← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 124

Sashe 35

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dudubawa yayi bai ga Kamal ba! Ya fito farfajiyar hospital ɗin, ya tsinkayo shi a mota ya nufi motar. Kamal kuwa tinda ya buɗe kofar room ɗin zai shiga yaji wane hali ake ciki, yaga Mubina idonta tar abuɗe tana hira, yaji iskanci ne Mubina take idonta ras wai dan ta ɗauki fansa ne, ya dawo mota yay kwancin sa yana amsa waya da abokan kasuwancin sa... Sageer ya buɗe motar ya shigo ya zauna yana tiƙar dariya harda tafa hannu. Kamal yace"Ok zamuyi mgn zuwa dare insha Allahu." ya faɗa yana tsinke kiran, ya kalli Sageer yace"kun gama gulmata?" Sageer yace"Wannan baby ina da aiki kar fa muyi aure duk abinda na mata tace se ta rama...?" Kamal ya taɓe baki yace "matsalar kuce yanzu dai Alhmdllh tinda lfy take jeka fito min da ita na kaita gida..."Sageer ya kai masa duka yace"Wlh bamu yafe ba kuma sai mun rama."Kamal yace"Ai nafi karfin ku wlh se dai ku rame... Ni jeka fito da ita mu tafi"Sageer yace"ka tafi zan kaita ai..."Kamal yace"ƙaniyarka kai ka kawota? bari idan na ajiyeta a gidan su kaje ka ɗaukota bai dame nuba , ai yarinyar ina tsoron sharrin ta." ya faɗa yana buɗe motar ya fito ya nufi cikin hospital ɗin.

Sageer ya biyo shi yana dariya. Kwance take kan dadduma ta gama sallah bacci ya fizgeta, ta ƙudundune cikin hijabi. Kamal ya buɗe kofar ya shigo kallanta yayi yaga kamar bacci take, sanin halinta na karya yasa yace"Ke!! Tashi mu tafi gida" yaji shiru bata motsa ba, Karasowa yayi ya sunkuya dab da ita yana leken fuskarta yaga tana fitar da numfashi a nutse, hannayensa ya sanya ya cicciɓeta yay sama da ita firgigit ta farka idanunta cike da bacci, amman ganin Kamal ne ta maida idanunta ta lumshe ta kara narkewa jiknsa ta zagaye hannunta bayansa take ta koma baccin daman sama-sama ne tashin. Kamal na buɗe kofa Sageer ya shigo ya kallesu yana dariya yace"baby ina sonki sbd bakya yafiya yanzu ma dakon kaita mota ne ko?" Kamal bai kulashi ba ya fice da Mubina tana rungume a kirjinsa har mota. Sageer ya rufe room ɗin ya biyo bayan su.
Kamal a gaban motar ya kwantar da ita, daman kujura na kwance take ya zaga ya shiga mazaunin direba, Sageer ya iso yana cewa"Se anjima mun haÉ—u ko?"Kamal yace"Yes insha Allah." ya faÉ—a yana ma motar key ya fuzgeta ya bar hospital É—in. Sageer ma ya shiga mota yana dariyar Mubina, ya fuzgi motar ya nufi gida dan yayi wanka.

Kamal driving yake a nutse har yazo kofar gidan su Mubina, wacce take baccinta tsakani da Allah. Parking yay ya kalli Mubina, ya ɗan rankwafo dab da fuskarta ya hura mata iskar bakinsa ya sanya hannunsa kan kyakyawar fuskarta yana shafawa ya ja dogon hancinta, ya kai bakinsa dab da wuyanta ya dora habarsa kan wuyanta, ya shaki wani daddaɗan kamshinta, ya lumshe tsumammun idanunsa yana sauke tagwayan ajiyar zuciya, yaji numfashin sa na ƙoƙarin sauyawa yay maza zai janye, Mubina kuwa ta sanya hannunta ta zagaye shi a shagwaɓe tace"Uhm Kamal nah ni wlh bazan iya ba fa wayyo ni bana so ka bari pls." ta faɗa a shagwaɓe tana sakin kukan sangarta ta ƙamƙame shi sosai, har lips ɗinsu na gugar na juna. Kamal ya zaro idanun waje ya fara ƙoƙarin janye ta zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugo da sauri, a hankali muryasa mai cike da rauni ya furta" *Mubeena* me na miki me zan maki sorry yi shiri bari kuka kinji." ya faɗa yana ƙamƙameta kamar zai maidata cikinsa, fuskokin su na haɗe laɓɓansu ma na haɗe waje ɗaya har wani damshi-damshi yake badawa, yayin da bugun numshin su ma ya haɗe waje ɗaya suna shaƙar hucin junansu, kana jin bugun zuciyoyinsu yanda suke bugawa da karfi, se kukan Mubina marar sauti, har yawunta na ya fara shiga bakin Kamal , ta wani shige jikinsa sosai ta maƙaleshi. Kamal yayi saurin janye fuskarsa ya ɓanɓareta jikinsa, murya can ƙasa yace"Mubina kina mafarki ko?" ya faɗa yana kamota ya zaunar da ita, ya sanya hannunsa yana share mata hawayen fuskarta. Se lokacin ta buɗe idanunta ta kalli Kamal ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta zumburo baki, ta buge hannunsa ta matsa baya ta kalleshi zata masa rashin kunya cikin tsiwa tace"Wlh se na faɗama umpah na ganka a mafarki na zaka min fyade mugu ta Allah ba ta..." wani irin kallo da ya watsa mata yasa sauran maganar ta maƙale a bakinta tayi ƙasa da kanta ta beƙa hannun ta dauki jakarta tana gunguni. Kamal yace "karya kike wacce za'ama fyade ce take wani ƙamƙame wanda zai mata ba ma ta shiga neman kwatar kanta ba , wuce min a mota kiban guri maras kunyar banza kawai."Mubina bata yi masa mgn ba ta buɗe motar tana riƙe da jakarta ta fito ta tsaya tace"kuma Allah ya isana mugu gurgu kawai sai na rama bayan auran ku da Aunty mugu mai katon kai." ta faɗa ta zuba da gudu tana ihu se kace ya biyota. Kamal dariya yake harda riƙe ciki, ya ɗauki wayar sa ya kira Amrah bugo ɗaya ta daga da sallama. Yana dariya yace"My cutie angel ga rigiman ma nan mun dawo harda hijab nasa mata , yanzu ta gama min fitsara tas duk marin da taci har ta manta." ya faɗa yana dariya. Amrah tace"Au haba kace ka cimin kaniyarta? Yarinyar bata ji wlh Hubbina" Kamal yace"angel zan leƙa kamfani se zuwa dare zan shigo ok bye." Amrah tace "ok bye my Hubbi." daga can ya tsinke kiran yama motar key yabar layin, ko get ɗin gidan su bai kalla ba, dan sauri yake yanada baƙi a company.
Chapter 35 · 0% Book details