← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 124

Sashe 106

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zuwa ya nasa cikin ruwan, wani irin kuka ta fashe masa dashi ta riƙo hannunsa, tace"Kamal zafi." tsugunnawa yayi ya ɗora kanta ƙirjinsa yace"Sorry Sweetie kinsha wuya dole zan gasaki, shiru amshi ruwan kisha."
Ya faɗa ya ɗora mata robar ruwan bakinta, yana shafa lallausan gashin kanta. Sosai takeshan ruwan baiyi yinƙurin hantaba, har saida ta janye bakinta tana sauke numfashi.
Kamal yace"Sannu Sweetie i love u more." ya faɗi ya miƙewa yay mata wanka haɗe da na tsarki se kukan shagwaɓa take masa yana lallaɓata. A towel ya naɗota ya fito da ita ya zaunar da ita samman kujeran ɗaya da take ɗaki ya ciro wata katuwar rigar sanyinsa ya saka mata. Ya nufi toilet a gaggauce yayi wanka ya fito ɗaure da towel jikinsa na ɗigar da ruwa, ya goge ya zura jallabiya, ya ɗauko mata abaya ya zura mata yana goge mata gashin kanta, wanda ke ɗigar da ruwa kamata yayi suka nufo wajan darduma, kuka ta saka masa tace"Kamal inajin ɗan zafi a ƙasana wlh."rungumeta yayi yace"Sorry Sweetie wlh nasani daure dai muyi sallah kinga tin ɗazu an gama sallar magarib." ya faɗi suna takawa rabin jikinta na jikinsa suka hau kan babbar sallayar, ta gyara tsayuwarta, ya gyara mata mayafinya, ya jasu sallah.

Can ciki kuwa Kawu da baiga Kamal a masallaci ba, suna fitowa yace da Anwar "leƙa ka ga lafiya bai fitoba ko jikin na matarsa ne se muje asibiti." Anwar ya amsa da"To" ya nufi kofar parlon nasu Kamal. Kawu kuwa ya shiga parlonsu.
Anwar yajima tsaye yana knocking amman shiru ba'a buɗe ba, lokacin suna toilet. Haka ya bar kofar ya Nufi parlon su. Umaimah tana zaune tana shan fruit, tana me cike da tsanar Mubina. Kawu yace "Umaimah ya ƙarfin jikin naki?" Fuska ta ƙwaɓe, Yumna tace"Wai lafiya kuwa ina Kamal da matarsa ne...?" Anwar ne ya shigo Yana cewa, "Anya ba bacci ya ɗaukesu ba, nayi ta buga kofar shiru." Kawu yace"Allah yasa suna lafiya, dai." Yumnah tace"Amin" Anwar ya kalli Umaimah yace"Wai waye ya wanwanka miki mari naga fuskar tayi jan?" Umaimah ta kalli kawu tace "Dady ka masa magana wa ya isa ya mareni na shanye, banida lfy ne."Yumna tace da kawu"Wai a masallaci bakuji cewar anga wata bane?" murmushi yayi yace.
"Zuwa anjima dai muje sallar isha yaufa talatin daidai gareshi kinsa kuwa ganinsa wajibi."Umaimah tace"nide kar atasheni sai jibi zanyi."da kallo suka bita ta miƙe ta nufi ciki. Raihana ta fashe da dariya tace"Dady wlh aunty batada hankali kaga abinda tama aunty balaraba." nan ta basu labari. Ai kuwa sun gano cewar to ba wani ciwo marine tashi, Anwar dariya yake harda faɗowa daga kan kujera.....
Suna gama sallar Kamal ya miƙe ya cire mashinfiɗar ya shimfiɗa wani yazo ya ɗauketa caɗak ya cire mata abayar ya saka mata riga ƴar ficiciya, ya kwantar da ita saman laulausar katifar ya rungumeta jikinsa gam yana mata tausa yana shafa lallausan gashin kanta. Jikinsa ta shige a hankali ta ƙirasa"Habibina." tana matsar ƙwalla, ƙamƙameta yayi ya haɗe face ɗinsu still yana manmatsa mata jikinta, yanda gajiya zata barta.
A hankali ya amsa da "Na'am Sweetiena farin cikina burin raina mahaɗin rayuwata, oya faɗamin menene." ya ƙarashe maganar yana tallafo kanta ya manna kunnensa saman bakinta. Yana shafa gashinta. Zazzafan numfashi ta sauke Masa a cikin kunnesa a hankali cikin murya kuka tace.
"Habibina zansha juice mai sanyi kuma yunwa nakeji kuma inason nayi magana da Mamuna da Umpah nah da Ablah..."da sauri ya É—ora bakinsa anata jin tana fizgo numfashi dakyat ga tanaso ta saki kuka. A hankali bakinsa cikin nata yace.
"Da Aunty Amrah nah da Yaya Kabeer ko? Zaki ƙarasa faɗa." ya faɗi yana sakar mata kiss a tsakiyar bakinta, ya zare bakinsa a nata ya zare jikinsa daga nata, ya miƙe ya cicciɓeta sama ya rungumeta ya nufo parlo da ita.
Lamo tayi a ƙirjinsa, yana isa saman kujerun ya zaunar da ita, yace"Bari na amso maki juice ɗin kafin aƙira sallar isha se na ƙira maki su kusha hira ni na tafi masallaci." ya faɗi yana juyawa zai fita.
Hannunsa ta riƙo tana matsar ƙwala tace"Habibina karka mata magana." murmushi ya saki ya ranƙwafo yace"kawo kunnenki Sweetie." ya faɗi yana riƙo kanta ya manna bakinsa a kunnenta yana mata magana yana shafa gashinta, ko me yace oho batasan lokacin da kyalkyale da dariya cikin guntin ƙarfinta da yayi saura ta maƙalƙale wuyansa cike da shagwaɓa tace"Allah Habibina da gaske kake?" ɗago da kansa yayi ya zuba mata tsumammun idanunsa yace"Yes sweetie bari na amso maki kinji an fara ƙiran sallah." ya ƙarashe maganar yana bata kiss a goshi ya miƙe ya nufi kofar parlo. Da idanunta ta bishi tana lumlumshesu, yana fita ta kwanta tana ɗan ciza lips ɗinta. Kamal yana kama kofar parlon zai shiga su Kawu suna fitowa. Anwar yace"Ango ganinku sai da ticket?" Kamal ya zabga masa harara, yana gaishe ds Kawunsa.
Kawunsa yace"Kamal lafiya bakaje masallaci ba? Ko jikin natane"Kamal cike da kunya yace"Eh kawu zazzaɓi ne me zafi ya rufeta amman da sauƙi yanzu."Kawunsa ya kama hannunsa yace"Subahanallahi! Allah ƙara sauƙi muje kar atayar da sallah."Kamal kunya ta hanashi magana dole suka nufi masallaci.... ~*Yacin babu Editing me kyau😌🥱🥱*~

*Ladee Me wando ce🤣😂🤭*

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣

Mubina har tsawon 20 minutes tana jiran Kamal, ya kawo mata juice shiru bai zoba, itako ƙishiryawar shan abu me zaƙi takeji sosa, miƙewa zaune tayi tana yamutsa fuska, ta tashi ta nufi bedroom, abaya ta saka ta yane kanta da mayafin abayar fito, kofar parlon ta buɗe ta fice. A nutse take tafiya a hankali saboda yanayin yanda Kamal ya gurjeta ƙasanta na mata zafi.
Da sallama Mubina ta shigo cikin parlon da sallama a nutse. Umaimah ta ɗago da kanta suka haɗa idanu, kai ta kauda bata amsa sallamar ba. Yumnah ta amsa sallamar, tana cewa"Mubina zo zauna mana sannu ya ƙarfin jikin naki?" Mubina ta ƙaraso kusan Yumnah ta zauna, tana cewa.
"Da sauki Umma ina Dady kuwa." Yumnah tace. "Suna masallaci." Raihana tace"Aunty balaraba kiyi kyau" Mubina tayi murmushi ta kalli Umaimah wacce take kaɗa ƙafafu tana hura hanci, ta danne dariyata tace"Umaimah ba gaisuwa, please idan da akwai juice me sanyi kawomin, bakina ɗaci wlh." Umaimah ta ɗago da sauri tana kallon Mubina. Itako Mubina tin lokacin da ta gama mata magana ta ɗauke kanta, suna magana da Raihana.
Yumna ce tace"Wai bakya jin tace ki kawo mata juice ne? Inaga baza arasa ba kuwa me zanyin." Umaimah ta miƙe batayi magana ta nufi bedroom, tayi kwanciyarta. Yumnah ta miƙe taje fridge ta ɗaukoma Mubina juice ɗin ta bata.
Mubina ta amsa cike da kunya tace"Nagode Umma barina naje nayi sallar isha se na dawo." Yumnah tace"To se kinzo da kin gama kizo zamuyi lunch, bari nima nayi salla." Mubina ta miƙe ta fice Raihana zata bita Yumna ta hanata.
Mubina tana shiga parlon ta baje saman kujera ta buɗe juice ɗin ta fara sha a nutse, saida tasha fiye da rabi ta ajiye, ta miƙe ta nufi bedroom
Tana shiga ta cire abayar jikinta ta fara linke kayan Kamal da ta masa fata² dasu, ta shirya masa su cikin trolley ɗinsa tsaf ta rufe ta share kwalaban turaren da ta farfasa ta gyara ɗakin tsaf dashi ta wanke toilet, ta jona abin turaren wuta ta zuba, ɗakin ya ɗauki wani irin ƙamshi, ta kunna Ac wani irin sanyin daɗi ke tashi. A gajiye ta shiga toilet ta sake gasa kanta tayi wanka ta fito ta shirya kanta tsaf cikin riga da siket na atamfa, ta saka hijab tayi sallar isha'i, tana gamawa ta miƙe bata cire hijabin ba ta nufo parlo tana ƙwaƙwaɓe fuska tana ƙiran.

"Kamal! Ina ka shiga ni yunwa nakeji." ta faɗi tana matsar ƙwala ta zauna a parlo tana rarraba idanu. Kamal ne ya buɗe kofar ya shigo hannunsa ɗauke da juice. Kai ta ɗago taga shine tsaye yayi ya ajiye kwalin juice ɗin, ya ware mata hannunsa a kofar parlo yace"Oya zo gareni my sweetie i miss u." cike da shagwaɓa ta miƙe tana takowa a hankali saboda yanayin nata. Da sassarfa ta ƙaraso ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi, a shagwaɓe tace.
"Habibina miss u too ina ka tafi ka barni?" tsam ya matseta ƙirjinshi ya tura kansa ƙasan wuyanta yana ɗan jujuya kansa yana bata lafiyayyun kiss, ya ɗago ya ɗauketa caɗak yana juyi da ita tsakiyar parlon yana sakar mata lallausan murmushi, yace.
"I love u Sweetiena ina masallaci babu inda naje." ya faɗi yana sunkuyawa ya ɗauki kwalin juice ɗin, ya nufi kan kujerun parlon. Zaune yayi tana jikinsa, yace" Oya amshi kisha." ƴar dariya tayi tana kallonsa tace"Habibina nasha fa , da kaina naje na amso." ta faɗi tana ɗora hannunta saman fuskarshi tana shafawa. Idanu ya waro yace"Oh sweetie kiyi haƙuri wlh mun tsaya jin wa'azine kinga anga wata gobe azumi fa." cikin murna ta maƙalƙaleshi tace"Wayyo daɗi Kamal zanyi azumi a saudiya, amman ai shikena bazaka sake min kome ba ko?" ta faɗi a shagwaɓe tana turo baki gaba, tana shafa sajan fuskarshi.
Ɗan guntun smile ya sakar mata, wanda ya ƙara masa kyau ya shafi fuskarta ya ɗora bakinsa saman nata ya kamo lips ɗinta na ƙasa ya tsotsa kaɗan ya zare bakinsa ya tallafe gefen fuskarta suna kallon junansu cikin wani irin mugun yanayi naso da kauna gira ya ɗaga mata ya kai bakinsa saman kunnenta a hankali yace"Uhm sweetie ban maki alkawaliba." kukan shagwaɓa ta saka masa tana dukan ƙirjinshi. Lallaɓata ya fara yi ta cikin siyasa, ya lashe mata fuskarta tas yace" Oya Sweetie muje kiyi lunch se muzo kusha hira da Umpah da Mamu." cikin murna ta rungumeshi tana godiya. Hannunta ya kama suka nufi ɓangaran su kawu.....
Chapter 106 · 0% Book details