← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 124

Sashe 65

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamal kuwa har ya kammala abinda zaiyi baiji kiran Mubina ba, ya shiga sallah. Sai karfe uku na dare ya kammala ya kwanta Mubina kuwa da ɗan cikinta sunsha Addu'a, haka su iyamu da Mounkaila sun sha Addu'a kan Allah ya toni asirinsu. Juyi ya fara yana jin rashin daɗin ganin sakon sa da Mubina bata yi ba! Yaso ya mata wani wayo kafin take barin ƙasar Niger gobe. Wayarsa dake hannunsa ya kalla yana sakin murmushi yaga karfe uku da minti a shirin, na dare, sake gwada kiranta, yay yana lumlumshe idanunsa....

```Real Ladingo ce😅```

*KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣7️⃣

Yana danna kiran yaji ta shiga tana ringing. Basma da da har yanzu batai bacci ba gama wayarta kenan da Kabeer sunsha love, tana shirin kwanciya har ta ajiye wayar Mubina, tana gyara kwanciyarta ganin kiran yasa ta É—auka, ta manna a kunnenta. Kamal kuwa jin anyi picking É—in call É—insa ya saki lallausan murmushi, cikin farin ciki yana niyar mata kiss, ya tsinto muryar Basma tana cewa.
"Hello waye ne? Mubina fa tayi bacci." ta faÉ—a tana jiran taji anyi mgn. Kamal jin murya Basma ya sanya ya zaro wayar daga kunnensa ya tsinke kiran. Ya ajiye wayar nan gafen sa saman bed É—in, ya shige cikin bargo yana sakin tattasan murmushi yana shafa kirjinsa mai yalwar gashi.
A hankali ya furta cewa" Uhum Mubee anyi bacci Allah ya bamu alheri, maybe wayar ma Basma ce ta kunnata Allah yasa gobe kafin take tafiya mu ɗan zanta, baiwar Allah haƙiƙa na cutar dake a bisa kuskure, ki yafe mani Mubee mmn baby , tabbas ƙaddara cikin jikinki ce tasa hakan ta faru na afka maki ba tare da nasan yama hakan ta faru ba!? ta yama har suka kawoki wajena?" Kamal ya faɗa yana mai zubar da hawaye, nan take mikin abun ya dawo masa sabo. Ya jima sosai yana kuka kafin yake bacci, Asubah tagari ɗan kurma...

Basma ganin an kashe kiran yasa ta taɓe baki ta ajiye wayar ta kwanta tana rungume Mubina wacce take manne da Amrah, tana baccinta cikin nutsuwa, ba jimawa itama baccin ya ɗauketa...

Washegari tinda akayi sallar Asuba Umpah yake shirye shiryan tafiyar su, sbd jirgin safe ne zasu hau.
Mubina ma bayan Basma da Amrah sun gama shirya mata kayanta tsaf, itako tana gefe kwance suna waya da Sageer har sai da ya fito ya kamo hanyar gidan su ya kashe kiran lkcn Kamal ya gaji da kiranta, kuma ta gani taki ɗauka, haka sakon sa na whatsapp ma ta gani taki bashi amsa duk da yana manne a ranta tayi niyar sai bayan sun isa London ta koma makaranta da kamar sati zata nemesa tace yazo, taga yazo ɗin ko ƙaryar banza yake mata.

Abbu ne zaune cikin shirin tafiya saman gado Ummah na haÉ—a masa kayansa, yana waya. Abbu yay murmushi wanda ya baiyana zallar kyaunsa da tsantsanr kamar sa da Kamal, yace.
"Wlh Jafar da gaske nake maka yanzu jirgin mu nan gaba bazai wuce 40 munites ba zai sauka, ya ajiye sai kuma ya ɗauke mu." Kawu Jafar daga can yayi murmushi yace"Humm Sadeequ ni wai ina yarona ne?" Abbu ya nisa yace"Kaga yanzu ina kan hanyar tafiya bari nadawo zamuyi mgn Ok." Jafar yace"Ok amman ina son tinda ya fasa Auran ƴar abokin naka to zan haɗashi aure da ƴar wajena insha Allahu ayi abu na gida, so dan haka ka faɗa masa ya shirya ƙanwarsa Umaimah tace bataga miji ba sai Kamaluddin yayanta, kuma jininta ." ya faɗa yana murmushi. Abbu cikin farin ciki yace" Wallahi nafi wata biyu banji daɗi ba irin na yau na amince dari bisa dari daman zaman nasa haka na damuna yaro shekaru 30 year yaci yayi aure mana, duk fa ya girmi Ibarhim da Anwar yaronka so ga ibrahim yayi aure harda yarinya, so ka ga shima ya kamata yayi auran, amman akwai matsala har na dawo dai ina zuwa idan na gama abinda nake , kuma.kun gama kwana kwanar, nan da ƴan watanni wlh Saudiyar zan taho a ɗaura auren kowa ya huta , nasan zuwa lokacin kewarmu zata saka ya dawo , ko uaban riƙon nasa ya sayoshi gaba su taho, su tarda matarshi Umaimah, insha Allahu." Abbu ya faɗi yana jinjina kai dan yaji daɗin tayin Ɗan uwansa Jafar shima zai nuna masu bai san kome ba.! Murmushi Abbu yay.

Jafar yayi murmushin jin daɗi yace, "Allah ya kaiku lafiya ya bada sa'ar abinda akaje nema wlh nayi farin ciki sosai da jin wannan kalamai naka ban taɓa zaton zaka yarda da tayi naba, amman ban gane hausar kaba?" Jafar ya gaɗi yana murmushi." Abbu yayi dariya yace" Wlh zaka gane ne, ai ko ba ƴarmu bace ko ƴar wani ka ɗaura masa aure ta ɗauru bare ƴar ɗan uwana na jini da mahaifina da naka uwa ɗaya uba ɗaya fa, so yanzu dai zamuyi mgn bari na shirya." nan sukayi sallama.

Umaimah da take shirin shigowa parlon, tana sanye da wani farin siket har ƙasa da ƴar guntuwar riga ta saki ɗan matashin gashinta iya wuya tayi kyau sosai mazauannta sai juyawa suke masha Allah. Jin abinda Daddyn ta yake faɗi yasa ta juya a guje cikin mahaukacin farin ciki ta nufi bedroom gun Nafissa yayarta wacce tazo haihuwa gida daga Jiddah. Cikin murna ta shigo ɗakin tana kiran"Aunty Nafissa kina ina?" gyaran murya tayi tana ta famar zazzaga. Umaimah tace.
" Yayana Kamal ya kusa zama nawa, ni ɗaya abina Daddy ya bashi ni wayyo zanji daɗina yayana mijina, Niger zamu koma insha Allahu." ta faɗi tana faɗawa saman bed, tana dariya tana juyi tana rausaya kanta tanajin tamkar an mata bishara da gidan Aljanna. Wayarta dake hannunta ta ƙurama pic ɗinsa idanu tana murmushi, yayi kyau sosai yana sanye da 3 quater green coulor me haɗe da rigar sa kamar singlet, lallausan gashin kansa sai sheƙi yake, murmushi kwance kan fuskarsa fararan haƙoransa ras jere. Umaimah ta sumbaci wayar tana murmushi.
Nafissa kuwa wacce ke cikin bathroom matashiyace baƙa me kyau ba laifi zata kai 20 year, itama tayi murnar hakan sosai, Allah Allah take ta gama zazzage ciye ciyen da tayi ta fito dan zawayi take...

Ummah tana ƙarasa haɗa masa kayan, tazo ta zauna kusa dashi. Abbu ya rungumota jikinsa yana ɗago da fuskarta yana sakar mata murmushi yace. " Fatima nasan kewar ɗanki Kamal kike gashi nima zanyi tafiya, amman ki ajiye hankalin ki Kamal nafa gano inda yake shiyasa kika ga na watsar da damuwata , haba ni ba yaro bane kuma ki barsu ina zauwa zan ɗaura masa auran, da Umaimah ba dai ni suka ɗauƙa shashaba daga shi har Jafar ɗin." ya faɗa yana murmushi ya manna mata kiss a saman bakinta.
Cike da farin ciki Ummah ta kara rungume Abbu tace, "Mijina da gaske an sami inda Kamal yake ɗin?" Abbu yace"Eh ina zargin hakan nake ke!! Haka ɗin nema wallahi ki ajiye hankalinki har na dawo Kamal ɗinmu na cikin ƙushin lafiya." ya faɗa yana sauya salon labarin irin nasu na manya kuma wanda suka ƙware wajan iya soyayya, nan Ummah ta saki jiki sosai tana ba Abbu kulawa ga muranar jin yasan inda Kamal yake dan tasan baya mata wasa.

Samha ce zaune ita da Ibrahim da Sumaiyya da Hafsat sunzo se Safiyya wacce itama ta gama shirinta yanzu direba zai ɗauki hanyar Kebbi. Abbu ya fito cikin shuri Ummah na riƙe da jakarsa. Samha ta miƙe ta rungume Abbu tana cewa, "Abbu nah zanyi missing ɗinka sosai wlh..." Abbu ya buga bayanta yace "Ai kwana hudu kawai zamuyi Samha ki fa maida hankali gun karatunki." ya faɗa yana kallon su Hafsat yace. "Tau wajena aka zo ko wajan Safiyya bankwana ɗin?" Ibrahim yayi dariya yace" Ai duka mukazo gun yayunmu." Sumaiyya tace" Yayan mu Allah ya tsare hanya." Abbu ya iso gun Safiyya ya kama hannun Suhailat yace"Tom baby a gaida dady dakyau." Safiyya ta miƙe ta rungume Abbu ta saki kuka.

Saifa daket Abbu ya samu tayi shiru suka fito baki É—aya, suka rako Safiyya har mota su duka suka shiga dan har Samha dan sai taje gidan gaggo sunyi sallama kafin su wuce. Bayan tafiyar su Abbu ya kama hannun Ummah suka koma parlo harda Æ´ar kwallarsa, ta rabuwa da kanwarsa. Ibrahim na masa dariya dan yana tare dasu sai ya kaisu Airport zai kama gabansa. Abbu da Ummah da ibrahim suna zaune, Umpah ya kirasa ya fito lokaci na tafiya. Haka suka fito Ummah tana masa Addu'ar sauka lafiya, Ibrahim na tsokanarta, haka suka nufi gidan get É—insu Umpah É—in a motar Ibrahim...
Chapter 65 · 0% Book details