← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 124

Sashe 42

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umpah kuwa yana gama tsinke kiran Mubina na farkawa tana fizge-fizge, Kamal ya kirawo Dr tazo ta riƙeta tana dubata tace"Yanzu baza mata allura ba, me sunata?" Umpah yace"Mubina" sunta da Umpah ya faɗa yasa ta rage fizgewar tana motsa bakinta. Dr ta girgizata tace"Mubina ki nutsu buɗe idanunki kiga ƴan gidan ku kinji." ta faɗa tana zama kusanta tana riƙe da ita. Mubina cikin wani irin ƙaraji tace"Ka sake ni ka sakeni bana so abinda zai sake kusantamu har abadan dana sake ganinka gwara na ga gawata..."Umpah ya riƙeta yana hawaye yace"Autana buɗe idonki nine umpah kinji" Mubina duk da bata haiyacinta muryar umpah ta daki dodon kunnata yasa ta tsayar da fizge fizgen ta fara ƙoƙarin buɗe runanun idanunta wanda suka mata nauyi da wani irin zafi ta fara ɗagasu a hankali tana son buɗewa bakinta na motsawa a sannu sannu ta buɗe runannun idanunta wanda daket take gani sosai, cikin rashin sa'a ta sabke su akan fuskar Kamal wanda yake gefan Umpah yana haawaye. Habawa wani irin ihu ta saki ta rumtse idanunta da karfi jikinta na kyarrrma bakinta na rawa cikin dashasahiyar murya tace"Ba... Um...pah... Ba...ne... Shi...ne... Wan...nan... Ya min...fya...de...Ka...mal...ne..." ta faɗa tana ƙokowa da numfashinta... Dr ta fara ƙoƙarin seta mata amman ina ta sume ɗif numfashinta ya ɗauke. Amrah da shigowarsu kenan kuma taji abinda Mubina ta fada, take ta saki ihuuu mai karfi ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. Kamal se yanzu yaji sabon tashin hankali ganin Amrah, kasa ko da motsi sai jin mari yayi Abbu yana wanke masa fuska ta ko ina, ya kamashi yana cewa "Jeka na sallamaka idan ka yarda muka sake hadu tsine ma albarka zanyi..." Ablah a rikice tayi kan Mubina tana kuka, Majeed kuwa ya sumgumi Amrah ya dorata saman gadon ya fita neman Dr dan Khadija ta dage neman ceton ran Mubina. Goggo ta kama hannun Kamal suka fita ta tisasa gaba har mota ya shiga ta shiga tace"Muje gida. Yan yana kuka yace "Goggo Mubina dan Allah ku barni na gantan kisa baki kar Abbu ya tsine min kar yasa nayi nisa daku , ya bari Mubina ta warke sai nabar ƙasar ma baki ɗaya bayan amin hukunci, amman yanzu Wlh bazan iya barin Mubina ba banga halin da take ba..." Goggo tace"zaka ja motar mu tafi koko kukan zaka yi da sambatun?" Kamal yace "Zanja bari naja." ya faɗa yana ma motar key yaja ya nufi get. Dr ne yazo ya fara ba Amrah temakon gaggawa. Umpah yayi zuru yana kallon Mubina da Ablah da Mamu suna kuka ƙasa-ƙasa dan Dr tace zata kora su wlh. Ya juya ya kalli Amrah ya juya ya kama hannun Mubina, yayi tagumi yana hawaye. Abbu kuwaya rasa taina zai fara. ```Shawarata daku masu jiran na bati kayan sata ana turawa kuna karanta bagas baku biya ba... Me zai hana ku rufawa kanku asirri ku fasa karantawa, tinda kunsan dai ba hakkin ku bane...🤔🤔🤔```

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*
[26/07, 1:29 pm] +234 806 949 3599: *KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

2️⃣4️⃣

Abbu kallon su kawai yake yana girgiza kai tabbas Kamal ya tozarta su, ya zubar masu da mutuncin a idanun duniya, bai san ta in da zai fara basu hakuri ba... Dr daket ya samu Amrah ta farfado ta kece da wani irin kuka, Mamu ta rungumeta tana cewa "kiyi hkr Amrah haƙiƙa an cutar damu da dake amman duk me hkr na tare da Allah insha Allahu Allah zai bimana hakkin mu..." ta faɗa tana kecewa da wani irin kuka. Amrah tace"Kamal ka cuce mu ka yaudare mu ka tozartar damu..." Umpah ya katse ta hanyar cewa"pls muyi hkr ya isa haka bana son yawan mgn da koke-koke fatana Mubina ta dawo haiyacinta , kiyi hkr Amrah Allah zai kawo maki wani mijin nagari insha Allahu..."Majeed yace"Umpah an tozarta mana family..." Dr ta katse shi suma mutane shiru. Shiyasa suka kyale, amman Ablah ƙasa-ƙasa na kuka, Mamu na rungume da Amrah Dr ta kara gwadata tace"Babu wata matsala ta firgitane sosai amman ki kiyaye damuwa ko tunani dan zai iya haifar maki da matsala." ta faɗa tana fita. Mamu tace tunani dole ne haka damuwa dole ce.

Dr Khadija kusan 40 munites ta kwashe tana neman ceton ran Mubina, cikin ikon Allah ta farfado, tana fitar da numfashi da sauri-sauri, nan ta kuma banka mata allura ta ɗaura mata drip. Ta kalli Mamu da umpah tace"Pls kubar hayaniya yanzu ma kawai duk ku fita abar ki." ta faɗa tana nuna Mamu, tace"Ke uwace ki zauna ki kula da ita idan ta farka kiyi ƙoƙarin sata jikinki ki kwantar mata da hankali kibar kuka na fahimci babban lamarin Allah ya kiyaye gaba amman tabbas wannan bawan Allah da wuya idan da gangan ya aikata mata hakan, dan ni naga halin da yake ciki lkcn da ya kawota asibitin nan..." Mamu da Ablah suka haiyaƙo mata kamar zasu cinyeta suna cewa"Eh Sbd ba ƴarki ko ƙanwarki aka yima ba ko?" Umpah yace"Dr jeki kiyi hkr." Dr Khadija ta fita tana girgiza kai. Sabeelah tana gefe da yaranta sai sharɓar kuka take marsa sauti hawaye na fita. Abbu guiwa a sake yace"Abdulrahim banida bakin baka hkr bansan ta ina zan fara ba..."Umpah ya miƙe ya kama Abbu yace"Abubakar wlh baka min laifi ba muje dan Allah kuje ku kwanta ku huta dare yayi." fada yana jansa yace da Ummah"Hajiya muje a kaiku gida Majeed muje a kaisu gida dare yayi sosai." Ummah tace "Ah ina nan har naga farkawar yarinyar..." Umpah yace"Don Allah muje gobe da safe sai kizo." dole Ummah tayi sallama tayi ma su Mamu sallama ta bisu... Umpah da kansa ya tisa su gaba shida Majeed suka kaisu har kofar gida a mota. Daga nan Umpah ya shiga gida ya kwasoma Mubina kayan sawa dasu hijabi da kayan kwaliya da duk wani abun ɗa zai sata farin ciki harda su nunus suka koma hospital. Umpah ya sanyo Sabeela da yaranta gaba da Amrah suka dawo gida su kwanta su huta amman Ablah takiya da ya matsa mata ma kuka ta saka masa dole ya hkr, Sabeela tasa Amrah a gabanta suka kwanta tana lallashinta dan bata da aiki sai kuka.

Ɓangaran Kamal kuwa suna zuwa gidan goggo ta sashi dole yayi wanka, babu yanda bata yiba yaci abunci yaki ci daket ta haɗa masa tea mai kauri shima daket yasha tamkar maɗaci haka yake ji, bayan ya gama ta kama hannunsa suka shiga ɗaki ya kwanta ta saka shi gaba ya faɗa mata gaskiyar da yasa yay haka...? Kamal ya rufe idanunsa yana me jin dama mutuwa yayi ya huta da baƙin ciki. Goggo tace"wato dai baza kayi mgn ba ko Kamalu ka fiso na barka Abubakar ɗin?" sam yanzu baya sha'awar mgn dan ba fuskantar sa ba zasuyi, a hankali ya furta goggo nima ban saniba kawai tashi nayi na ganmu babu kaya har na rufar mata, amman Allah baya bacci shine zai saka mani..." goggo tace"Kamal bazaka faɗa ba ko?" Sbd Allah idan ita kake so me yasa baka faɗa ba se ka lalata masu yarinya yanzu ji furicin da Abbu yake a kanka, Kamalu shaye-shaye ka fara ne? To bari muga abinda Allah zaiyi gobe ni na tafi na kwanta."ta faɗa tana miƙewa ta fice. Kamal ya miƙe zaune ya haɗa kai da guiwa yana mai jin ina ma mutum na kashe kansa, ya sauko ya shiga bathroom ya. ɗauro alwalla ya fito ya shimfiɗa dadduma ya tayar da sallar nafila ta neman tuba da gafara gun ubangijinsa...

Can hospital tsakanin Mamu da Umpah ba wanda ya runtsa, Ablah ma a zaune take gyangyaɗi, seda Mamu ta lallabɓata ta kwanta Mubina kuwa bata tashi ba sosai take baccinta Umpah se lokacin ya sami damar ma Mamu magana ya fuskanceta sosai yayi gyaran murya yace"Nusaiba pls ina son ki ajiye maganar kara kotu ke kinsan nafiki jin zafin abun nan kawai dai naga kaddara ce ta rigayi fata kuma Allah zai iya jaraba bawa ta inda baya zato daman Allah yafi jarabaka da abinda kafi so dan ya gwada imanin ka, tabbas wannan haka yake an jarabemu ne ta wannan hanyar kuma dole mu ci jarabawa mu amshi kaddara da hannu biyu , dan Allah karki kuma nuna ma yaron nan kyama babu maganar kai kara mune zamu tozarta, kuma idan muka kai karan bamu ci jabawar ba kenan bana son kina nuna masu ko a fuska wannan kar yayi sanadiyar lalacewar zumuncin mu, kalli yanda suka tashi hankalin su shi kansa yaron da fa bakinsa ya faɗamin yana kuka , so dan haka mu kashe magana iya mu pls Nusaiba kaya dai a basu abinsu tinda aure ya haramta tsakaninsa da Amrah sai ya nemi wata mata itama Allah ya bata miji nagari me nagarta..." ya faɗa yana goge kwalla idanunsa. Mamu ta rungumeshi ta saki.kuka ta kasa magana. Bayanta yake bubbugawa yana jinjina kai. To haka suka kasance hankulansu a tashe babu bacci...

Kamal sai da aka kira sallah ya dakatar da sallah ya zauna yana kwarara Addu'a, yana kuka yana neman gafara wajan wajan ubangijinsa, duk yasan ba da sanin sa yayi ba. Yajima kafin ya dakata ya kirayi Sageer a waya ta jima kafin ya ɗaga cikin magagin bacci Sageer yace"Haba Kangiwa jiya ina ka shige suna yafi biyar gidanku wlh sai Samha tace kunje garine...?" Kamal cikin dashashiyar murya yace"Kazo gidan goggo daga kayi sallah ina jiranka." bai bari Sageer ya sake mgn ba ya tsinke kiran, ya miƙe domin zuwa masallaci.
Chapter 42 · 0% Book details