Yana shiga ya shiga ciki bai jima ba ya fito, ya shige mota yay mata key yana ma megadi horn, ya wangame masa get ya sulala motar waje. Har yanzu su Abbun suna tsaye amman yanzu ƙoƙarin shiga mota suke wacce Haladu ya fito da ita, Kamal ya girgiza kai ya ba motar sa wuta ya fice a guje, yaga suna nunushi, murmushi yayi yana driving ɗinsa cikin nutsuwa, ya nufi hospita nan Katsina hospital kasancewar itace cikin unguwar ba nisa sosai.
Yana zuwa bayan ya shiga ciki yay parking ya ɗauki wayar sa ya kira Dr Munnir, cikin sa'a bugo ɗaya ya ɗaga, Kamal yace"Dr ykk? pls ina son room guda nazo da wata yarinya zan dubata da kaina , ta ɗan sami accident ne."Dr Munnir yace"Ok yallaɓai ba damuwa se ka shigo bari na fito na tare ka." Kamal yace"ok tnx" ya faɗa yana tsinke kiran, ya saka wayar cikin aljihunsa ya buɗe motar ya fito, ya zagaya set ɗin baya ya buɗe ya shiga ya zauna ya sanya tattausan hannayensa ya ɗagota ya tallabota jikinsa ya sanya mata hijab ɗin, ya kwantar da ita ya fito ya rankwafo ya cicciɓeta ya rungumeta ya shiga ciki. Nan A reception ya isko Dr Munnir tsaye, ya tare sa cikin gaggawa yace"Barka yallaɓai bismillah." Kamal ya bisa a bya Dr na gaba suka haura can sama. Wani hadadɗan room me gado ɗaya se fridge se Tv manne a bango, akwai kome a ciki kayan aiki na duba marasa lafiya. Suna shiga Dr ya kunna Ac, Kamal ya nufi gadan ya kwantar da ita yana ƙoƙarin jona mata wata na'ura. Dr munnir yace"Allah bada sa'ar aiki bara na wuce zan shiga tiyata ne." ya faɗa yana wuce wa. Kamal yace "Ok tnx." ya faɗa yana cire mata hajabin jikinta ya jona mata na'uran, nan ya fara ƙoƙarin ceto ranta yana bata temakon gaggawa.
Can gidan su Mubina bayan Amrah da Mamu sun gama sallah, Amrah ta shirya ta sauko ƙasa, lokacin Mamu nata sintiri a tsakiyar parlo da waya a hannunta, se kai komo take.
Amrah ta iso dab da ita ta kama hannayenta tace"Mamu to ta ina zamu fara nemanta ne? Tinda ba mu san inda taje ba ita da bata yawo , nafi zargin ruwane ya tare ta a hanya bata isa can gidan Baffa ba..." Mamu tace " Yanzu ma dashi muka gama waya bata je ba Basma ma na can ta tisa su gaba tana kuka wai yanzu zasu fita neman ta , ina yaga kwarin yawo yana can ya tashi hankalin sa se faɗa yake min , ya na barta ta fita ana ruwa." Amrah tace "bari na naje gidansu Basma ko dai tana uwar ɗaka tana bacci basu saniba..."Mamu tace"Lubah ma yanzu ta kirani bata can wlh yarinyar nan bata ji inda umpah ya yarda ai mata aure kurum ta ƙarasa karatunta a ɗakin mijinta , wlh bana son rashin jin Mubina sam bana son wani abu ya sameta , amman nasan umpah bazai yarda ya aurar da ita ba..."Umpah ne ko ya katse mata hira yana shigowa yace"Wlh Nusaiba ki fita a idanuna bazan aurar da itaba!! Nawa take? yarinyar , ga katuwa nan a gabanki amman ƴar mintsilar yarinya kika sama idanu , dudu yanzu take 20 year amma sbd takura gata kamar yar 14 year a tsunbure , ina dalili se ta kammala karatunta na cika mata burinta , har wani yawo take ina take zuwa? Yanzu ma laifinki ne kina kallon hadari kika barta ta fita , ina kiran wayar yanzu tana ringing aka ki ɗagawa daga baya aka kashe , meyasa da zata fita baku faɗa min ba? Ai cewa kika yi nan gidan su Basma ne tsallaken titi , amma bata can na kira Isma'il , mun fita mubi hanya ni da Abbu ko ma dace ban amince ku fita ba kuka wani haɗe kai hammm..." ya faɗa yana ficewa a parlon.
Mamu ta saki hannun Amrah ta zauna dabas, tace"Ya Allah kasa duk inda Mubina take tana lfy kuma cikin hannun nagari Sbd Allah mace shekaru 20 a ce wai yarinya , Sun daure mata gindi shida Ablah se taɓara take ." Amrah tace"Amin Mamu insha Allah tana lfy." ta faɗa tana zama. Wayarta ta ɗauki ringing, ganin sunan *my brother* yasa tai picking ɗin call ta manna a kunne haɗe da sallama, tace "yayana barka da yamma." Kabeer daga can yay murmushi yace "Amrah ya gida fatan anyi sallah juma'ah lfy?" Amrah tace lfy lau brother ina missing ɗinka yaushe zaka zo ne?"Kabeer yace na kusa zauwa insha Allah , ina Baby ne?" Amrah tace"Wlh yaya Kabeer itace ake nema daga gidan su Basma ta fita ba'a san inda tayi ba..." Kabeer ya katseta cewar"kuke zaune gida ina umpah da Mamu ɗin?" Amrah taba Mamu wayar, ta amsa nan suka fara magana tana faɗa masa kome dake faruwa dai...
Umpah ko lkcn da ya fito har yasa Haladu ya fito da mota, nan kofar get inda Abbu yake tsaye, shine Kamal ya gansu zasu shiga mota za'a neman Mubina. Basma kuwa bayan tayi sallah la'asar ta gama ta shirya direba ya kaita gidan Baffa, lkcn Baffa inusa hankalin sa a tashe Mubina bata iso ba, ya kira Mamu tace bata gida, se ga Basma tazo neman ta ba tanan, nan ta zauna ta girka kuka inna da Baffa suna lallashinta shine ya kira Mamu yana bam bamin faÉ—a. nan inna da Basma da Baffa É—in suka. shiga mota É—ireban su Basma na yawo dasu suna bin hanya wai ko sa ganta irin yanda su Umpah da Abbu suke yi...