← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 124

Sashe 121

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sageer yace"Uhm su laila majanun sannunku."Mubina cikin kunya tace"Yata Sageer barka da rana." Sageer yace"Barka amarsu." Kamal yace" yanzu dai muje mu ba zama ya kawomu ba."Sageer yay dariya yace .
"Haka fa."dariya sukayi suka shiga Sageer nacewa"Wai motarma baza a shigo da itaba?" Kamal baice masa komeba murmushi yake. Amrah kuwa zuwa tayi kafin su shigo ta shirya cikin É—oguwar riga ta abaya mai shegen kyau.
Suna shigowa Mubina tace"Ina auntyn nawane?" Sageer yace"Ku zauna tana tafe." ya faɗi yana nufar bedroom. Kamal ya zaunar da Mubina ya zauna kusanta, kanta ta kwantae saman kafaɗarsa, tace"Kamaluna zansha juice." Kamal yace"Sweetie a gidan mutanan?" baki ta zumburo ta kama hannunsa tace"Habibina yanxu ne nakejin ƙishin shansa." Kamal ya murza lallausan tafin hannunta yace "Ok bari matar gidan su fito." kai ta ɗaga.
Sageer ya iso Amrah na shiryawa ya temaka mata ta shirya ya kamo hannunta suka fito sai tsaburata yake, ta riƙosa ta marerece tace"Cheri please karka sani kunya wajan ƙanwata kaji, dan Allah." ta faɗi tana lafe a ƙirjinsa. Murmushi Sageer yayi yace"my chocolety suma fa ba kunyarce dasuba, to zan kamanta amman naga naa mana gwaninta zan manne abata kinsan bana iya nisa dake tawan." ya faɗi yana ƙoƙarin zura hannunsa cikin rigarta ta janye tana marerece fuska.
Kamota yayi yace"Ok muje to." haka ya kamo hannunta suka fito. Amrah kallon yanda taga Mubina da Kamal suke manne. Mubina jin tafiya yasa ta janye daga jikin Kamal ta miƙe tana dariya tace"Oyoyo Auntyna." Amrah ta saki Sageer ta rungume Mubina cikin murna tace"I miss u ƙanwata ya amarci?" Mubina tace"Me too antyna." Jan hannunta Amrh tayi suka zauna. Amrah ta gaishe da Kamal cike da jin yauninsa. Ya amsa cikin sakin fuska. Kamal yacema Sageer"Dr tashi Matata juice take so." Sageer ƴae dariya yayi ya miƙe yace"Abu mai sauƙi." ya faɗi yana nufar kitchen. Juice mai sanyi ya kawo mata, Kamal ya buɗe mata ɗan murfin ya beƙa mata ta amsa tana sha. Bayan ta gama Amrah ta jata suka tafi ɗakinta, Mubina tana yaba bedroom ɗin nata kome mai kyau kamar parlon. Haka dai sukaba junansu shawara wacce zasu ƙara riƙe mazajansu da gaske. Sun sami 1 hour suka tafi dan saida sukayi sallar azuhur, gidan Basma suka nufa, abakin gate Kamal ya tsaya, Mubina ta shiga. Basma na kwance a parlo ita ɗaya Mubina ta shigo parlon da gudunta, tana ƙiran "Basma kina ina?" Basma ta miƙe.cikin murna suka rungume juna suna murna. Basma tace"I miss u." Mubina tace"Me too." sakinta tayi ta nufi kitchen ta kawo mata ruwa da lemo da kayan motsa baki. Mubina tace"Wow ƙawata yayana ya iya kiwo kinga yanda kikayi kyau abinki." Basma tayi ƴar dariya tace''Humm ai ban kaikiba ina wani daɗi abin ni har yanzu zafi nakeji kullum sai nayi kuka." Mubina tace"Zaki ji daɗin very son nima haka nasha wuy Duk da anyi kofa kafin auran amma wlh nasha azaba kafin na saba. Ina yayana ne?" Basma tace"ya fita aiki yau ya fara fita kwana 8 ai amraci ya isa." dariyaMubina tayi, suka taɓa hira kafin tace zata tafi Basma harda ƙwalarta, Mubina ta lallaɓata ta tafi har bakin gate ta rakota. Mota ta shiga Kamal ya mata key ya haura saman titi. Suna hirasu tana kwance jikinsa har suk Iso bakin gate ɗinsu Kamal, horn yayi aka wangame masa gate ya shige ciki. Parking spece yay parking ya janyeta yace"Oya muje Sweetie." shagwaɓewa tayi ta narke ajikinsa tace"Habibina kunya nakeji, halan sunsan inada ciki?" Kamal yayi ƴar dariya ya matseta jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta yace"A'a basu saniba ko na faɗa masu kinyi ciki ne uhm Sanyin idaniyata?" kukan sangarta ta sakar masa tace"Wlh bana so karka faɗa kunya zanji Allah Kamaluna kaji." Kamal yace"Ok yi shiru da kukan sangarta babu hawaye." ya faɗi yana shafa cikinta, ya duƙar da kansa ya janye rigarta yama shafaffan cikinta kiss kamar ba ɗan mutum a ciki ya ɗago ya ɗaga mata gira. Dariya tayi ta rungumeahi. Haka ya buɗe mata motar ta fito ya buɗe gefan ɗaya ya fito ya rufe motar ya zagayo ya kama hannunta, ta fizge tace"Ni dai banaso." kwaikwayonta yayi yace"Nidai bana so." baki ta zumburo tana ƙwaƙwaɓe fuska. Hannunsa ya haɗe alamar haƙuri yace"To muje." jerawa sukayi ma'aikatan gidan suna gaisu Kamal na amsawa cikin sakin fuska. Garba ne ya iso yana masa ƙirarin da ya saba. Kamal yace"Garba baka gajiya, to ina fitowa." Garba yace"A fito lafiya mijin balaraba." murmushi Mubina tayi tana kallon Kamal, gira ya ɗaga mata. Da sallama suka shigo parlon Ummah na zaune Samha tayi matashin kai da cinyarta. Ummah tace"Oyoyo Ɗiyar albarka sannunku da zuwa." ta faɗi tana janye Samha daga jikinta. Mubina ta ƙaraso gun Ummah ta sunkuya ta gaisheta, cike da ladabi. Ummah ta kamota ta zaunar da ita kusanta, tana amsa gaisuwar cike da fara'a tace"ya karfin jikin naki sannu ɗiyar albarka Allah ya raba lafiya." Mubina kanta ta sadda cike da kunya dan bata san sunsa tanada ciki ba. Rungumeta Ummah tayi tace.
"Me kikeso yanzu a girka miki, ko amiki kunnun tsamiya?" cikin murnar da bata san ta baiyanata ba tace"Eh Ummah." ta faɗi tana ɓoye kanta a kafaɗar Umnah ɗin. Murmushi Imnah tayi tace"Ok bari yanzu da kaina." Kamal ya zauna kusan Ummah yace"Ummah wai ni baki ganni bane halan?" Ummah ta zungureshi akai tace"Eh ban ganka ba ta ƴata nake."ta faɗi tana miƙewa ta nufi kitchen.
Samha tayi dariya tace"Yaya nifa na fara gaisheka amman ka shareni gashi Ummah ta ramamin." ta faÉ—i tana dariya. Hararata yayi ya zunguri Mubina akai yace.
"Duk ba wannan bace ta ƙwacemin Ummah." Mubina ta masa gwalo tace"Eh ɗin na ƙwace kuma bazan baka kunnun tsamiyata ba." ta faɗi tana gwalo harshe waje, tana masa wani gwalon. Samha tace "Uhm masoya ba." Kamal yace"Yes ƴar saudiya ina Anwar ?" Fuska ta rufe ta ɗora kanta kafaɗar Kamal tace"Yayana ka bari kunya nakeji."Mubina tayi murmushi tace"Samha kice kawai yana lafiya kuna shan love yo miye a ciki." Kamal ya taɓe baki yace"Miya ce aciki, ni kike cewa a gayama magana ko? Ta faɗi mana na gwabje mata baki, ɗagani jeki ki hau Mubina." Ya faɗi yana janye Samha ya miƙe yace"Uhm Allah sarki bari na ƙira Umaimah mu gaisa nayi missing ɗinta." ya faɗi yana zaro phone ɗinsa daga cikin aljihunsa, ya nufi kofar fita yana latsa wayar. Mubina ta miƙe dan sam ta manta inda suke da gudu ta faɗa jikinsa ta baya, ta runƙumƙumeshi tace"Wallahi bazaka ƙirata ba Allah se nayi maganinku kai da ita bazan yarda ba wlh ban yafe ba idan ka ƙirata." ta idar da maganar tana sakin kuka ta shiga kokowar amshe wayar a hannunsa. Samha ta bushe da dariya tace"Ummah fito wlh yaya Kamal ya saka maki ɗiyarki kuka." Ummah kuwa kukan Mubina taji tana kitchen, ta kaɗo da gudu tiris ta tsaya ganin Mubina ta riƙe Kamal tana kuka. Mubina kuwa jin maganar Samha ta dawo da ita hankalinta da sauri ta saki Kamal dan da farko tama manta inda take. Kamal yayi sauri kamota ya ja hannunta ya waigo yace da Samha"Wlh sai na ɓata maki kika haɗani da Ummah wasa fa kawai nake mata..." Ummah ce ta katseshi ta hanyar cewa.
"Kamal kaci gidanku kawomin ƴata nan bayan ka sakata kuka, ina ne zaka kaita? dota taho nan." ta faɗi tana yafitota da hannunta. Mubina wata irin kunyace ta kamata, ta fizge hannunta, ta sadda kanta ta nufi wajan Ummah tana matsar ƙwalla.
Kamal ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa, yana murmushi ya ƙurama Mubina idanu ta nufi wajan Ummah cike da nutsuwa take tafiyarta. Yace" Ummah Allah baku haƙuri na fita sai na dawo, wai ɓari na leka company wajan Abbu." ya faɗa yana kallon Mubina ta isa wajan Ummah Ummah ta kama ta rungumeta tace"Rabu dashi zan kamashi ai muje kitchen." ta goge mata hawayen idanunta ta kama hannunta suka shiga kitchen. Samha da Kamal suna masu dariya, Samha tace"Wallahi yayana matarka ta kashe maka kasuwa wajan Ummah." ta faɗi tana dariya." hararata yayi yace.
"Eh ina ruwanki? Kema ai saudiya zaki zaki kashema Anwar kasuwa wajan Yumna, ki ga ai ba kome nima za'a ramamin kan mijinki." ya faÉ—i yana tafiya, ficewa yay daga parlon. A kitchen kuwa Ummah ta zaunar da Mubina kan kujera, tana mata hira, itako kunya takeji ta sadda kanta, dan sam lkcn idanunta sun rufe ta manta cewar nan suke ta rungumi Kamal ta saka masa kuka. Ummah ta buÉ—e fridge ta É—auko gumba, wacce taji citta da kananfari ta dama ta kaÉ—a kunun tsamiyar tanama Mubina fira, itako kunya ta hanata mgn.
Chapter 121 · 0% Book details