Sashe 84
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ƙirane ya shigo wayar Umpah ganin number ummi yasa ya ɗaga ya kara a kunnensa, ba tare da ya mata magana ba! Ummi daga can tace"Yaya Abdul ina wuni, yasu Ablah? Wlh kaga yaron nan ya biyo Mubina fa london, abinda yafi a ɗaura mata aure da Sageer kawai a gobe, tace bata sonsa amman dan jaraba wai harda siyayya ya mata, na korasu shida siyayyar tasa..." Umpah yay murmushi ya katseta, ta hanyar cewa.
Uhummmm Sabeela kina ina yajata keɓaɓɓan guri sukayi video a masu aure, ai ƙarya take miki cewar bata sonsa, ki barta kawai nasan maganinsu, abinda nakeso ki saka mata idanu, karku kuskura kubarta ko kofar parlo ta fita, a tsaremin ita a cikin gida ina tafe zanzo na ɗauketa, ai a goben nan bayan sallar juma'a zan ɗaura mata aure da Sageer wlh bazan bari yaron irn Sageer ya kuɓucemin ba ..." Mamu ta miƙe tace"Wallahi baza a aura mata shiba ɗan iskan, kayi ƙaƙa kuma da Sageer...?" Umpah ya tsinke kiran yace"Nusaiba kenan kina buƙatar wani shegen ne a nan kusa?" shiru tayi hawaye ya wanke mata fuska. Yace "to ki saurareni da kyau ba Kamal nace zan aurama Mubina ba mai sonta Sageer nace, bakiji nace a kulleta ko makaranta kar abarta taje zan koma na ɗaukota." Ablah tace"Allah ka isar mana" Umpah yace "Tsakani da Allah wanda ya kawo kuɗin auranta, to zan aurama ita gobe bayan sallar juma'a zan ɗaura masu aura, yanzu zanje gun mahaifinsa domin nace su shirya gobe suzo da shiri." Mamu ta sauke ajiyar zuciya tace"Alhmdllh naji yo ka ambaci Mubina na son wancan macucin yaron shiyasa..." Ablah tayi caraf tace.
" Allah dai ya isa,
tsakaninmu da wannan shegen yaron, tinda ya shiga rayuwar mu ya hanamu jin daÉ—i."Zubairu yace.
"Don Allah kuyi hakuri ku amshi ƙaddara a duk yanda tazo Allah baya abu banza kuma mummunin ƙwarai an sanshi da amsar ƙaddara mai kyau da akasin haka, Abdul ƙirata kaji ta bakinta." Umpah yace"Nasani wannan duk shine zai kitsa mata wlh bayin kanta bane, sai dai abinda zaku lura Mubina tana sonsa kawai ku barta zan aura mata Sageer tinda itace ta kawo mani shi ƙarya take na canza sheƙa wallahi, ko gawarta ce sai an kai gidan Sageer, amman ta bani mamaki bansa rashin wayonta yakai haka ba, har idanunta sun rufe akan so ta tsaya gaban wanda ya mata irin wannan babbar illah a rayuwa ta iya cemana shi zata aura harda cewa yayi nadama, kai! Kai wlh ba yin Mubina bane kitsa mata yayi kokuma ta Ablah ce ya tsafemin ɗiyata, Mubina kaifi ɗayace..." Mamu tace"Wlh babu son da take masa sai de tsafin kawai."Amrah dai tagumi tayi tana kuka kawai. Ablah tace "Akan shegen yaron nan babu wanda baiyi kuka ba, amma shine zaka aura masa ƴarka?" Umpah miƙewa yayi yana murmushin karfin hali. Yace" Ablah ba fa shiba Sageeru na wajanki zan aura mata gobe bayan sallar juma'a, Tom Zubairu tashi muje neman aure."ya faɗi yana dialing ɗin number Sageer bugu ɗaya ya ɗaga. Cikin girmamawa ya gaishe da Umpah, kafin umpah yayi mgn Sageer yace.
"Umpah karku damu da amincewata Mubina zata auri wani bani ba, wlh na yafe mata duniya da lahira Allah ya basu zaman lafiya, ni ƙanwa na dauketa ayanzu...."Umpah jiyayi ya kunyata, yana mamaki ashe har ta faɗa masa shima? Umpah yace"Sageer banida bakin baka hakuri, amman insha Allahu bazan taɓa bari ɗa nagari ba ya kuɓuce mani irin ka ba, wlh gobe ba fashin auranku da Mubina! ina Abbanka ne?" Sageer yace"Yana gari."Ok Umpah yace masa kawai ya tsinke ƙiran, suka fice da Zubairu. Ablah tayi tagumi tana tsinewa Kamal a ranta. Mamu ce ta ɗauki wayarta ta ƙira Mubina, amman switch off. Mamu tace"Ta kashe ma wayar baki ɗaya..." ta faɗi tana miƙewa, ta nufi sama. Ablah tace"Murɗeɗan banza yaji kunya ai dole gobe idan yaji ɗaurin auran ya shafa mata lafiya." Amrah tace"Ya Allah kama Kamal abinda yake ma family ɗinmu, ka sakashi ƙunci kamar yanda ya saka Umpah da Mamu kallo ɗaya zaka Umpah ka fahimci yana cikin damuwa dannewa yake kawai."
Ablah tace"Ameen Amarah in Allah ya hakumta kuwa sai yaci gidansu katon kwarto kawai." Amrah miƙewa tayi tace"Hummm Ablah bake bace kuka ɓatata dayawa gashinan kome idan tayi ji take daidai ne, yanzu saboda Allah wace yarinyace mai hankali zata yarda, namiji yasata ta turoma iyayanta abinda ta turo saboda Allah fa?" Ablah idanu ta shiga matsawa tace" Amarah harda zagina?" Amrah saman bene ta haye. Ablah ta fara jan carbi....
Umpah suna fitowa a mota a mota da niyar yaje Company gun Abbu ya nuna masa abun alajabi kawai sai suka ci karo da motar Abbu daide gate, yay parking zai fito. Umpah ya tsayar da motar yay parking, ko gama tsawa bai ba, Abbu ya iso. Umpah ya fito, yaba Abbu hannu sukayi musabaha, Zubairu ma sukayi. Abbu yace.
"Ashe na taki sa'a fita zakuyi?" Umpah yace"Ai gunka zani, kaga abun alajabi kafin na nemi mahaifin Sageer kasan na dawo da ɗaurin auransu gobe, to bismillah mu ƙarasa ciki."Abbu yace"Sun tura makane kaima...?" Parking ɗin ibrahim ne da yayi a gabansu da karfi yasa suka waigo suna kallonsa. fitowa yayi daga cikin motar yana cewa"Abbu zan shiga ciki na hangi ka anan ga kome ta ɗauko min wlh..." Abbu ya katseshi da cewa"Ok mushiga ciki har Abdulrahim ya gani."Umpah da Zubairu dai kallonsu suke. Abbu yace mu shiga mana."Umpah yace"Muje duk arikice nake."ya faɗi suna nufar cikin. Suna zuwa ya buɗe parlon baƙi suka zazzauna. Ibrahim kuna masu video ɗin suka fara kallon Mounkaila da alhaji Tukur suna faɗin yanda sukama Kamal tugu aka sato Mubina har yayi anfani da Mubina ɗin. Umpah tsaye ya miƙe jikinsa yana ɓari yace"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ke duniya ina zaki damu akan su ɓata masa suna suka ƙulla wannan abun? To mene ɗiyata a ciki saboda Allah..."Abbu ya riƙeshi yana hawaye yace"kayi hakuri don Allah ai bazamu kyale suba zamu nuna ma duniya ne yanda suka tuzartamu sai mun tozartasu suma, zamu saka a kamasu har matan dan da babu su hakan bazata faru ba."
Zubairu yace"Allah ya mana sakayi duniya da lahira."Ibrahim yace yanzu ku tashi muje police stetion kawai aje a kamasu duk suna gari."Umpah yace muje zasu san ƴata sukama haka wallahi tallahi, kuma gobe babu gashin ɗaura mata aure." ya faɗin haka ya ƙira Abban Sageer kan gobe bayan juma'a yan ason a ɗaurama yaran aure yarinyar ma zata dawo gida ta tare baiga anfanin karatunta ba.!! Ai kuwa yaji daɗin hakan Abban Sageer ya amsa da "To Alhaji AbdulRahim an gama Allah ya kaimu." Nan sukayi sallama. Miƙewa sukayi baki ɗayansu suka fito, Abbu baiso Umpah zai yanke hukuncin ɗaurama ƴarsa aure ba da gaggawa sanin ɗansa takeso, amman kuma hakan yayi dai dai wani fannin tinda zai maidota hannunsa. Shima haka zaima Kamal dan ya ƙuntata masa aure ba shiri ba.! Mota ɗaya suka shiga suka nufi police stetion. Suna zuwa bayan sun rattabo bayanai, nan D.P.O ya amshi video ɗin da kansa, ya ajiye ya bada umarnin aje tare dasu Umpah a kamo su Mounkaila da Tukur dasu Iyamu, tare da ACP Sahabi zasu, har yaji azabar da zai saka amasu kafin a shigar dasu kotu.... Babu ɓata lokaci, suka ɗinguma, gudansu iyamu suka fara nufa...